AHALINA
(Siblings of different fathers)
Book two 'in Aure uki series
By
CHUCHUJAY ✍🏽
EPISODE4⃣5⃣➡4⃣6⃣
Lokaci guda ji da fahimtar Jamaimah Ya dauke domin maganar tazo mata ne a bazata sannan kamar ƙanzan kurege wanda tama san shine ,
Dariya tasa Mai sauti tana Mai Nuna Nadiya ,sai da tayi Mai isarta sannan tace "kalli Nadiya nasan muna da differences namu tsakanina dake ,and nasan abunda nayi miki ranar da kikazo bai kamata ba,sannan Kema wanda kika mun bai kamata ba,Ya wuce lets bygones be bygones ,muyi moving on ,amma wannan kam ba Wasa bane ,idan kuma wasane Ya bani dariya ba sosai ba,so please mudaina kalar wasan nan,im sure sabuwar yar Aiki ce Mami ta bani ko? "
Zama tayi tana Mai crossing Kafarta tace "kin iya zaba mata daki kuwa ba sai nasha wahalar ƙawala mata kira ba ko ita ta b'ata min lokaci,ni dama nasan Mami zata ji dani,dole gobe na shirya naje nayi mata godia,"
Wani irin Kallo Nadiya ta bita dashi Kana ta ɗora yatsunta guda biyu gefen kunnen ta tace"are you nuts"?
Ko kuma wani abu akanki yana miki yumm yumm da yake hana ki gane lissafi?
To bari kiji na faɗa miki,maganar da kike ɗauka kanzan kurege gaskiya ce wadda babu ƙarya ko wani wasa a cikin ta a yanzu wata daya kenan da Auren su kamar yarda akayi naki babu wanda Ya sani,to suma haka akayi nasu wanda ita a wannan karan iyayanmu sun sani kuma sun amince maganar da nake miki a yanzu ma cikin ne a jikinta ,wata guda kinga kuwa tana shiga tayi tuntube dashi, idan baki fahimta ba bari na fasa miki baƙi ,ita da Hamma Nameer sun san juna sun zama abu ɗaya,sunyi consummating Auren su wanda a process ɗin aka samu rabo Mai amfani sannan....
Katsewa maganar Nadiya tayi sakamakon marin da Jamaimah ta ɗauketa dashi ,tana ƙokarin zuba mata wani Nadiya ta kama hannunta tamau tace "kar ki kuma,idan kuma kika kuma zan manta ke matar Hamma ce na ɗaukeki da wanda ba'a tab'a miki ba,kuma Aurene yayi idan kinso ki kashe kanki babu wanda zai hana ki ,na dai san duk jahilcin ki kinsan makomar wanda Ya kashe kansa,So back off zama kuma da kishiya dole. "
Kallan Hafsa Jamaimah tayi da kyau,wani irin faɗuwar gaba ce ta dirar mata musamman yarda taga kyanta Mai ɗaukar hankali Ya bayyana a gareta,
A hankali ta fara takawa gun Hafsat tana Mai faɗin"wanne gangancin Ya sakaki Auren Nameer?"
Mene nayi maki,ban sanki ba baki sanni ba domin mene zaki nemi ki tarwatsa mun farin cikina kin shiga rayuwata kinyi kane kane har ki san mijina wanda ni ban sani ba har da ciki?
Ke ɗin yar gidan uban wace da har kike Da wannan zarar,wanene ubanki a duniya?
Gaban Hafsa Nadiya ta shiga tace "kar ki kai hannunki jikinta koda kuwa da wasa,domin ita keda ragamar hamma a yanzu.
Kamar an tsinkuli hafsa tace "to mene kike maganar me kika mun na auri mijinki na tarwatsa maki farin cikinki,
Ni babu wanda nayi miki a ciki ,ki kalleki da girmanki amma sai ance miki ki kula da mijinki gudun kar Ya gano wata a waje?
