Yau Monday amar an bashi sabon office babba sosai wanda yaci uwar na da, kuma an kara mashi wani girma sosai, don daga overall head na headquarters sai shi, shiyasa girmanshi ya karu sosai ko daga guards dinshi zuwa responsibility dinshi kuma ayanxu bazaiyi reporting to kowa ba saidai shi akawo mashi report ya bada go ahead wanda hakan yayi mashi dadi sbd Akwai abubuwan da yake planning ba tare da sanin kowa ba.
Yau shiri amra tayi na musamman, ta sanya abaya skyblue mai baza ta kasa, ta wurin waist line dinta kuwa ta kamata chip chip, abayar mai budewa ce amma ana rufeta daa buttons, gashi tasha stones sosai, duba wayanta tayi nan taga message ya shgo na alert ganin daga dady ne yasa bata budeba , jakanta ta dauka da wayanta sannan ta fuce, ride dinta ta shiga sannan suka fara tafiya, tunda suka fara tafiya gabanta yake faduwa ta rasa dalili, har sukazo gaban united arab emirate army head quarters, tundaga first gate aka fara bincikarsu, saida na'ura ta tabbatar dasu sannan aka barsu suka wuce, haka akayi ah second gate shima,yana sauketa gaban bulding din ta fito tana duba wayanta, wannan email dindai ta bude sannan ta shiga cikin builing din a reception ta tsaya gaban canter, ganin wata yar balarabiya soja yasa ta gaisheta itama tayi mata murmushi sannan ta tambayi me ya kawota, nan ta nuna mata mail din saida matar ta duba system sannan tace, you'll have to be identified by the general first then you can start your work'' godiya tayi ma matar sannan matar ta hada ta da wani dan saurayi shima soja ne sannan suka wuce 10th floor wanda nanne office din general yake, koda suka isa ya nuna mata office din tsayawa kawai tayi tana karanto addua kafin ta sanya hannu domin yin knocking, budo kofar akayi daga ciki, kai tsaye idonta ya fada cikin na m-5 daya fito, ganin mace ah gaban office din oganshi yasa yayi mamaki sosai,dan zai iya cewa kamar tun farkon aikinshi da amar bai taba ganin mace tazo wajenshi musamman wannan da take kamar yar egypt, kallonta yayi fuskarnan babu annuri, soja duk inda yake saiya nuna halinshi, ''do you need anything miss?" ya fada yana kallonta, anatse ta fara mashi bayanin zuwanta da kuma wadda ta aikota domin zuwa wajen general, kai tsaye yace mata ''he's not on sit but I will tell him about it, amma yanxu ki wuce wajen asibiti, yana nan idan kika fita daga bulding dinnan, the next bulding by your left'' godiya tayi mashi baima amsa ba ya wuce abinshi, itakuwa wucewa tayi direct wajen lift ta sauka qasa, inda yayi mata bayani nan taje, asaman bulding dinma an rubuta (UAE armed force specialist hospital) tana gani ta gane nan ne asibitin, koda karasa ciki hadadden asibiti ne wanda baida wani girma sosai,don anyishi ne kawai sbd kula da sojojin headquarters ko wani emergency, wurin receptionalist ta karasa, nanma saida tayi masu bayanin koma, anan suka karbi document dinta, akayi registering dinta as an intern sannan suka nuna mata inda zatayi aiki as nursing assistant, wani office aka nuna mata, knocking tayi daga ciki aka bata umarnin shugowa sannan ta sa kai ta shiga, wata yar budurwa ce da akalla zatakai 28years, irin bakaken Egypt dinnan, murmushi tayi ma amra sannan tace ''come in and have a sit what's your name?'' murmushi amra tayi mata daga ganin budurwar zatayi mutunci, nan tayi mata bayanin komai nata sannan ta ce mata ''ma'am i am the new assistant and I will do my job well'' mumushi matar tayi sannan tace ''I love your confidence keep it up by the way I'm sister hafiza and I will surely train and assist you well, but I will like to tell you, more like an advice, wajen nan is not like every other organisation, dole sai kin kama kanki don aiki da sojoji sai mutun mai hakuri okay'' girgiza mata kai amra tayi...yan kananun abubuwa sis hafiza tayi dangane da aikin su sannan ta bata coat da stethoscope da yan files, gefenta kuma ta nuna mata wani mini desk wanda zata dunga amfani dashi throughout aikin da zatayi ah asibitin.
Kwanan amra biyu tana zuwa asibitin dukda bata gama sabawa da kowa ba amma kadaici yayi mata yawa, har allah allah take kwanakin su ja sbd Haifa ta dawo kusa da ita, sis hafiza kuwa tana kokari sosai wajen koyar da ita, kuma kullum sai anyi assembly dinsu anyi masu lectures gaba daya interns, ahankali ta fara sabawa da mutane sosai, tun bata Magana har ta fara koyan zama da mutane, wato cikin headquater dinma kamar bariki ne, bayan buldings har bulding apartment akwai ga duk wanda yake da buqatar zama anan, zama da mutane yasa ta fara jin general, duk inda ta gitta maganar new general ake da yanda yakeda qwazo dukda wasu zaginshi suke sbd abubuwan shi akwai tsauri aciki, tun bata tunanin san ganin wannan general har ta fara burin ganinshi, hatta sis hafiza idan ta zauna batada Magana saita general, tun amra dake zauna da ita bata saba ba har tazo ta fara sabawa da zancen general wajen sis hafiza, dakwai ranar da sis hafiza ta fita domin dauko abu daga motorn ta anan taga general da tawagarshi zasu shiga headquater, ay kuwa tana dawowa ta susuce da zancenshi, amra dai na jinta tana waya da kawarta tana zuzuta kyan da general yake dashi, karshedai tace kota halin qaqa saita mallakeshi. Amra dai tabe baki kawai tayi ganin abin sis hafiza ya fara yawa akan namiji.
