AHALINA
(Siblings of different father (s) )
(Book two 'in Aure uku series)
By
CHUCHUJAY
Episode
9⃣➡1⃣0⃣
Zazzaune suka a babban folon dake cikin Gidan Alhaji Bulama kowa da irin saƙa da warwarar da yake,
Baki ɗayansu ne Harda Ummu da Abbi iyayen Imam paki wanɗanda suka amsa kiran na Alhaji Bulama cikin mutunci,kallan Mami Alhaji Bulama yayi yace "yanzu Umaimah Kina tunanin kin kyauta akan Wannan Aure da kika ɗaurawa Nameer daga zuwa bincike Akan yarinyar dake ikirarin ta haifa masa ɗa?,
Ina tunaninki Ya tafi ,i mean koda Auren za'a bazaki dauro masa shi ba daga zuwa ganin iyaye babu wani bincike sosai, ".
"Gaskiya dai abun babu daɗi,menene Amfaninmu mu manyanku,Mai zaisa daga ke sai imamu zaku karbo masa aurenta daga zuwa ganin iyayenta,gaskiya baku ƙyauta ba"
Abbi Ya faɗa yana Mai jin aransa babu daɗi ganin yarda Nameer Ya nuna mutuƙar tashin hankali da Ya tsinci maganar Auren bayan zuwansu gidan Kakan nasu,
Ƙasa mami tayi da kai tana tuna incident ɗin da Ya faru da safe lokacin da taje tashin Nameer a ɗakinsa 'dan yin kari ,a kan gadansa taga Anisa haihuwar uwarta wanda ta tabbatar ba gizau bane sanann da hankalin ta tasan me haka ke nufi 'dan haka cikin rashin dana sanin abinda tayi tace "Abbi da daddy ku gafarceni ,sannan dukkan abun nan ba laifin Papansu bane tunda ko da fari sai da yayi jayayya amma na kafe sannan bayan dawowar mu naga gwanda da aka ɗauro Auren saboda koda muka dawo daddy Nameer bai masan da Auren ba amma a mumunan yanayi na shiga ɗakinsa na tarar da Anisa wanda Ya tabbatar mun da abunda muka yanke ba kuskure bane ba shine rufin asirin mu baki daya,sannan yarinyar nan iyayenta sun ƙarb'eta sun yafe mata ,wanda ganin hakan yasaka nace kawai su bamu Aurenta kuma suka bamu aka dauro".
Ƙaramar dariya ta bakin ciki itace ta ƙwacewa Nameer kana yace "Mami amma koda kika shiga ɗakina Ai baki tarar dani ba ita kaɗai kika tarar,shikenan wani abu Ya shiga tsakanin mu?"
Wallahi a daren ranar ma a ɗakin Abdallah na ƙwana .
Kuka Anisa tasaka sosai tana Mai fadin"dan Allah Nameer kayi shiru haka,mai yasa wai ka kasance mutum wanda baya daukar laifinsa,"Ina mace menene riba ta idan nayi maka sharri?
Kuma 'dan an Kama mu sai kazama namiji Mai tona asirin matarsa?
Na ɗauki laifina jiya da ka kirani dakin ka da dare ban faɗa maka ni matar ka bace wanda nazata kasani ne tunda da kanka ka kirani,to yanzu ba Ya ƙare ba tunda an riga an ɗaura mana Aure .
Dan Allah a bar tone tone.
Tashi tsaye Nameer yayi Ya juya Ya fice a ɗakin yana Mai kunnen uwar Shegu da Alhaji Bulama yake masa ,cos tabbas idan yacigaba da zama a gurin zai illata Anisa fiye da zaton mai zato,
Kallan Anisa Alhaji Bulama yayi yace "Taɗan basu guri ,babu musu ta tashi Ya zaman daga Alhaji bulama,Ummu, Abbi,sai mami da Papa a gurin,
Ajiyar zuciya Alhaji bulama yayi yace "duk wani abu idan bawa yaga Ya samesa a rayuwa to yin Allah ne bana mutum ba ,sannan 'dan adam baya taba iya wuce ƙaddararsa ,wanda Allah yayi maka shine dai dai,dan haka tunda an riga anyi Auren nan to a rufe babin komai,Allah yasa wannan abun shine mafi alheri a rayuwarsu baki ɗaya,".
Amma dole zamu sake bincike Akan ita yarinya ko me kace Admiral?
Kaɗa kai Abbi yayi yace "wannan gaskiya ne dole mu sake bincike 'dan haryanzu hankalina bai kwanta da wannan yarinya ba ."