2

2 0 0
                                    


   Kusan za'a iya kiran gidanmu da gidan 'yan boko. Ga misali, Yaya Muntari malamin jami'a ne a FUT Yola, yanzu haka digiri na uku yake shirin kammalawa. Yaya Mahmoud kuma saura external defense ya yi saura ya kammala digiri na biyu, amma yana aiki a Minna ta jihar Naija. Yaya Zainabu da Yaya Naziru sun kammala digirin farko ne, suna shirye-shiryen tafiya bautar ƙasa (Yaya Naziru ya yi spill over ne shi yasa tafiyar ta zo masu lokacin ɗaya).
   Ni kuma Ummu Kulsum da aka fi kira na da Ummu, na kammala sakandare da distinction (A) guda 9. Sai Sauda da take aji biyar na babbar sakandare. Biye da ita kuma 'yan biyun Mama watau Hassana da Hussaini, waɗanda suke aji biyu na ƙaramar sakandare.
  Ni ma abin da ya ja mun tsaiko wurin shiga jami'a rashin rubuta jarabawar Jamb ce. Ko ban faɗa ba, nasan zuwa yanzu kun san irin baiwar da Allah ya ba Ni na ɗimbin ƙwaƙwalwa, hakan ya sa ba Ni da fargaba akan jarabawar.
  Ranar Litinin gidan ya watse, Yaya Naziru da Yaya Zainabu sun tafi camp, shi an tura shi Gombe, ita Taraba. Ragowan kuma duk sun koma wuraren ayyukan su. Hakan ya kasance mu uku kaɗai muka rage a gida tare da su Mama da Baba.
   A wannan lokacin ne na himmatu da yawaita karatu da safe, da yamma kuma na samu wata islamiyya a kusa da gidanmu nake zuwa. A haka har lokacin jarabawar ya zo, kuma na rubuta ta cike da zaton samun nasara. Sannan na tattara hankalina gabaɗaya a islamiyya, kasancewar Ni ce koma baya a gidanmu, don sun tsere mun nesa ba kusa ba.
   Bayan sati Uku sakamako ya fito (yanda aka saba a shekarun baya), kamar yanda na tsammata, na samu Maki 283. Duk da haka gani nake ƙwaƙwalwata tafi ƙarfin haka, ina ma laifin maki ɗari Uku. Yaya Muntari ya shiga ciku-cikun sama mun admission anan jami'ar Bayero da ke Kano.
Allah ya yi Ni da rashin son zama haka, sai na fara neman abubuwan da zan cike lokacina da su, kuma su ɗauke mun kewa. Ɗakin Yaya Naziru na fara bincike, don na san shi da karance-karancen littattafai. Shelf guda gare shi da ya buga da kansa cike fal da littattafai. Kasancewa ta sabuwar 'yar karatu sai na zaɓa daga cikin marasa yawa, don haka da James Hardly Chase na fara, ganin na ga wasu na shi sun kai hamsin a ɗakin.
Rashin sabo ya sanya sai da na kwana tara a guda ɗaya, don idan na ajiye shi ma mantawa nake da shi. Amma dai na fara ɗaurewa, don sabon da na fara karantawa kwana huɗu ya ɗaukeni.
Ranar wata Lahadi da yamma Mama ta aike Ni Ƙofar Na'isa gidan Kakarmu karɓo maganin basir. Da ɗoki na hau shirin tafiya, sanin akwai sa'o'i na a gidan. Ni har mamakin ɗokin da nake yi nake, ganin Ni ƙawaye basu dame Ni ba, don zan iya cin laya ba ni da Aminiya sai ƙawayen aji ko hostel, kuma bai fi mutum biyar na taɓa kai wa ziyara har gidajensu ba.
Na sauka dg cikin ɗan sahu daidai kwanar layin, kasancewar ba Ni kaɗai ce fasinja ba, na ba shi kuɗin shi na juya na shiga layin domin ƙarasawa gidan. Kamar wadda aka taɓa sai hankalina ya sauka kan wata mota da take ƙoƙarin barin layin, matuƙin motar ne ya ɗauki hankalina. Ban san ya aka yi ba, amma tabbas daskarewa na yi ban cigaba da tafiyar ba, kuma na zuba masa ido. Ina jin jikin sa ne ya ba shi ana kallon sa, ya juyo ɓangaren da nake, ya kalle ni a taiƙaice ya ɗauke kansa ya kuma sake juyowa ya sake kallo na da alama mamakin irin kallon da nake masa yake yi. Sai kuma ya gyaɗa kan shi, fuskarsa cike da kadaran-kadahan ya fice daga layin ya bar Ni a nan.
Ajiyar zuciya na saki sannan na ɗaga ƙafa ta da sauri cike da kunyar abin da nayi. Ina tafe ina ɗan waiwaigawa ko wasu sun lura da abin kunyar da nayi yanzun nan har na ƙarasa gidan. Nan ƙofar gidan na iske kawunai na da jama'arsu zaune bisa tabarma suna ta hira. Na tsaya muka gaisa sosai kafin daga bisani na wuce ciki, ina kuma jiyo kawu Habibu yana tsokanata (ƙaramin uba aboki, don bai wuce Yaya Muntari a shekaru ba) amma ban kula ba.
