Tsokaci

284 37 8
                                    

Assalamu Alaikum

Yawan mata a Arewacin Nigeria suna fama da al'amura musamman wanda suka shafi aure. Ranar da aka ce auren wata ya mutu ko ta hanyar rabuwa ko a ce mijin ya rasu to fa shikenen ta shiga wata sabuwar rayuwa.

Musamman ma a ce bata da wata madogara ko wani gata da zai tsaya mata tssyain daka ya kula da ita da kuma yaranta. Wacce duk bata da ilimi ko wata kwakkwarar sanaa to tana cikin wani hali.

Shi ya sa ake so a wannan zamani mace ta dage ta nemi ilimin duniya da lahira ta kuma nemi kudin kanta ta hanyoyin da Allah ya halatta don ta dogara da kanta don kuma taimakon iyalinta da kuma 'yanuwanta.

Ya 'yaruwa ya kamata ki nemo MURYA wacce idan kika yi magana za a ji!

Na rubuto muku wanna Gajeren Labari ne don ya zama izna ya kuma ilmantar ya nishadantar.

Nagode

MURYA -Gajeren LabariWhere stories live. Discover now