Kwanaki sunata jaaa yau kusan shekara daya da rabi da zuwan amra uae, hankalinta ba karamin kwanciya yayi ba, yanxu suna 200 level dayake semester uku sukeyi ah shekara kuma yau suka gama exam din second semester na 200 level, fitowa sukayi daga hall sannan suka wuce café itada Haifa, zama sukayi bayan sunyi ordern cappuccino wanda kullum sai sun sha shi, anatse Haifa ta kalleta sannan tace ''amra dan Allah tunda anyi hutu kizo muje gidan mu ki kwana biyu mana please...'' kallonta amra tayi sannan ta ce''haifa haka kawai saina tafi gidanku dan Allah ki rufa min asiri nikam kunya nakeji bazan iyaba kuma kinsan yanxu na shiga gym banason ina skipping time bakiga yanda na zama qatuwa sosai ba''....dakyar Haifa tayi convincing dinta harta yarda zata kwana daya sannan suka wuce gidansu Haifa, amra taso taje gida domin ta dan debo kayan sawa sai Haifa tace mata karta damu akwai kayanta da suka mata yawa sosai saita sakasu.. suna isa suka tadda ummi wadda itama tanason ganin wannan amra data chanza masu Haifa.. ummi ta karbeta hannu bibbiyu kamar yarta kuma sun dan taba hira kafin daga bisani kuma suka wuce sama domin kwanciya.. wasu hadaddu kayan bacci Haifa ta bama amra masu shegen laushi saida amra ta shiga wanka nan taga aljannar duniya sannan ta fara wanka da kayan kamshin Haifa masu sanyaya zuciya da saka nutsuwa sannan ta fito itama Haifa ta shiga wanka, shiryawa tayi cikin kayan da Haifa ta aje mata sannan ta haye gadon Haifa mai shegen laushi, wayanta ta jawo sannan ta bude social media da Haifa ta koya mata, yan dube duben tayi inda taci karo da wani hospital mai kyau da aka bude daman ita yawanci abubuwan daya shafi karatunta take following, nan take tayi following asibitin dama suna yin advert din asibitinsu ne, fita tayi daga Instagram din sannan ta shiga notepad tayi clicking inda ta rubuta housmanship tana shiga ta fara typing inda ta rubuta different hospital ta fara typing UDF special hospital for housemanship aje wayan tayi lokacin Haifa harta fito itama ta shirya cikin kayanta masu kyau riga da wando silk sannan suka kwanta, yar hira sukayi daga bisani bacci ya daukesu asuba ta gari.....
Washe gari da safe ya kasance Saturday abuh na gida, fita sukayi amra sanye da hijab din Haifa sannan suka wuce part din abu domin gaishesa, koda suka isa yana zaune ummi na serving dinshi white soup, gaishesa sukayi cikin girmamawa sannan suka dan taba hira,.. kallon Haifa yayi yace ''ya kamata kuje yawo ko tunda anyi holiday'' ba karamin dadi sukaji ba nan Haifa ta ce mashi zasuje mall ma anjima suyi dan shopping, black unlimited card dinshi kawai ya basu yace su sayi duk abinda suke so,godiya sukayi mashi sannan suka wuce domin yin wanka, amra ce ta fara lokacin Haifa ta fito mata da wata abaya white wadda tasha ubansun stones sosai, bayan ta fito Haifa itama ta shiga, shiryawa sukayi chass dasu kamar ka sace ka gudu sannan suka fito driver ya ja su har mall......suna isa suka fara zagayawa, Haifa ganin abuh ya basu black card dinshi yasa ta fara jidar masu kaya da yawa ita da amra wadda ita kunya ma ta hanata diba kwata kwata, babu abinda Haifa bata kwasa masu ba, kaya, abayas, undies, koda suka zo wajen undies Haifa mamakin yanda girman bras da panties din Haifa take, ganin amra na noqe noqe yasa ita ta fara jida mata da yawa, niki niki suka fito da kayan sannan suka shiga shops din handbag da takalma, anan ma saida Haifa ta kwasa masu kusan kala goma sha biyar kowannen su sannan suka wuce wajen cosmetics masu shegen tsada da gyara fata, amra kuwa mamaki ya hanata cewa qala, saida suka yi mai isarsu sannan suka wuce wajen parking suka aje kayan suka fita daga mall din, direct wani restaurant suka shiga babba, pastaíor café italian restaurant ne wajen sai yayan wane da wane ke zuwa aqasar fitowa sukayi daga motor lokacin wayan Haifa yayi ringing tana dagawa tace ''we're coming in now'' hannun amra taja sannan suka wuce ciki kafin su shiga amra ta kalleta sannan tace ''waye zamu gani anan?" murmushi kawai Haifa tayi mata sannan tace ''it's a surprise girl''...bayan sun shiga dan dube dube Haifa tayi sannan ta jawo hannun amra sukaje chan cikin restaurant din,.. zaune yake yana latsa waya ahannun shi jin sallamar Haifa yasa ya dago, mikewa yayi sannan ya sumbaci kumatunta yace ''my love marhaban'' kallonshi cikin so da qauna tayi sannan tace ''meet my best friend amra'' juyawa yayi ya kalli amra dake labe abayanta sannan yace ''marhaban best friend how are you?... zama sukayi, sannnan sukayi order sukaci abinci kala kala hadaddu, saida suka koshi sannan hammam yayi masu order dessert bayan sun gama suka fito sukayi sallama da hammam inda yace zai kaisu flower garden next time idan sun hadu.
YOU ARE READING
Auren Katin Kasa(unexpectedly falling❤️🇦🇪) by QueenMarh✍️
Lãng mạnAUREN KATIN KASA (Akk unexpectedly falling)❤️✨✨ Labarin auren Katin kasa yarjejeniyar aure ne tsakanin wani saurayi wanda rayuwarshi da tasowarshi da career dinshi duk a dubai yayi, General Muhammad taura, (Amar) da kyakyawar yarinya marainiya (Amra...