52

117 3 0
                                    

Washe gari da safe ta shirya domin zuwa motsa jiki, yauma kamar kullum ko'ina busy, black tight ne ajikinta sai riga mai girma sosai wadda ta rufe mata kwankwasonta har kasa, saida ta gama komai tukunna ta fara shirin futowa domin zuwa gida, jin sallama abayanta yasa ta tsaya, wani saurayi ne fari dan gajere dashi don kusan ta fishi tsayi kadan balarabe ne, murmushi yayi mata sannan suka gaisa, gabatar da kanshi yayi ''sunana abdul-basit, kullum ina ganin ki ke kadai bakida company, shine nace bari mu gaisa,'' ganinshi kamar kamilalle yasa amra maida mashi martini '' hey nice to meet you I don't need a company ay, I'm a grown up lady thank you'', ganin she's hard to get yasa basit saurin cewa, ''you look so calm daga yanda kike Magana na gane kina da kirki, zan iya zama abokin mai kirkinnan,?''  ganin zai bata mata lokaci gashi dare yana yi yasata cewa ''yes goodnight'' bata jira amsan shi ba kawai ta wuce ta fita,, murmushin gefen baki yayi sannan yace ''she's hot'' yana lashe lebensa.

Gida ta wuce kawai bayan ta tsaya ta saya abinci, ko data karasa wanka tayi don yau tayi exercise sosai jikinta yayi tsami, kuma tana ganin progress din ajikinta, sbd yanda ko ina ya fara zama snatch, duk wani excess fat ajikinta ya fara tafiya, abinci taci sannan ta kirasu salima, yau kwana biyu Kenan bata samunsu, kodata kira ishaq ya shaida mata suna cikin koshin lpy, hakan yasa hankalinta yadan kwanta, ta dukufa da karatu sosai batada wata sauran damu banda su salima.
Aranta tana tunanin dama da yanda za ayi ta kwasosu ta kawosu kusa da ita sbd bata jin dadin rashin zamansu ba tare ita ba.

Kwanaki karamar ruwa ja suke sosai inda amar ya fara shirinshi na last case din da zaiyi wanda yake saka ran idan har ya tafi daidai zai samu promotion saboda shekarunshi sun kusa 30years gashi Amma kullun saita dameshi akan ya dawo dukda taki fada mashi dalilinta nason dawowa amma bayajin zai dawo nan kusa.

Tsaye yake cikin shirinsa na kakin sojoji inda ko ina na jikinshi sanye yake da bullet proof, anatse ya sauko kasa inda ya samu Pablo yana shirya abinci a dining, coffee kawai ya dan sha sannan ya wuce motorn shi, futowa harabar gidan yayi inda m-5 da wasu guards dinshi suma sanye da uniform suke duk suka sara mashi, bayan motor ya zauna sannan kowannen su ya je mazauninshi suka fice daga penthouse din, aguje suke tafiya kamar zasuje yaki, koda suka isa head quarter anan suka tarar da general atsaye da manya manyan karfafan officers, kowannensu ashirye da bindigu kaca kaca ajikin su, futowa yayi daga motor tare da sarama general sannan ya qame a gaggauce general din ya fara Magana '' senior officer amar yunus TAURA of rank 1, this is an order you are to take the lead of this operation successfully with your men'' atare duka suka ce ''yesss sir sannan suka fara shiga motocin yaqi, koda ya shiga motor waya ya dauka kawai ya kira Amma bayan sun gaisa yace mata ''Amma na I need your prayer zan tafi wani operation yanxu''... addua sosai ta shiga zabgo masa cikin kamilar voice dinta sannan sukayi sallama.. ahankali ya lumshe idonshi sannan ya fara karanto adduo'I domin kariya da samun nasara,.. operation sukayi nakusan sati guda, inda sunsha wahala sosai kuma an kashe wasu daga cikin mutanenshi wasu kuwa sun raunata amma cikin ikon allah sunyi nasara don babu wanda suka ragamawa acikin wanda suka kaima farmaki, lokacin da suka kira headquarters ba karamin dadi kowa yaji ba game da wannan successful aikin da sukayi, wanda har shugaban kasar yaji dadi sosai sannan yayi masu alqawarin kyaututtuka da dama, aciki kuwa harda waenda za a masu promotion, ajigace suka dawo koda ya dawo direct apartment dinshi yasa aka kaishi domin ya huta, babban building ne wanda yake kunshe da apartment din mutane da yawa, ciki ya wuce kawai yah hau 7th floor daidai house number 53 ya manna smart keys dinshi ya bude kofan, gida ne mai kyau sosai bashida wani girma daidai mutu daya harma da karin mutun daya, tundaga sitting room ya fara rage komai nashi, parlor ne maidan girma sai L shape kujera babba sai katuwar tv da dan center table mai dauke da glass flower asamanshi, gefe kuwa wani jibegen flower vase ce mai kyau jikin curtains dark gray masu kyan gaske da tsayi, daki kawai ya wuce direct, shima ba laifi akwai girma gadone babba sai side lamp masu kyau ako wane gefen gadon sai yar couch acahn gefe, bai tsaya komai ba ya fada toilet, shima toilet din babu laifi akwai girma amma baikai ko kwatan na penthouse dinshi ba, sabule kayan jikinshi yayi ya soma wanka, saida ya dirje jikinshi sosai kamar zai chanza fata tukunna ya dauro alwala ya fito, sallah kawai yayi kafin ya bi lafiyar gado bayan ya kashe duk wayoyinshi da aketa faman kira tunda suka dawo.

