*Motherhood*A duk lokacin da aka samu ma'aurata su ka kwana biyu da yin aure, to kowa tsammanin sa shine ya ga an samu albarkar aure. Idan aka ji shiru Mace za a dinga nunawa ana tunanin gazawar da ga gareta ne. A kan manta cewa haihuwa na Allah ne, kuma shi Ubangiji ya kan ba da kyautar haihuwane a lokacin da ya so. Ya gaya ma na cewa wasu zai ba su Maza zalla wasu kuma Mata zalla, wasu ya haɗa musu Maza da Mata wasu kuma haka za su rayu su mutu ba tareda sun samu kyautar haihuwa ba...
Tun lokacin da Rabi ta tafi damuwar Faɗima ta ƙaru, babu sallah da za ta yi da ba za ta yi addu'ar Allah ya bata haihuwa ba. A lokacin da ma yanzu gani ake haihuwa shine Ribar aure, idan ka yi aure ba ka haihu ba gani ake ba abinda ka rabauta da shi.
A shekarunta shabiyar ta san rashin haihuwa babbar matsalace ga 'ya mace. Ta na fata kada ta zama Gaji da ake labari a ƙauyen su, wanda aka ce kusan shekaru Arba'in da aure amma ba ta taɓa haihuwa ba har ta rasu, kishiyoyinta uku kuwa duka sun hayayyyafa har ma da jikoki. Duk lokacin da mace ba ta haihu ba a ƙauyen su, da labarin Gaji ake tsoratar da ita. A dinga cewa "idan ba ki haihu ba haka za kiyi rayuwar kaɗaici kamar Gaji ki mutu ba tareda kin bar mai mi ki sadaka da addu'a ba".Sai da ta shekara ɗaya da wata uku da aure kafin ta je ƙauye ziyara. Ta na kewar gida amma ba yadda za ta yi, idan mace ta yi aure sai da dalili ta ke zuwa gidan su abinda ta taso da shi kenan. Goggo ce ba lafiya kuma jikin ta yayi tsanani sosai shiyasa Buba ya ce ta je ta yi kwana biyu. Gidan su Buba ta fara zuwa dan ta gaishe su daga nan kuma ta wuce na su ƙauyen. Rashin sakin fiska da ma habaici da ta ci karo da shi a gidan ya sa ta sha jinin jikinta, har ta bar gidan hankalinta a tashe ya ke.
A chan ƙauyen su Tunfure kuwa ta samu tarba mai kyau. Goggo ta yi marmarin ganin jikarta sosai wanda rabonta da ita tun da aka kai ta ɗakin miji.Ta na son faɗawa Goggo akan ta nema ma ta maganin haihuwa amma yanayin da ta samu Goggon ya sa ta yi shiru.
Tsab Goggo ta karanci damuwar da ke fiskar jikar ta. Yadda itama a baya ta damu lokacin da Aminatu ta wuce shekara ba ta haihu ba, ta san dole ne 'yan uwan Buba su damu.
Zurfin cikin Aminatu Faɗiman ta ɗauko, ba za ta taɓa gaya ma ta damuwar ta ba."Ki yi haƙuri Faɗimatun Baffa. Ina ga jinin Aminatu ki ka ɗauka shiya sa ki ka ji shiru har yanzu. Allah ya sa ina da rabon ganin 'ya'yan ki Faɗima"
Faɗima ta amsa da Amin.
Dawowar Faɗima Misau da kwana biyar Goggo ta rasu, ta so ta je ta'aziya amma Buba ya hana wai ai ba ta jima da dawowa ba, haka ta haƙura akan sai wani lokaci idan ta je ƙauye sai ta yi mu su ta'aziyar. Mutuwar Goggo ya shigeta sosai saboda shaƙuwar da su ka yi musamman bayan rasuwar Baffan ta, duk soyayyar Goggo ga Muhammadu to ta juyeshi zuwa kan 'yar sa Faɗima...
Wasa-wasa shekaru biyu su ka shuɗe babu labarin ciki. Buba dai bai damuba hidimar gaban sa kawai ya ke yi, tunda zai ci ya sha sannan ya tara da iyalin sa ai ba wata matsala. Damuwar rashin haihuwa da kaɗaici ya sa Faɗima ta fige ta lalace, dama ba ƙiba gareta ba sai ta ƙara bushewa. A irin wannan zaman ne Ladi maƙociyar ta ta bata shawaran akan ta dinga sana'a saboda ta rage kaɗaici. Da farko ta yi watsi da shawarar daga baya kuma ta amince, ko dan yadda Buba ke yawan zaginta da rashin tattali.
Namiji ke ciyar da mace ya tufatar da ita ya kuma ɗauke duk wata ɗawainiya na ta, sai dai miji kaman Buba wannan haƙƙoƙi da ya rataya a wuyan sa kaman wani nauyi ne da ke hanashi sakewa. Kuɗin da zai fitar dan iyalinsa ta ci ta sha ba ƙaramin takura ya ke yi ba.Za ta yi sana'a ne ba dan ta samu kuɗi ko ta nuna gazawar Buba ba sai dan ta taimaka ma sa. Goggo ta yi sana'ar daddawa kuma ba abinda Faɗiman ba ta sani ba gameda harkan. Hebbini kuma ta yi sana'ar ƙosai wanda shekaru uku kafin aurenta ita ke tuyawa Hebbini ƙosan.
Cikin Daddawa da ƙosai da ta iya ta zaɓi ƙosai domin shi zai fi ma ta sauƙi kuma Ladi ta ce za ta fi samun kasuwa.
Da ta gama yanke shawara sannan ta tuntuɓi Buba akan ya ba ta izini ta fara sana'ar ƙosai. Ranan kuwa sai da ta ƙwammaci ba ta yi zance mai kaman wannan ba, ta inda Buba ke shiga ba ta nan ya ke fita ba. Ya haɗa da cewa ta san yadda za ta yi ta haihu tun kafin maganganun da ake faɗa akan ta ya tabbata.
Kenan shi ma ya damu da rashin haihuwar na ta?
Ya za ta yi da ranta ne?, duk magungunan da ake kawo ma ta daga ƙauye babu wanda ba ta sha amma shiru. Ta yi yunƙurin zuwa asibiti Buba ne bai bata dama ba ya ce ba shi da kuɗi...