Ni a tunanina duk abunda kike takama dashi bai kai ya farin ciki da bawa mijinki na sunna kulawa ba ,ubana ba kowa bane kuma ni ba yar gidan uban kowa bace ba aduniya face ɗiyar manomi wanda ke zaune a ƙauye ,hasalima bani da uwa ,ban samu gatan mahaifiyar da zata faɗamun dai dai ba,amma dai dai gyargwado nasan dai dai nasan kuma menene hakkin mijina akaina ,ba wani girman kai tsakanina dashi sannan gaban iyayensa nima ƴace kamar yarda yake ɗansu,sannan da kike magana ko tunanin na kwacesa Ai abunda Ya kamata Yana samun mata masu sakin mazajensu da rashin sanin kimarsu kenan,kin sake shine Ya faɗo fatsa ta inda na nuna masa soyayya da biyyayar da bai samu a gidansa ba sannan insha Allahu ita zan cigaba da bashi da yardar Allah sannan kema ina fatan zakiyi koyi dani ki sake duk wani taƙama mu bawa mijin mu kulawa ,ni wallahi ba da sharri nazo gidan nan ba ,burina mu haɗa kanmu mu koya ga junanmu mu mutunta juna,babu wanda zai cutu,kiyi haƙuri Adda na nasan kishi yana da zafi,kar mu bari Ya saka muna wa juna kallan mowa da bora.
Wata dariya ke san Kwacewa Nadiya amma ta danneta tana Mai gudun kecewarta musamman da ta kalli irin reaction d'in dake kan fuskar Jamaimah,bata san Hafsa ta san takan iya shege ba domin dama fargabar tafiya ta barta da JAMAIMA take ganin bata da magana sosai ashe ba ƙanwar lasa bace.
Wata irin dariya Jamaimah ta saka tace"the guts for me ,just the guts,and the liver,hannunta ta yarfa tace "Nadiya abuna kuka koya mata ta faɗa mun kenan ko?"
Tafa Hannayenta ta farayi guda biyu tace"kin shiga lion den ki saka a ranki domin wallahi magananganun nan da kika faɗa mun sai kinyi dana sanin su zan tabbatar da hakan,ba dai ni kike faɗawa magana marasa daɗi ba ,zaki san kinyi dani gimbiyar babbar masarautar Dilah"
Ƙaramun murmushi hafsa tayi tace "ni ba magana na faɗa miki ba amma idan kin ɗauketa magana kiyi hakuri ni ba faɗa nazo gidan nan muyi ba ,koda kuwa nace zan faɗa Ai ke Mai hananice saboda ina ɗauke da cikin abunda kike so,kiyi hakuri Addana ta kaina gimbiya a babbar masarautar Dilah kawai".
Rasa abun faɗa Jamaimah tayi 'dan haka ta yi snapping hannu ta bawa Hafsa wani irin mugun kallo Kana ta koma kan Nadiya wadda ta ɗaga mata gira guda ɗaya ,ƙwafa tayi kamar an hurata da iska ta fita a Falon kamar guguwa,
Dariyar da Nadiya ke san riƙewa ce ta Ƙwace sosai har tana faɗuwa,kallan Hafsa wadda ke faman murmusawa tayi tace"you're Naughty ,kinga fuskar gimbiya kuwa"?
Dariya Hafsa itama tasa kana tace "Ni dai Aunty tsoro nake ji kar cikin dare tazo ta shaƙe ni"
Dariya Nadiya ta kuma sawa tana Mai nuna Hafsa tace "You're kidding me ko?"
Lokacin da kika saka gimbiya dimuwa ban sani ba kinga kuwa idan tazo shaƙeki yau da daddare ina gidan Papana Babu abunda Yayi mun dumi,wato gimbiya a babbar masarautar Dilah ko? .
Da sauri hafsa ta taso cos tafara tsorata tace "amma Ai Aunty kina nan fa baki hanani ba ,ni dai sai dai Nabiki gidan Papan gobe sai na dawo"
Dariya sosai Nadiya tasa ganin tsoron fuskar Hafsa ,zama tayi da ita tace "Look What you did was amazing like ban ma taba tunanin zaki saka ta wurinta ba a ɗan wannan lokacin,amma naji daɗi sosai da Ya zamana kina da zarrar domin Jamaimah sai Mai zarra,kinga yanzu da kika mata haka im sure shakkarki ta shigeta sannan Hamma gidannan zai kwana babu abunda ta isa tayi miki duk haukanta kuwa ,responsibility ɗinki na kan Hamma wanda im sure zai kula dashi ɗari bisa ɗari bani da wannan shakkar,dan haka yanzu ki tashi mu shiga kitchen na tayaki haɗa dinner kafun na wuce ,shima wani babban bangarene na Plan ɗinmu".
