Chapter 09
*Raudha*
***
Aikin koyarwa na hucin gadi Raudha ke yi a wasu private school guda biyu kafin ta tafi bautar ƙasa. Duk da albashin bai wani taka kara ya karya ba amma a hakan da shi ta ke samu ta ke kula da kan ta da kuma mahaifiyar ta.
Abu na farko da ta farayi bayan dawowan ta gida shine hana Innayi yin aikin wahala.
Ta sani suna samun riba sosai a sana'ar ƙosai sai dai lafiyar Innayi ta fi ma ta komai. Bayan ta dawo ne ta lura da ciwon ƙafar da Innayin ke yi hakan ya ƙara ba ta ƙarfin gwiwa wajen hana Innayi ayyukan da ta ke yi na wahala.
Dan ta sani ciwon ƙafan ya samo asali ne saboda ayyukan wahala da Innayi ta yi a baya kuma ta ke kan yi har yanzu.Cikin wata biyu Innayi ta samu kwanciyar hankali, duk wani yawan ciwon kai da ciwon jiki da ta ke ji duk ta ji sauƙin su. Wannan nitsuwa ya sa ta maida hankali wajen karatu da ta ke yi, bayan na kwana biyu da ta ke zuwa a ranakun weekend ta shiga Islamiyyar dare wanda ake yi a ta kusa da gidan su. Sau huɗu a sati. Ta dena tunanin komai sai addu'ar Allah ya ba wa Raudha aiki ya kuma ba ta miji na gari domin ta ga tausayi a idon Raudha hakan ya sa ta ke da yaƙinin Raudha za ta kula da ita har iya ƙarshen rayuwar ta...
Yammacin ranan wata Lahdi Raudha na zaune tana marking assignment na yara wayarta ya shiga ƙara, Innayi da ke kusa da wajen ta miƙa ma ta wayar.
Murmushi ta yi bayan ta ga sunan da ke jikin screen ɗin sannan ta amsa wayar da Sallama. Idan akwai mutumin da za ta kira da Uba to Dr Ambi ne, akan samu malamai dayawa ma su neman ɗaliban su a makaranta amma Dr Ambi baya ciki, kowa ya shaideshi da kyawawan halayensa. Tunda ta bar makarantar lokaci zuwa lokaci yakan kirata su gaisa ko ita ta kirashi. Ya ƙarfafa ma ta gwiwa sosai wajen ganin ta cigaba da karatu.
Bayan sun gaisa ne ya ma ta maganar wani scholarship da ake cikawa na wa ta makaranta a Malaysia. Ta ma sa godiya tareda alƙawarin a ranan za ta je cafe ta cika...
Ganin yadda ta ke murmushi bayan sun gama wayar ne ya sa Innayi tambayar ko dai sirikinta ne?
"Kai kai Innayi rufa min asiri, ni da aure ai sai na zama likita"
Innayi ta yi dariya ta ce "Allah ya nuna ma na. Amma auren ma idan ya zo za ayi shi ko?"
"Innayi kenan. Wa ki ke ga zai aureni kuma ya bar ni na cigaba da karatu?"
Kafin Innayi ta ba ta amsa sai ga Ado ya shigo gidan yana ƙwalawa Raudha kira da ƙarfi
"Yaya lafiya?"
"Lafiyan uwar ki. Na ce lafiyan uwar ki. Wato Raudha har wuyan ki ya yi ƙwari da har zan yi magana ki tsallake"
"Mi na yi kuma?" ta faɗa a kausashe
"Dan uwar ki ba na ce ki bar dabbobina a cikin gida ba, miye nufinki da za ki kora min su waje ki ƙi bari su shigo gida jiya?"
Miƙewa tsaye ta yi tana kallon Yayan na ta ido cikin ido ta ce " Yaya tun ba yau ba na ce ka nemi mai kula ma ka da dabbobi amma ka ƙi. Yaya Iro da ya ke da zuciya ai ya kwashe na sa, wallahi matuƙar ina gidan nan ba za ka kwaso dabbobi ka ajiye mana da niyyar ni da Innayi ne za mu dinga kula ma ka da su ba"
"Haka za ki ce? To wallahi dabbobin nan su na nan gidan ki ka ƙara kora min su waje sai na saɓa miki"
"Yaya Ado!" Ta faɗa da ƙarfi har sai da ya ɗan tsorata
"Wallahil Azim indai ka ga na bar dabbobin nan a nan to kai ko matarka ko 'ya'yanka za ku dinga shigowa kuna kula da su ne amma idan ba haka ba ba za su zauna a nan ba. Fisabilillahi Yaya wannan adalci ne, ni da Innayi za mu dinga ciyar maka da dabbobi mu na kula ma ka da su, mu ba su ruwa mu share kashin su, ko sisi ba ka taɓa ajiyewa ba. Wallahi..."