AHALI GUDA PART 1 PAGE 1

30 3 2
                                    

*AHALI GUDA HAUSA NOVEL📔📖*

'''PART ONE'''

*PAGE   1️⃣*

*Wanda Suka Kawo Muku Littafin Rayuwa Ta The Novel*

_Syeserm_✍🏾✍🏾✍🏾

'''GABATARWA!!!

RAYUWA KALA KALA CE HAKA KUMA JUYI JUYI CE. KOWA NE DAN ADAM A DUNIYAR NAN AKWAI ABINDA YAKE GANIN SHINE DAIDAI. KOWA DA IRIN FAHIMTAR SA HAKA KUMA KOWA DA IRIN DABI'AR SA.

SHIYASA MA WASU MUTANEN SUKE GANIN BASU YADDA DA WANI ADDININ BA GWARA SUYI NASU DABAN, SUNA GANIN SHINE DAIDAI. LITTAFIN AHALI GUDA KIRKIRARREN LABARI NE WANDA MARUBUCI YA KIRKIRA DON TURA WANI SAKO NA MUSAMMAN.

BA'A RUBUTA WANNAN LITTAFIN DONCIN MUTUNCIN WANI KO WATA BA KOKUMA ADDININ KOWA BA. IDAN KUMA SUNA, HALI KO DABI'A SUNYI KAMAN CECENIYA DA IRIN TAKA TO MUNA MASU BADA HAKURI.

LITTAFIN AHALI GUDA LITTAFI NE DA AKA KIRKIRESHI AKAN YADDA RAYUWAR WASU AHALIN SUKE, AKAN YADDA WASU SUKE KAWO ADDININ SU INDA BAI KAMATA BA KOKUMA CIKIN WANI LAMARI DABAN.

KAFIN SHIGA CIKIN WANNAN LITTAFI DOLE SAI MAI KARATU YA FARA SANIN AHALIN DA AKE RIKICI TUKUN.

KUBIYOMU CIKIN LITTAFIN AHALI GUDA DON GANIN IRIN RIKICE RIKICEN DA AKE SHIGA.

WANI TAMFATSETSEN GIDANE.

Gidane Mai Kyau Sosai Wata Matace zaune Kan kujera tana daddanna wayarta ta zamani kamfanin Apple.

Kana ganinta kasan taji kudi domin kuwa gwalgwalai ne a wuyanta da zobunan gwalagwalai.

Fara fat Son kowa kin wanda ya rasa. Saidai a lamu sungwada tanada aure.

Wata Budurwace tafito mai tsananin kyau. Yarinyar zubin 'yan gayu masu kudi

Kana ganinta kasan hutu ya ratsata koda ba'a fada maka ba.

FATEEMAH: Aunty Khairyya Nagama hada kayannawa.

AUNTY KHAIRYYA: Yauwa Fateemah, Kinga idan anzo daukan naku bazaku bata lokaci ba.

Inasu Khadeejah da Mariam?

FATEEMAH: Suna daki Aunty Khairyya Suna Hirarsu.

AUNTY KHAIRYYA: Jeki kiramin su dukansu.

FATEE: Thom..

Daki ta nufa kai tsaye wajen 'yan uwanta.

FATEE: Aunty na Kiranku.

MARIAM: Thom Gamunan Zuwa Cewar Mariam daya daga cikinsu.

Tashi sukayi suka fito waje farlo inda Hajia Khairyya take zaune.

MARIAM: Mommy Gamu!

AUNTY KHAIRYYA: Yau zasu tafi shine kika zaunar da ita kike bata labari ko?

Kuma bayan kinsan antawo daukansu.

MARIAM: Mommy kawai dai 'yar hirace kafin azo kuma sunma gama hada kayan ai.

AUNTY KHAIRYYA: To ku zauna anan karku koma ciki dai.

MARIAM: Thomm Mommy.

KHADEEJAH: Aunty Khairyya, Labarin da kikace zaki bamu gashi har hutun namu yazo karshe zamu koma gida baki bamu ba.

AUNTY KHAIRYYA: To ai bakwa tinamin kullun kuna daki shiyasa amman idan kundawo next time zan baku.

FATEE: To ai yanzu babu abinda mukeyi Aunty Khairyya aida kinbamu.

AUNTY KHAIRYYA: A ah Yanzu Lokaci ya kure kuma labari ne mai tsayi.

Saboda haka kubari idan kundawo.

MARIAM: To ai Mommy Kifara idan yazo kawai shikenan wata ran sa dawo kikarasa.

AHALI GUDA CHAPTER ONEWhere stories live. Discover now