1-2

11 1 0
                                    

*LAULAM* ( _Kishiyata_ )

                Na

        *{SADEEY}*
         _'Yar Gatan Royal Star_

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
       {R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
  *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
      

Page....1&2

______Ta fara nisa cikin gyan-gyad’in data fara, wanda har ya kai ga mafarkan bazata sun fara ziyartar k’wak’alwarta, ba tare da zato ko tsammani ba taji sauk'ar ruwa mai sanyin gaske yana ratsa dukkan sassan jikinta.
Sanyin ne ya ratsa ilahirin jikinta wanda yayi sanadiyar farkawarta cike da fargaba, tsoro, da razani duka lokaci guda suka dirar mata, ba komai ya haddasa mata hakan ba sai dan sanin cewa Inna ce kad'ai mai mata wannan aika-aikar.

Kuka ta fashe dashi wanda yai sanadiyar k’aruwar ɓacin ran Inna har yakai ga ta d’aka mata duka tare da cemata ”Munafukar Yarinya!  yanzu tadakin da nayi donki tafi d’ibamin ruwa ashe baccin naki na asara kika cigaba dayi anan?, lallai kin isa kuma jikinki sai ya gaya miki, inhar baki tashi a gurin nan ba,”

Inna ta fad’i haka tare dasa k’afa shureta sannan ta wuce tana bambami.

kuka ta ke tare da rawar d’ari haka ta nufi inda tulun d’iban ruwanta yake  dauk'a tayi sannan na nufi rafi, don dib'o mata ruwan da rashin d'ibosa ba k'aramin yak'i zai tayar a gidan ba, don muddin bata d'ibo ba, to na lahira sai ya fita jin dad'i a wajen Inna.

Tafiya ta ke a hankali hanyar shuru had’u da kowa ba saboda lokacin yawancin al’ummah suna gida suna bacci wasuma suna kaiwa ubangijin halittu kukansu, don ba lallai wassu sun tashi daga inda sukayi salla ba, kasancewar gari bai gama wayewa ba,

Tafiya ta ke tana had'a hanta sa boda gyan-gyad'n da ta ke yi haka har ta isa rafin, kasancewar suna da tazara sosai da rafin amma hakan baisa Inna ta jin tausayinta ba, watannin baya da suka wuce wani mai kud’i yashigo garin nasun tare da sakawa aka jawo musu ruwa kusa dasu, amma saboda son zuciya irin na Inna tace bata son ruwan dake fitowa daga k’arfe na rafin ta ke so. Haka  ta isa  rafi  na deb'o ruwa.
 
Wanda ya ɗauketa lokaci mai tsawon gaske, a daidan wannan lokacin ne
Kuma Inna ta fito tana gyara ɗaurin  Zaninta tare da yin dogon hammah.

kallon ILHAAM tayi tare da jan dogon  tsaki "tace   me kike kallona da shegun idanu kaman na mayu  nikam karki cinyeni Mayyah  kawai, mai siffan aljanu, Shuru  tayi tare da sadda  kaita ƙasa domin tana mugun tsoron Inna.

Inna buta ta ɗauka  tayi hanyar band'aki. tana fitowa daga band'aki tayi hanyar Badauru (madafi) domin yin d'umame. Kallonta tayi kana tace" kije daki ki tayar min da 'yar Lele, sauran ki mata mugunta irin wacce kika saba. wallahi sai na sab'autak'i, don na lura hassada kike da ita, kuma ki sani ko zaki mutu ta fiki wallahi.

D
Ita dai da to ta amsa kana ta kama hanyar shiga ɗakinsu, inda suke kwana tare, ita a gado a yayin da ita kuma Ilham ta ke kwana akan taburma,

Kallon yarinyar dake bacci nakeyi wacce a girme ta girmeta, kawai iko ne da isa irin na Inna da kuma gadara. Hannu tasa a gefen kumtunta ta fara tada da daga bacci ta hanyar ta6a kumatun tare da kiran sunanta.

Ido ta buɗe tana sakin doguwar hamma, ganin  Ilham ce yasa ta saka kuka mai ƙarfin gaske kaman wacce aka cirewa ido, wanda yasa Inna faɗowa ɗakin kaman an jehota, har tana tuntube, zanin ta a hannu yana neman fad'uwa. Cikin kidima tace " 'Yar Lele mene ne? Gaya min meke faruwa? Kukan me kike da ga tashin ki? Baccin ne bai isheki ba ko me? Ta karasa jera mata tambayoyin cikin son abunda ya saka ta kuka.