Yasha bacci sai wajen takwas na dare ya tashi, yayi sallah sannan yasa m-5 ya karbo mashi abinci daga gida wajen Pablo. Within 30mins saiga m-5 ya kawo mashi sannan ya juya ya tafi....

Amra kuwa yau kai ya gama daukan zafi sosai, last paper suka gama na 400 lvl first semester, ta wahala sosai sbd ba ayi masu da sauqi ba, ta wani bangaren kuma dadi takeji domin yanxu hutun karatun yazo mata sbd zasu fara housemanship, dama qa'idar school dince sai sunyi 400lvl tukunna saisuje housemanship bayan sun gama na yan watanni saisu dawo school suyi last semester ba kamar wasu school dinba da saikayi graduation zakayi housemanship wannan Kenan...

Atare suka fito daga examination hall itada Haifa wadda itama kana ganinta kasan an sha wahala, direct café suka wuce suna dan taba hirar last paper da sukayi, saida suka ci burger da banana smoothie sannan suka miqe, atare suka wuce motorn Haifa wadda babanta ya saya mata recently Bugatti la voiture noire baqa,.. koda suka kama hanyan gidan babu abinda suke magna akai sai housemanship din da zasuyi...kallon amra Haifa tayi sannan tace ''amra wani hospital ne ah first choice dinki naga sun saka sabon asibitin nan na army's ah farko''... aikuwa shina saka fa as first choice dina" a cewar amra,,, kallonta Haifa tayi sannan tace nima shina saka fa, amma meysa kika saka ke?' murmushi amra tayi sannan ta ce ''its because of my little brother, yana burin shiga army, koda na fada mashi cewa ah cikin headquater din armys zanyi yaji dadi sosai sbd tun muna qananu zakiji yana cema abban mu shifa soja ne kuma zai kare abba da oumm dinmu'' wasu siraren hawaye ne suka zuboma amra, Haifa dake kallonta da gefen ido tace ''baki taba cemin komi game da iyayenki ba amra please ki fada min '... shuru amra tayi chan kuma ta share hawayen nata sannan tace ''banida iyaye duk sun rasu ni yar riko ce wajen uncle dina tun bayan rasuwar iyayena ta dalilin hatsarin moto'' jin haka yasa Haifa gangarawa gefe tayi parking sannan ta dube ta ''I'm so sorry amra shiyasa bakya maganrsu, inata mamaki ashe sun rasu, allah yayi masu rahama ameen, amma idan bazaki damu ba inason nasan tarihinki amra.. ahankali amra ta soma Magana ''kamar yanda kika sani sunana aisha amma ana cemin amra dalili kuwa sunan maman mahaifiyata ne, mun taso mu uku ne wajen mahaifinmu wanda ke son mu sosai nida kanne na, haka uncle dinmu yayan mahaifinmu shima yana sonmu sosai,ranar da bazan taba mantawa ba shine ranar da iyayenmu suka bar duniya, ranar munzo hutu gidan uncle Mustapha wato dady nidasu salima, lokacin su abba sun tafi umra, ranar da zasu dawo aranar Allah ya karbi ransu akan hanyar su ta dawowa gidan uncle daga airport domin dauko mu, lokacin uncle ya fita shida salim kanin mu, muna zaune nida salima da yaran gidan muna wasa uncle ya turo motor a daukemu, bayan mun isa asibiti emergency ward aka kaimu, gaban wani daki muna shiga mukaga uncle zaune yana kuka salim kuma kwance rai ah hannun allah sakamakon buqawa da zuciyarshi tayi, anan ake shaida mana iyayenmu sun rasu sakamakon hadarin mota kuma motorn su ya qone qurmus don ko gawarsu ba'a samu ba sai toka,nan take salima ta sume,mun shiga damuwa, sosai salim kam saida ya dauke watanni goma yana comer dalilin jin rasuwar iyayenmu wanda dady ne ya fada mana hakan, kullum muna tare da kaninmu school ne kawai ke rabamu har Allah ya farfado mana dashi saidai abin mamaki tundaga wayonshi har zuwa lokacin ya manta da komai, nan uncle ya kwashemu ya maidamu gida, bayan yan watanni mun samu kulawa daga bisani kuma muka fara ganin chanji, munyi rayuwar walaha sosai Haifa kamar ba mutane ba, har Allah ya tsallakar dani, shiyasa yanxu banida burin daya wuce na kawo kanne na kusa dani sbd hankalina ya kwanta nima bana burin komawa wannan gidan, har kusan raping dina yayana yayi wato wahab babban dan daddy'' tana kaiwa karshe ta fashe da kuka sosai... ba karamin tausayi ta bama Haifa ba sai taji yanxu duk duniya babu wanda take ji a jininta kamar amra kuma tasha alwashin zata kula da ita har tsawon rayuwar ta kuma zata dunga taimaka mata.
Gida suka wuce direct inda Haifa tadan debe mata kewa sannan ta dawo gida itama.

Kwanan ta hudu a kunshe tun bayan last paper rabonta da fita gida, yamma nayi ta shirya cikin shigarta ta zuwa gyming, kamar kullum saidata killace al'aurarta sannan ta fuce, koda ta isa basit ta tarar shida wasu friends dinshi, yana ganin ta shugo yace ''guys ga sabuwar hit dina chan, saina kwashi rabona'' ya fada da larabci, dariya sukayi sannan yaje wajenta, gaisawa sukayi kamar kullum sannan sukayi exercise tare don kwana biyu tana dan sake mashi sakamakon farko farko da take kaffa kaffa da kowa,

Auren Katin Kasa(unexpectedly falling❤️🇦🇪) by QueenMarh✍️Where stories live. Discover now