AHALINA
(Siblings of different father's)
Book two 'in Aure uku series
By
Chuchujay
EPISODE 1⃣1⃣▶1⃣2⃣
Tun Daga soron gidan kake jin shesheƙar kukan Hafsa wadda tayi sa har ta gaji,
Rarrafawa tayi dai dai ƙafar Mama Laure tace"Mama 'dan Allah kiyi mun rai kiyi hakuri,wallahi bazan iya Auren Idi mai faskare ba wallahi 'dan iska ne ,babu irin lalatar da baya yiwa yara duk da tsufansa ,ki tausaya mun ,bani ba hatta babana Ya haifa ,'dan Allah kar ki bari rayuwata ta lalace kamar yarda bazaki so ta hasiya ta lalace ba kiyi mun rai 'dan Allah,Baba ka saka baki,"
Ta ƙarasa maganar tana Mai mayar da kallanta gurin mahaifinta wanda yayi saurin ɗauke kai,
Sake maido da ture kaga tsiya ɗin dake kanta tayi tace"lalai ma yarinyar nan,zakiyi ki gama ki gaji kiyi shiru ,'dan Idi ne sai kin Aura,dama mene kuke wa ke da ubanki,Karatu ko,sannan baku san tallah,shine nayi maki gata ,ga Aure nan Zan maki sannan babu ruwan Idi da karatunki, ke dai kawai ki buɗe masa kafa yayi maki ciki ki haihu,shine amfaninki,sannan na faɗa maki ba lusarin ubanki ba,idan duniyar nan ce zata hadu baki daya babu wanda Ya isa Ya hana na Aura maki idi nan da sati Mai zuwa ,
Tashi tayi a gurin tana Mai faɗin "ni kinga ma fita zanyi hasiya zata fitar mun da hura ,ke kuma ki ɗora tuwo, ".
Da sauri hasiya ta ɗauko bokitin hurar tana Mai fadin dole nayi ma amaryar malam idi wannan karar ,
Suna fita ta koma tayi zaman dirshan tana kuka,bayan wasu lokuta Malam balarabe Ya tashi yayi hanyar zaure ,bayan mintuna Kaɗan Ya dawo gida yana Mai saka masa sakata ,
Ɗagota yayi yace "bari kukan nan haka Ɗiyata ,banyi lalacewar da za'a Aura maki malam idi ba,maza tashi kije dakinku ki haɗo kayanki da komai na amfaninki,"
Kamar wadda bata fahimci abunda yake nufi ba ta miƙe ta shiga ɗakin ta haɗo yan irgaggun karanta cikin tsohuwar jakar saka kayanta ,
A tsakar gida ta tarar da mahaifinta da jakar kuɗi ƙarama Mai Ɗauke da kuɗaɗe ciki,sai wani abu cikin leda a kulle, miƙa mata yayi yace "wannan kuɗin gashi nan zai isheki wani abun ,sannan karatun ki idan Kinje chan kya ɗora ,ledar dake riƙe hannunsa Ya saka cikin kuɗin yace ,wannan ledar zinaren mahaifiyarki ne a ciki wanda ta mutu ta bar miki nake ta maki ajiya ina san sai kinyi Aure na baki,
Cikin shesheƙar kuka tace "baba ina zanje na barka ,."
Shafa kanta yayi yace Hafsatu babu abunda zai sameni, ke dai yanzu ki tafi ,kije ki zama wadda zanyi Alfahari da,sannan ki riƙe mutuncinki kar kiga 'dan bana nan mahaifiyarki bata nan kiyi tunanin Allah baya nan,
Yana nan yana ganinki duk wani abu da zakiyi mara kyau,
Nayi magana da Inna ta Adama jiya wadda na sanar mata da zuwan ki ,tana nan Adamawa Unguwar dawa"
Kije chan Zan na kiran ku a boye a waya ina jin yakike,
Kuka ta saka sosai tana Mai tunanin tafiya tabar Mahaifinta,
Hannunta ya Kama yace "kar ki damu ,muje da kaina zan kaiki tasha na sakaki a mota ki tafi,ƙaramar wayarsa Ya bata yace gashi nan da layina ciki Zan kiraki,"
Cikin kuka tace "Baba dame zaka kirani idan na karbi wayarka,?"
Shafa kanta yayi yace"kar ki damu Hafsatu na zan kiraki ke dai,gaba Ya sakata suka nufi tasha A sace da jakarta cikin hijab.
***********************************
Bayan dawowar Nadiya daga Abuja kai tsaye Abdallah ta kira inda Ya ke shaida Mata yana Office dinsa,