Ayyuka sosai sunsha kanshi da m-5 wanda kullum saiya tuna mashi cewa akwai new intern da baiyi identifying ba, wanda basa barin har su fara aiki sai anyi identifying dinsu, yaudai agajiye yake sbd tun safe suke meeting gashi yana dan jin ciwon kai sosai, umarni ya bama m-5 akan ya kira intern din don yayi identifying koma wane sannan ya wuce gida, wucewa m-5 yayi har hospital bulding sannan ya sa reception suka kira office din da amra take, lokacin hafiza na duba wani patient,koda taji sakon cewa ana neman amra acikin headquater bata kawo komai ba, lokacin ta aiketa frozen store domin dauko wani maganin, ganin almost minti goma yasa m-5 cewa afada mata ta gaggauta zuwa office din general for identification, amra kuwa data dawo hafiza saita manta bata fada mata ba saidata je tayi sallah tukunna ta dawo anan receptionalist ke tambayanta ko taje kiran general, arude ta fara tambayan wani kira because ita ba a fada mata ba, ganin haka yasa kawai receptionalist din yace mata ta tafi kawai yanxu tsayuwar ma da take tana wasting time, da sauri ta tafi headquater bulding, a gagauce ta wuce 10th floor hannunta sai kyarma yake, tsoro duk ya lulube ta, da sauri ta karasa har kofar tafkeken office din general, bismilla tayi sannan ta fara knocking ahankali, an dauka wajen minti biyar kafin chan taji ance "come in"daga ciki, anatse ta bude kofar idonta akasa, wani daddaden kamshi ne mai sanya nutsuwa ya bugi hancinta ahankali ta fara ajiyar zuciyar tama rasa ta ina zata fara ahankali bakinta ya fara furta ''good afternoon sir, I'm so sorry for coming so late,'' jin shuru kusan minti biyar yasa ta dago kanta,office din tabi da kallo, ko'ina tsaf tsaf gwanin burgewa, facing din katon office dinshi tayi babu wasu tarkace akai, dan files ne sai laptop sai frames guda biyu side by side suna facing hadadiyar kujerarshi bata hangensa saboda ya bata baya, shiko goga ya juya kujera ya bata baya, idonshi alumshe kamar mai bacci, nutsatsiyar muryarta ce ta doki kunnenshi, ahankali ya soma juyowa saitin ta, ganin fuskarshi yasa ta zaro ido sosai wani irin kwarjini yake dashi kyanshi kamar bana mutane ba, fargaba ta cikata sosai, hankali atashe take kallonsa ganin yanda yake motsa bakinshi idonshi alumshe, ahankali ya bude kananun idonshi kamar mai jin bacci akanta, baiyi ko second daya ba ya sauke idonshi ya bude bakinshi dakyar don ciwon kai yakeji, yanxu idan yace zaiyi fada ma kanshi kara ciwo zaiyi, ahankali ya furta '' who the hell do you think you are? Your wasted about 30 minutes of my time''..yakai karshe yana lumshe idonshi yayin da yake resting kanshi jikin kujeran sannan ya zagayo da hannunshi saitin wuyanshi, bakinta kuwa mutuwa yayi ta kasa cewa komai sbd tsoro, shiko wannan shurun da tayi kara bata mashi rai yayi, azafafe ya kara da cewa ''are you deaf? Don't you dare ignore me''...cikin tashin hankali da fargaba yasa amra zubewa qasa kawai ,gwiwoyinta sun gaza daukanta, hankali atashe ta soma Magana ''dan allah kayi hkuri bazan kara ba sir'' tunawa da yaran da tayi magana dashi yasa tayi sauri juya harshe zuwa turanci shikuwa mamaki yayi wannan mai Zubin baqaqen larabawan ya akayi ta iya hausa dukda ba wani kallon kirki yayi mata ba... bai kuma cewa komai ba kusan minti talatin, gwiwoyinta duk sun sage sunyi tsami gashi shi baiyi Magana ba bai dago ba kuma baice ta tashi ba, kamarma bacci yake yanda ya lumshe idanunshi, ahankali ta soma dago kanta sai kuma ta sauke, tsinkayar muryashi tayi yana cewa ''you're dismissed'' da kyar ta iya tashi tace ''thank you sir''.. sannan ta fuce harda saurinta, tana fitowa ta fara jero nunfashi kamar wadda tayi gudu,ahankali ta fara sauka kasa, kodata koma office dinsu hafiza na ganinta ta tambayeta ko taje kiran da ake mata tace eh taje, wunin ranar babu abinda tayi tana zaune har time din tafiya gida yayi.
YOU ARE READING
Auren Katin Kasa(unexpectedly falling❤️🇦🇪) by QueenMarh✍️
RomansaAUREN KATIN KASA (Akk unexpectedly falling)❤️✨✨ Labarin auren Katin kasa yarjejeniyar aure ne tsakanin wani saurayi wanda rayuwarshi da tasowarshi da career dinshi duk a dubai yayi, General Muhammad taura, (Amar) da kyakyawar yarinya marainiya (Amra...