Bismillahir Rahmanir Rahim
Dukkan yabo da ɗaukaka sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki, wanda ya halicci duniya da abinda ke cikinta. Tsira da abincinsa ya ƙara tabbata ga annabin Muhammad (SAW) da alayensa da sahabbansa.GARGADI
Wannan labarin ƙagagge ne, an yi shine domin faɗakarwa, wa'azantarwa da kuma nishaɗantarwa. Sannan kuma dukkanin haƙƙin mallakar sa abin kiyaye wa ne, don haka a kula kuma a kiyaye.
KYAUTARWA
Gare ku iyayena, Alhaji Umar Aliyu da kuma Haj. A'ishatu Ɗahiru. Allah ya ba ku tsawon kwanaki masu albarka, sannan ya cika rayuwaku da albarkarsa. Ameen.**********************
Kowa ka kalla cike yake da fara'a, a yayinda mutane ke tururuwar shiga cikin makarantar, ɗalibai kuma na tarbo jama'a zuwa cikin ɗakin taron sannan a hannu ɗaya kuma malaman makarantar na taya su da nunawa baƙi wajen zaman su.
Farin ciki biyu nake yi a wannan ranar, murnar kasancewar na kammala makarantar gaba da firamare sannan farin cikin kasancewar ilahirin 'yan gidanmu a wajen taro, in ban da ƙanwata Sauda, da ita ma take makaranta a lokacin.
Fara taron babu daɗewa ne, Allah yayi wa tawagar gwamna na wannan lokacin, Alhaji Salihu Kabir, isowa, tare da Kwamishinan Ilimi da mukarrabansa. Manyan baƙi sun yi jawabai a kan abinda taron ya ƙunsa, kafin daga bisani mai girma Gwamna ya yi na shi jawabin. Jawabinsa ya ƙunshi nuna jin daɗin sa akan yanda ɗalibai mata, kuma 'yan jihar Kano su takwas suka lashe jarabawar kammala makarantar sakandare da sakamakon da ba'a taɓa samun shi ba. Dukkannin mu daga makarantu mabanbanta muka fito (ana taron ne a makarantar mu, kasancewar ta mafi girma).
A ka fara kiran mu kuma don sauran jama'a su ga waɗanda aka yi taron domin su. Ta cikin amsa kuwwa sunayen Sadiya Umar, Sadiya Aliyu, Sadiya Abubakar, Sadiya Zannuraini, Sadiya Kabir, Sadiya Abdul Manaf, Sadiya Mansur da Ummu Kulsum Aminu (Ni kenan, kuma Ni kadai ce daban a cikinsu) ke tashi.
Kowa mamaki ya cika shi ganin sunayen duka iri ɗaya, har mai gabatarwa yana cewa ko nasarar na da nasaba da sunayen ne, kowa ya dara. Gwamna yayi mana kyautar dubu ɗari biyu da hamsin kowanne mu. Cike da murmushi na juya na kalli sashen da Mama, Baba, Yaya Muntari, Yaya Mahmoud, Yaya Zainabu, Yaya Naziru sai ƙannena 'yan biyu Hassana da Hussaini, suke zaune fuskokinsu cike da annuri. Kafin daga bisani manyan baƙi su ma suka yi mana ta su bajintar kafin a rufe taron.
A gajiye na koma gida. Su Mama sun riga mu dawowa. Yaya Muntari ne ya jira Ni na gama sallama da ƙawayena, bayan ɗaukar hotuna sannan muka taho. Wanka na fara yi kafin nayi sallah, na bi lafiyar gado don rage baccin da yake kaina.
Wurin magriba na farka, raina ya fara ɓaci, ga jikina kaman an yi mun duka. Illar baccin la'asar kenan. Wanka na sake yi don na samun ƙwarin jikina sannan nayi sallah na fito.
Falo na dosa in da kusan kowa yake zaune idan ka ɗauke Sauda (tana makarantar kwana), Baba da Yaya Zainabu. Ina shiga na ji Mama tana tambayar Yaya Naziru ko ya gama haɗa kayan shi? Ban ma jira ya amsa ba da sauri nace "Au! Yaya Naziru satin tafiyarku ya kama ne?"
"Ai ba za ki lura ba, kina ta sabgar gama sakandare "
"Ni ai mamaki ne ya kama Ni, nasan dai mobilization list ya fito, amma ban san har kun karɓi Call -up letter ba" Na faɗi ina ƙoƙarin zama.
Yaya Mahmoud ya amsa " Ummu rabu da shi, wasa yake yi maki. Yanda suke ɗokin zuwa camp shi da Zainabu ai dole ne ma ki sani. Tare zamu tafi da shi."
A shagwaɓe nace " Kai Yaya Mahmoud don Allahhhhhhhhhh"
Mama ta taɓe baƙi tana cewa " Ji mu da yarinya, to da ke zai tafi ya bar Naziru a gida?"
Cikin sauri nace " To ai Yayan ne ya ƙi aure bare Ni ma na dinga bin shi, gani da son zuwa garuruwa"
"Da yake Ni kika fi gani dai-dai da ke ba? Amma ai ga Yaya Muntari ba kya maganar auren sa sai nawa. Gara Ni ina da budurwa, a gidan nan akwai wanda ya taɓa jin an ce ga budurwar........?" Filon kujerar da Yaya Muntari ya jefo masa ne ya katse maganar, a take kuma gaba ɗaya aka kwashe da dariya.
YOU ARE READING
Kowa da Ƙaddararsa
RomanceLabarin kowa da ƙaddararsa, labarin Ummu Kulsum ne on how her life took an amazing diversion from what she plans to something totally out of control. What doesn't kills you makes you stronger. The ups and down wasn't entirely pleasant but neverthele...