Ihun da su Faɗimatu na murnar gani na da suka yi ne ya jawo hankalin ragowan 'yan matan gidan zuwa gare mu. Sai da muka ɓata lokaci a wurin kafin muka ranka ya ɗakin Hajiya, nan ɗin ma bamu daɗe ba suka ja Ni muka koma ɗakin su.
Ban ma jira mun ɓata lokaci ba na hau basu labarin abin kunyar da na yi babu daɗewa ba. Shewa gabaɗaya suka sa har da tafawa. Safina tace "To haɗuwa yayi haka ko so ne yayi maki dirar mikiya? Suka sake ƙyalƙyalewa da dariya.
Ni ma cikin dariyar nace "Ni kam wa ya sanar mun ne? Worst part ɗin ma shine sau biyu yana kallo na da ya ga naƙi barin kallon shi kafin ya wuce ya abun sa."
Rahma cikin dariya har tana riƙe ciki tace "Amma ya kwafsa maki, maimakon ma ya taimaka ya taya ganin ki zama dumbfounded". Haka suka yi ta tsokanata ina bayarwa muna nishaɗi. Sai magriba na koma gida, chan kuma na iske Yaya Zainabu ta zo, murna ta cika ni na samu abokiyar hira a ranar, don kam sai da dare yayi nisa muka kwanta
Zuwa yanzu na zama gwanar karance-karance, don kam kaf James Hardly Chase ɗin dakin Yaya Naziru na gama su har na fara komawa kan masu yawa irin su Sidney Sheldon. Hakan ya sa muka fara musayar littafi da Safinar K/Na'isa domin ita ma gwanar karatu ce. Sai dai ina ja mata kunnen ta kula da littattafan da kuma dawo su idan ta gama, don na fi kowa sanin halin Yaya Naziru akan littattafan da ba ya ɗaga ƙafa.
Yau ma tun safe ta kira Ni a waya wai na duba mata ragowan wani series Na David Baldacci, ta karanta biyu sauran sun kasa samu ita da mai bata aro. Da yake Ni tuni na karance su shi yasa nasan yana da su, don haka na yi mata alƙawarin kai mata su da yamma da kaina tunda babu islamiyya.
Da yamma na kwashi litattafan har da ragowan wanda ta bani aro, wasu romantic novels ɗin Sara Craven, don Yaya Naziru baya mu'amala da irinsu.
Yau ɗin ma kamar koyaushe su Kawu Habibu na iske wajen da suka saba zama da yamma idan sun dawo daga wurin aiki/kasuwa tare da abokan su na unguwa. Muna gaisawa Kawu Habibu ya karɓi litattafan hannuna ya na dubawa, don haka sai na bar ma shi anan na wuce ciki abu na, idan ya gama gani ya shigo da su don gab ake da kiran Sallar magriba.
Ko minti goma ban wuce ba, wani yaron maƙota ya shigo wai Kawu na kira na. Yana gani na ya ce "Yauwa Ummu, wannan ne yace ki ba shi aro don Allah ya karanta sauran Divine Justice kaɗai bai karanta ba." Na juya na kalli wanda Kawun ke nuna mun. Gaba na ya faɗi, fukarshi kamar na san shi amma na gaza tuna a ina, na dake nace "Ba komai, amma Ni wanne zai ba Ni? Don ba'a bayar da aron littafi haka nan dole sai an bada wani."
Yana dariya ya amsa "Ashe 'yar hannu ce" ya karkace ya zaro littafi daga aljihun wandon sa na baya ya cigaba da faɗin "Ga wani sabo, ina fata kina da saurin karatu don ɗazun nan na siyo shi. Littafin Dan Brown ne Da Vinci Code."
Na amshi littafin tare da faɗin "Saurin karatu ya danganta da daɗin littafi ne, amma kar ka damu zan gama da wuri, Nagode." Na kwashi ragowan littafan da na bari ɗazu wajen Kawu Habibu na koma ciki daidai amma kiran Sallah. Ba yan da Safina ba tayi na bar ma ta wanda aka bani aro ba, naƙi. Nace mata idan ya gama da wanda na ba shi aro nan gidan zai kawo, saboda haka idan na gama zan aiko mata, in ya so bayan ta karanta sai ta mayar masa da abin sa.
Na isa gida na iske albishir daga bakin Baba cewa Yaya Muntari ya bugo waya ɗazu, gobe na je makaranta na duba serial number ɗina a jami'a domin karɓo admission letter, wai ma an kwana biyu da kafewa sunayen sabbin ɗalibai da aka ɗauka.
Wani irin farin ciki ne ya lulluɓeni har da ihuna na doshi ɗakinmu, har tsoro na ba wa Sauda (suna hutu) da Hassana. Kai! Na ci wa boko buri, gani nake ma sai na fi Yaya Muntari zurfin karatu, don ban cire ran zama Farfesa ba kafin na gama tara yara.

Yayımlanan bölümlerin sonuna geldiniz.

⏰ Son güncelleme: Jan 27 ⏰

Yeni bölümlerden haberdar olmak için bu hikayeyi Kütüphanenize ekleyin!

Kowa da Ƙaddararsa Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin