AHALINA
(Siblings of different father's)
Book two 'in Aure Uku series
By
chuchujay
Episode 1⃣7⃣➡1⃣8⃣
Tasowa Harith yayi yana Takowa ga Jamaima kamar babu abunda ta kamasa ya nayi,
Yana ɗaya daga cikin abunda Ya saka ta tsanesa ,a kullum idan zai ganta sai Ya nuna a fili jikinta yake so.
Kallan kuyangar dake ƙarma tayi tace "idan ma nace zan miki wani abu maine zan miki,kije kanki kike cuta saboda shi Yarima Harith ɗin da kike biyewa babu inda zai kaiki sai dai Ya baroki,sannan wani abu Mai daɗi da nake so ki sani,kinyi babbar sa'a da Ya zamana ba nawa bane kuma bazai zama nawa ba,'dan haka ki bace mun a guri sannan idan kika kuskura na sake ganinki sashe na sai na yagaki ,Alƙwarin gimbiya jamaima kenan,kinsan zanyi fiye da haka,"
Bace mun a guri stinky whore .
Da gudu yarinyar ta fita har tana tuntube 'dan tagama sawa aranta ta mutu kawai a sanin halayyar jamaima ,amma ga mamakin ta sai taga akasin haka,
Daf da ita harith Ya matso ,bata matsa ba sannan batayi gizau ba ,jira kawai take taga ƙarshen iskancinsa ƙugunta Ya kamo ya jawota jikinsa yana Mai mata wani irin shafa a ƙugu,
Wani karamin dariya tayi tana mamakin ƙarfin guts ɗin Harith,tayi imani da Allah idan baiyyi wasa ba akan jikinta shi zata fara kashewa,
Kansa Ya sako dai dai saitin kunnenta yace "Ki daina wancan furucin na ni ba naki bane ba kuma Zan zamo naki ba,ƙaddarar mu a haɗe take gimbiyata,Nan da ƙwana uku ki shirya mayar dani lamiɗon ki domin hakan zai faru ko Kina so ko baki so,a yayin da nikuma nake kan murnar da bana tunanin da wani Lamiɗo da zai Kaini,saboda na farko Zan samu masarautar nan sannan na biyu Zan samu sarauniya Mai kyau da diri na jiki nayi yarda nake so da ita Akan gadon milkina,ina mutukar kwadayin jikin ki Gimbiya jamaima ,sannan kar ki damu 6 inch ne D*ck ɗina kinsan babban goro sai magogar ƙarfe., "
Kafun yayi Aune tayi wani irin Hankaɗe sa ta ban mamaki da Kafarta inda Ya faɗi kasa wanwar,binsa tayi ta ɗora Kafarta kan kirjinsa ta taka da karfi kana tace "Abu na farko da nake so ka sani saboda yan iska irin ka koda naje china ba karatu kawai na tsaya ba sai da na samu Black belt a taekwondo ,idan na maka wani dukan sai anyi tunanin hatsarin mota ne kayi,
Kana daukar kanka jarumi ba?
To kai da b'awan gyada a gurina baka da banbanci ,b'awan gyaɗa wanda zanyiwa b'ara ɗaya ya fashe ,gwanda da kasan cewa babban goro sai magogin ƙarfe domin jikina yafi karfin wannan abun dake gabanka da kake bin low life kuyangu dashi ,be guided Next time idan ka kuma tab'a mun jiki Zan saka takobi nasare dukkan hannun ka da Ya taba ni,
Stupid scumbag ,
Yawu ta tofa masa a fuskasa ta bar gurin,
Mikawa yayi yana binta da kallo yana tunanin hanyoyi da dama da zaibi Ya wulakantata ,tabbas da ace baya san zama sarkin garin da babu abunda Zai hanasa yi mata fyaɗe tuntuni 'dan shi jikinta yake so ba ita ba,
Amma yazama dole Ya ƙwantar da wuya muddin yana san cimma burinsa guda biyu,na samun jikinta da kuma zaman sarkin DILAH,."
Tashi yayi daga ƙasan da yake yabar sashen da Tunanin kala kala.
Jamaima kuwa bayan ta shiga ɗakinta Gadonta ta hau ta ƙwanta ta jawo system ɗinta,
Maiyi mata tausace ta shigo,alamu tayi mata da ta tafi ,babu musu ta koma cikin girmamawa,
Page d'in Nameer na Instagram ta shiga,sababbin hotunan sa ta gani da Fadil,
Murmushi tayi tana Mai jin wani irin masifaffan sansa a cikin zuciyarta ,tayaya ma zata iya zama a raba ta da Nameer wanda take jinsa shine rayuwarta?