AHALI GUDA HAUSA NOVEL📔📖*
'''PART 3'''
✨ *PAGE 9* ✨
_SYESERM_ ✍🏾✍🏾✍🏾
GIDAN MS DEBORAH.
MS DEBORAH: Kifadi duk abinda kikeso ayi miki anything...
But this your decision is impossible Christina.
Kuma Kinga Mahaifinsa bai goyi da bayansa ba ya baki hakuri a madadinsa.
Kuma yayi nadama shima.
CHRISTINA: Mom bazan iya kina magana ina magana ba saboda girma da kike dashi.
Kuma dama na fadi hakane donna tayar masa da hankali kuma nayi hurting nasa kamar yadda yayimin.
I'm sorry i said that...
MS. DEBORAH: No Prob i got you now. Yanzu kifadamin Kin amince dashi Alex din zaki aureshi?
Kinsan idan duniya akanki yake da kuma abinda zakice.
CHRISTINA: Mom ban tabaji na daina sonsa ba koda ya boyeni ba cutar dani yayi ba fitane kawai banayi amman ya samarmin da duk abinda nake bukata.
Saboda haka haryanzu sonsa bai sauya ba saidai ma abinda yaci gaba.
MS DEBORAH: Woww, Saboda haka bazamu bata wani lokaci ba zamu cika miki burinki Christina.
CHRISTINA: Thank You Mom.
Christina cikin murmushi taceda Ms Deborah, ya kasance ita boyetan da Alex yayi ma gaba ya kaita domin yanzu aurenta ne kadai mafitarsa.
DA DADDARE.
GIDAN SU RAYHAN.BABBAN FARLO.
SIYAMA: Wallahi banji dadin abinda ya faru ba.
ABBAS: Ni dama boyemin yakeyi, bai fadamin cewar sunci gaba da mu'amala da ita ba.
SIYAMA: Tinda ta dawo ta sanar dani kowa a gidan nan yasan tana cikin damuwa banda kuka babu abinda takeyi.
ABBAS: Allah Sarki, Allah Ubangiji ya mata zabi da mafi Alkhairy, Amman dama nasani Siyama ba kowane Namiji mai aurene yake son Budurwarsa ta waje fiye da matarsa ba.
SIYAMA: Gaskia ne abindai babu dadi tabani tausayi sosai.
Shima kuma nasan ba laifinsa bane Rayhan ce wani lokacin bata iya bakinta ba.
ABBAS: Allah ya kyauta dai.
Kinaji nayi magana da dangin mahaifina jiya.Kuma sunce na sanar dake cewar ki fada zasuzo domin a nemamin aurenki.
SIYAMA: Thom Shikenan babu damuwa zan sanar da Abbana gobe In Shaa Allah.
Inyaso yadda mukayi dashi kawai saina sanar da kai.
ABBAS: hakan yayi babu damuwa.
Hirar su sukaci gaba ta soyayya.
GIDAN CHAIRMAN FAYZ.
Cikin Daki Najma ta shiga ta tarar da Fayz a kwance yana kallan sama yayi shiru.
NAJMA: Yaya kake zaune kaikai kadai memakon ka kirani na tayaka zama inma shirunne sai muyi tare.
FAYZ: Hmm Najma kenan, ba haka bane amman dama zan kiraki koda zuwa anjima ne.
NAJMA: Kamar akwai abinda yake damunka tinjiya.
Saboda yau ka makara izuwa Office sannan ka dawo da wuri ba kamar lokacin daka saba ba.
Tashi zaune yayi sannan ya gyara zamansa.
YOU ARE READING
AHALI GUDA CHAPTER ONE
Ficción GeneralLABARI AKAN SOYAYYA, YAUDARA DA CIN AMANA, LITTAFIN AHALI GUDA YANA DAUKE DA DARUSSAN ZAMANTAKEWA DA KUMA SAKO NA MUSAMMAN GA MASU KARATU.