Cikin maganan ta na taɓararrun yara da aka gama sangartasu ta fara cewa "ba  Ilham bace ta dinga kwad'amin mari ina cikin baccina, ta k'arasa maganar tana saka kukan k'arya, bore na zallan k'arya da Munafurci,

Tass! Inna ta d'auke 'yar k'aramar fuskarta da mari, wanda yayi sanadiyyar ganin gilmawar wassu taurari na wani lokaci a gaban idonta, bata dawo daga hayyacina ba ta fara fad'in "wato dai ni ban isa na sakaki kiyi abu, kuma kiyishi ba ko? tayar da  itan da nace kiyi shi ya baki daman marinta, to wallahi irin haka ya kuma sake faruwa zaki ga  yadda zamu kwashi adashen tsiya dake, shegiyar munafuka mai fuskar salihan bayi, annabi a fuska firauna a zuci, wallahi Ilham idan kikayi wasa ni zanyi ajalinki! Ina rike dake amma baki da makiyan da suka wuce ni da 'Yata, to wlh aniya bi aniya, aniyar mod'a tabi randa, hegiyar gora mai zubda ruwan alwala, wuce ki ban waje, kuma yau baki da abincin safe a gidan nan, naga uban da zai baki sai ki d'auki kwano ki tafi bara,

Kuka ta ke yi tamkar ranta zai fita, tunda taji sauƙin mari akan kumatunta, dama tasan hakan ne zai kasance dani, kullum haka Zainabu take mata bata daketa ba  tace ta daketa, Inna kuma sai ta yarda kuma ta rama mata, gashi Allah yayi ta mai tsoron duka musamman mari, don gaskiya ita mugun tsoron mari musamman hannun Inna duk da zata iya cewa ba Wanda ya taba marina a garinmu, to dukkansu tausayamin suke sai bala'i da masifar Inna ya hana kowa ya bayyana tausayawarsa a gareta, shi yasa kowa yake nuna halin ko in kula akan ta, domin duk fad'in kauyen nasun babu ta biyun Inna kasan cewarta masifeffiya ta rubutawa a Jarida,m.

Hannun Zainabu taja suka fita waje, kafin tace mata "aikin san ayyukanki ko? to dan Allah karki zo kiyi kici gaba da tsayuwa kina min kukan munafurci,

Fita sukayi hakan yasa tabi bayansu, ruwa tasa a buta ta miƙawa Zainabu a yayin da ita kuma Ilham ta d'auki  tsintsiya don yin shara, duk da ba wai ta iya sharan ko ta kai munzalin yinsa bane, sai dai a hakan take yi randa ta tashi gallazamin sai ta sakani sake sau biyu sau uku duk ba damuwar ta bane, bayan ga Zainabu ba aikin fari bale baki, tana nan kaman kashin maciji, ba taki ba magani.

*******
Bayan  Inna ta gama ne
Ta kalli gefen da ta ke, tare da jan dogon tsaki  kana ta ce "wato ke baki san ya kamata ba ko?  sai na gaya miki kullum?  Kinfi son kullum ayita abu kaman alwala ko?

Shuru  tayi  tare da tashi saga inda ta ke zaune ta iso a d'an nesa da inda Inna take,

Sunkuyawa tayi da niyyar ta daukan akushin da aka saka abinci karin Bappah. ba zato ba tsammani taji saukan  dundu a bayanta wanda ta jishi har cikin ranta, kuka tasa tare da tsugunawa kasa, Kafah Inna ta sa sake  sure ta da kafarta, wanda yayi sanadiyyar  buguwar kanta ajikin gini, ihu tasa  wanda ya k'ara hasalar da  Innah a karo na babu adadi. cikin haushi da kuma rashin controlling fushinta, ta wawuri itacen murhu  wanda yake da wuta ba tare da tayi tunanin Komai ba ta jefini dashi....

Ayi sharing fisabillah👏👏

07041353907
Sadeey ce

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 04 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

LAULAM (Kishiyata) Where stories live. Discover now