page 1

0 0 0
                                    

NA TSANI MATA

WRITTEN BY NAMEERAH ABDOUL

🅿️1

Bismillahir Rahmanir Raheem

Ina godia sosai ga fans Dina masu nuna min so da qauna
Allah ya bar zumunci Allah ya bani ikon kammalla littafin nan lfy

Farin saurayine sosai mai kwance da saje lublub kan fuskar sa,baqi lallausa Gwanin burgewa sai sheqi yake kallon qaramin bakinsa na tsaya yi sosai sbd yarda yake daukan hankali very cute and pinkish sama na daga na daura ido na kan hancinsa dake da tsayi Kamar zai Kare yana sanye ne da farin glasses a fuskarsa sakamakon ciwon idon da yake dashi glass din ya mai kyau sosai ba zaka taba cewa baya gani ba idan kuka kalla idanunsa sbd Allah ya mai wasu idanuwa masu dauke hankalin mai kallo gasu da kaifi kaff dai bazai wuce shekaru 26 ba a duniya
Driving yake yana murmushi shi kadai abunshi har ya isa qofar gidansu dake agric quarters mando kaduna horn ya danna mai gadi ya wagale mai gate gaskia gidansu ya tsaru iya tsaru dan idan na biye sai in cike page innan ban qare ba baki bude nake kallon gidan nace aljannar duniya da sauri sauri ya ya fito a motar bayan ya daidaita parking din bai qarasa shiga entrance din gidan ba naga wata er yarinya da bazata wuce shekaru 3 a duniya ba ta rugo da gudu tana yaya masoyi shima da dariya a fuskarshi ya cabeta yana qanwa matata dariya suka kwashe da ita bayan sun hada ido sai kuma ya bata rai yace shine ina school kikasa aka dameni da kira dariya tayi tace haba yaya masoyi yanzu ka daina so na ne?ta qarashe kamar zatayi kuka nikam na tsaya kallon ikon Allah ji yarinya mai shegen wayo da baki kamar wata babba haquri ya bata yana cewa am sorry wifey toh mujje ina daddynki qin bashi amsa tayi tace yaya drop me yan sauke ta tayi falo da gudu yarinyar kyakkyawa ce sosai black beauty ga gashi a kanta kamar me tana da manyan idanu sosai da dan qaramin baki mai dauke da launi biyu pink and black wanda yake qarama ta kyau
Tana shiga ta wuce gun mommarh inta da gudu tana 6ata rai dukkansu manyan mata a palon su biyu daka gansu kaga mata masuji da aji da kudi sai dai fah suna da san jama'a dukkaninsu kyawawa ne mom ta kalla Fadeela tace aaaa feedy ina masoyin naki?qara 6ata rai tayi zatayi mgn sai gashi ya shigo dauke da sallama a bakinshi yana qara fadada murmushinshi bayan ya hada ido da mom inshi   har gabanta yaje ya duqa ya gaisheta Kafin ya tashi ya rungumeta shafa kanshi tayi tana murmushi tace Aslam baka girma ne wai 6ata fuska yayi yace nifah har yanzu yarone since am the only son of the family so haquri zakuyi da duk abunda zanyi dariya tayi tace hakane my boy  ga mommah kunan baka gaidata ba koh nace sirikar ka dan sosa kai yayi kafin ya kalla hajiya laurat yace maman mu ina wuni sannu da zuwa yana dariya da murmushi a fuskar ta ta amsa mai
Mom ce ta ranqwashe shi a kai bayan ta kalla feedy tace boy me kama suruka ta ne?kallon feedy yayi shima ya 6ata rai yace kinsan matas da rigima nima bansan na mata laifi ba ni yakamata nayi fushi ai ba ita ba ina lecturer kuka dameni da kira ya qarashe mgnr tareda miqewa yana tafiya hanyar dakinshi yana shigewa feedy ta bishi da gudu
Numfashi hajiya laurat ta fesar kafin tace shidai Aslam yaji dadi ba ruwanshi da kowa murmushi yake baya fada da kohwa qwafa mom tayi tace aikam baki gama sanin Aslam ba yana da fushi sosai shiyasa ai yake zama faranfaran da kowa amma idan aka 6ata mai rai koh ni bana shiga bada haquri dan idanunshi rufewa sukeyi yayi ta rashin mutumci
Dariya kawai hajiya laurat tayi kafin suka cigaba da hiransu
Wnn knn familn alhaji mansur tafida knn mahaifin Aslam shi kadai Allah ya basu da matar amininsa watoh hajiya laurat ita ma daga baya Allah ya bata haihuwa yara biyu salman da feedy wanda yanzu Salman yake ss3 .da yake dama basuyi aure da wuri ba shiyasa hajiya laurat bata kai hajiya samha manyanta ba