Bayan sun gama komai suka wuce kitchen domin haɗa dinner inda Nadiya ta barwa Hafsa ragamar Girkin ta wuce ɗakin Nameer domin gyara masa,basu ji muryar ko motsin Jamaimah ba wanda Ya tabbatar musu da bata gidan ne.
Tunda Jamaimah ta fito daga ɗakin hafsa take kiran wayar Nameer amma ƙarshe sai message Ya tura mata na yana meeting ne wanda Ya sake hassalata ta nufi office din nasa domin ci masa mutunci a chan,
Tuƙi kawai take amma Kana kallanta ba sai ta faɗa maka tana cikin tashin hankali mara misaltuwa ba,idanunta yaƙi daina zubar Ƙwalla wanda batayi kokari wajen hanna ƙwallar zuba ba domin ta yarda da Ya kamata ace ta zuba ɗin,
Kai tsaye tana isa company ɗin Nameer Sashen da zai sadata da ofishin sa ta nufa tunda ba ranar ne zuwanta na farko ba,kamar ance Fadil Ya ɗaga kai ya hangota ,da fara'arsa Ya ƙarasa gareta yace "wa nake gani kamar Jamaimah ,uwar gida ran gida idan babu ke babu gida,yana kai ƙarshen maganarsa yayi dai dai da sauke masa yatsunta da tayi a fuska ta nuna sa da Yatsa tace"munafiki annamimi,ko me Nameer zaiyyi da sannayyarka tun ba yau ba nasan Ai ku abokan shawarar juna ne daga Mai kyau zuwa mara kyau shine yau iskancinku da ta'addanciku zai fara ta kaina ko? "
Zaka wani ɗauko kayan dirty mouth ɗinka Kana wani faɗamun uwar gida ran gida,ko ba uwar gida ba,to wallahi Ahir ɗinku,Aure na da Nameer babu wanda Ya isa Ya lalata sa idan ba Allah ba,
wallahi sai na ci muku mutunci tunda kuka ci nawa,har ni za'a kaiwa wannan yar shillar gida matsayin kishiya?
Aikuwa wallahi sai dai idan Ya zab'a koni ko ita idan ba haka ba kuwa za'a mutu.
Wanene zai mutu?
Muryarsa ta ziyarcesu .
Ɗaga idanunta tayi ta sauke cikin nashi,tsaye daga ɗan nesa dasu hanunsa cikin aljihuns yana Mai binsu da kallo,
Cikin haɗe rai Sosa Ya tako gurin yace "mene kike yi anan wanda bazaki iya jirana na dawo gida ba har sai kinzo wurin aikina kin tara mun mutane,Inajin na faɗa miki ina meeting ne".
Wani irin Abu ne Ya tsaya mata a wuya jin abunda Ya faɗa mata wanda Ya sake tabbatar mata da maganar Hafsa na ta Ƙwace mata shi wanda Babu Ma yarda za'ayi hakan ya iyu.
Ganin bata ce komai ba sai ruwan hawaye dake zuba a idanunta ne Ya saka shi takawa gareta Ya kamo hannunta Ya jata suka fara tafiya,bai tsaya ba sai da Ya kaita motan da tazo dashi ya sakata ciki kana yace "bani key"
Kamar tana jira ta jefesa dashi,bai ce mata komai ba Ya tashi motar suka nufi gida,duk tukin bai ce komai ba ,babu abunda ke tashi a bakin Jamaimah sai sautin kuka Mai cin rai,
Koda suka isa gidan bai ƙasa a gwiwa ba Ya zagaya Ya buɗe mata amma taƙi fitowa,ganin zata bata masa lokaci Ya sakashi ɗaukar ta bridal style Ya tura ƙofar da ƙafarsa,kamar Mai jira ta lafe jikinsa ta cigaba da kukan da bai lallashe ta ba.
Bayan shigarsu ciki ɗakinta ya kaita ,yana jin motsin su Nadiya a ɗakin da Ya bawa Hafsa cos dama yace Nadiya ta jirashi Ya dawo ,
Zaunar da crying JAMAIMA yayi a kan gado Ya tsaya yana Mai saka hannunsa a ƙugunshi yace "abu na farko da nake san ki sani kuma ki saka a bayan zuciyarki da ƙwaƙwalwarki wanda shine "bana so koda wasa ki sake zuwa mun office a yanayin da kikaje mun yau ,duk wani shirme dake kanki ki bari idan na dawo gida kiyi shi amma banda gurin Aikina cos a nan gurin ni abun girmamawa ne dan haka baki isa Kina ƙasana kije har gurin da nake shugaba ba tozartani,wannan Ya zama na karshe da zan miki kashedi."
Yana kai ƙarshen maganarsa Ya juya zai bar ɗakin,
Da sauri ta kamo rigarsa ta fashe da wani irin kuka tace "me nayi maka da kake neman kasheni Nameer?"
Mene nayi maka da kake so ka raba mun rayuwata da gangar jikina,Mai yasa zaka mun wulakanci mafi muni kamar haɗa jikin ka da wata har kayi mata ciki ,ciki fa Nameer yana nufin kunyi having sexual intercourse wanda koda wasa baka tab'a attempting sa akaina ba,
Tashi tayi tsaye tana Mai juyawa da kyau tace"ka kalleni mana,Shin banyi tsarin da zaka nema bane ko kuma bani da ɗaukar hankalin da zaka kusance ni,"?
Wani irin kuka ta fashe dashi tace "wallahi bazai tab'a iyuwa ba ,bazan taba yarda ba ,wancan cikin dake jikin ta sai an zubar dashi,idan kaga an haifesa to na mutu ne sannan yarinyar chan da take kiran kanta matarka ko da tsiya koda Arziƙi sai tabar gidan nan ,wallahi bazan yarda ba idan kuma ba haka ba za'a fitar da gawar ta ".
Fizage rigarsa yayi yana mata wani irin kallo,bai san inda maganar ciki ta fito ba amma shima ɗin wani abu ne,tabbas yana mutuwar san Jamaimah ta yarda yake jin bazai iya rayuwa da kowacce mace ba face ita ,amma halayyar ta abun ƙyama ce wadda take buƙatar gyara muddin kuwa tana san tsira,gyara tsayuwarsa yayi Ya nemo dukkan wata fitina Ya saka a idanunsa yace "dan Allah jamaima ki gwada zubar da cikin da ke jikin yar Aljanna kiga yarda zan maki dukan kato gidan nan ,kina maganar a fitar da gawar ta ko?"
To dan Allah ki taba ta kiga yarda zan baki mamakin da baki taba tunanin zan baki ba sabida yar Aljanna a yanzu da kike gani itace rayuwa ta saboda ita ɗin macece maratussalaha ,ki sani kuma ki saka a ranki xama a gidan nan yanzu ta farashi a ƙarƙashin soyayyata da kulawata ,tunda ita ɗin nan da kike gani na farko bata da girman kai,sannan bata da raina na gaba da ita da abubuwa da dama wanda na san idan kina zaune zaki fahimta ki gane dalilin da yasa ta mamaye ko ina na zuciyata ta,tsakanina kuma dake babu saki na faɗa maki ina sake faɗa miki ,idan kin ga dama a gobe saboda yar Aljanna ki koma Masarautar Dilah amma fa ki sani da Aurena akanki zaki koma domin idan kinga Aurena Ya kunce daga kanki mutuwa nayi indai nine zan sakeki kima cire batun akanki,sannan Zama da yar aljanna dole.
Juyawa yayi ya fara tafiya,cike da balai tace "Ai ni yar wuta ce idan kuma ka ganni cikin Aljanna ka maidani wuta,kuma wallahi koda kaƙi koda kaso ni kaɗai zaka so a rayuwarka,sannan wannan yarinyar zata sani"
Dariya Ya saka Ya Kalleta yace "Allah sarki nima bance bana sanki ba Ai kawai dai ina san ki sani a yanzu Yar aljanna ta ƙwashe rabi da kwata na zuciyata ,ke kuwa sai rabe rabe ,sannan kema bana fatan ki shiga wuta sai dai idan bakiyi wasa ba a borata zakije aljanna"
Yana kai ƙarshe ya fice,wani iirin ihu ta saka tana Mai watsi da duk wani abu dake kan mirror ɗinta .
Kai Tsaye Nameer na fita ɗakin Hafsa ya shiga ,
Yana shiga ya fashe da wata irin dariya ,duk da Nadiya bata san Mai Yakewa dariya ba amma haka dan tasan Jamaimah tayi wani abun,
Kallan Hafsa yayi yace "ina kuka samo maganar ciki?"
Dariya Nadiya ta kuma darawa da tace "Ai ta gama ihunta a haka zata haƙura ta sauko ,ce mata nayi Ai ciki ne da hafsa".
A tare suka dara suna maida zancenCHUCHUJAY ✍🏽