Jin an bude mai qofar falo yasa ya juya yaga koh waye murmushi ya saki kafin yace meye kuma ki fita ni ba masoyinki bane yana yi yana mata dariya sbd ya qara qular da ita  fikifiki tayi da ido kafin tace yaya am sorry nifah banyi fushi dakai ba kaine ka rage sona ni kuma kullum ina cewa kaine masoyi na kai kuma baka cewa hannunta ya ruqo yace no my dear sis ba komai fah kwanan nan nayi busy sosai kin gane kin san ina final year ne yanzu ina shirin exams ne zanyi graduating u don't have to worry da na gama nayi nysc zan sama time inki ai nima ina sonki ya qarashe yana bata peck a goshi  murmushi tayi kafin tace ok yayana nima yanzu ina nursery one idan na gama zamu sama time knn koh ta qarashe da sigar tambaya dariya ya mata yaja chicks inta yace mata ehh yanzu kije gurin su mommah gani nan zuwa yanzu wanka zanyi okay jinjina kai tayi alamar gamsuwa ta tashi ta fita da gudu
Daki ya shige yayo wanka yayi sallar la'asar ya dawo palor ya samu su feedy zasu wuce gida ana rigima da ita akan sai ta kwana gurin yaya masoyi
Kan dinning ya tafi ya gama cin abinci kafin yazo ya samesu gaba daya ta maqalqale mai tana kuka bazata bi mommah gida ba hakanan hajiya laurat ta tafi ta barta akan za a  kawo mata kayan sawanta
Nan suka zauna Sunata hira abunsu feedy na shirmenta suna dariya  wayar Aslam ce ta hau ruri ya daga sai ji nayi yana cewa ok gani nan zuwa yanzu zan kawo miki
Tashi yayi mom ta tsaya tana kallonshi kafin tace ina kuma zakaje gyara zaman glass inshi yayi kafin yace mmmm wata classmate ina zan kaiwa saqo albarka mom ta saka mai tareda fada mai ya kiyaye ya kuma ji tsoron Allah a duk inda yake da ameen ya amsa har zai fita feedy ta ruqo hannunshi tace yaya zan bika kanta ya dafa yace no TAYAYA I'll be back right now ba dadewa zanyi ba kinji?gyada mai kai tayi kafin ta sakeshi tana mai bye bye
Tunda ya sanya qafarsa a waje yaji gabanshi yayi mummunar faduwa wanda yasa mood inshi ya canza sai ya fara contemplating koh ya fasa fita ne?but kuma sai ya sakai ya wuce tafiya yake a mota zuciyarshi namai waswasi akan yaje koh karya je gaba daya zuciyarshi bata mai dadi kan fitan da yayi
Gurin masu kayan Miya yaje yayo siyayyar sa ya dawo still zuciyarshi ba dadi dan har ya nuna a fuskarsa
Bai tsaya koh ina ba sai a Malali gambiya road inda yayi parking a qofar gidan ya fito yayi knocking mai gadi ya bude  suka gaisa ya shiga a lokacin an fara kiran sallar magriba sai nace bara na tsaya nayi alwala kafin na shiga ciki sai bayan anyi sallah na shiga a daidai sanda naji ihun wata a cikin gidan sai ban shiga ba sbd tsoro ina jiran aslam ya fito shiru shiru har gap da Isha'I kafin naga ya fito yana fitar da numfashi da qyar gaba daya dai baya cikin hayyacinsa rigar jikin sa duk ta yamuste tayi squeezing mai gadi na mai mgn amma shiru bai bashi amsa ba dan hawaye ma yakeyi yana hahhada hanya kamar bai gani da kyau a daddafe ya shiga mota yayi gaba kadan da unguwar kafin ya tsaya tareda sakin wani marayan kuka anan yaci kukanshi ya qoshi nidai ina biye dashi har lokacin ina mamakin maiya sameshi da yasaka shi kuka haka  ambaton Allah ya fara a hankali kafin bayan wasu lokuta ya sama nutsuwa ya tayarda motarshi muka nufi hanyar gida sai alokacin ya tuna baiyi magrib ba balle Isha'I a masallacin unguwar su ya tsaya yayi sallah kafin  ya koma cikin mota ya qarasa gida
Ba yabo ba fallasa ya shiga cikin falon a lokacin ABBA ya dawo koh sallama baiyi ba ya fada kai tsaye bai ma ankara da kowa a falon ba sai da yakai qofar dakinshi yaji ABBA ya kirasa Aslam!juyowa yayi a hankali jiki a sanyaye ya nufi gurin ABBA ya duqa ya gaidasu yama kasa daga kai ya kalleshi hakan yasa suka ganeh yana cikin damuwa da 6acin rai da kallo mom ta bishi kafin tace boy tashi ka ci abinci bai koh kalleta ba ya juya yayi tafiyarsa hakan ya qara tabbatar mata da cewa son na cikin damuwa
Yana shiga palor shi ya fara watsi da abubuwa sai ji kake tasss damm tarararassss
Fitowarta knn tareda larai daga daki  take tambayar su ABBA koh yaya masoyi ya dawo basu kaiga bata amsa ba sukaji qaran fashe fashe a tare suka zabura suka  nufi hanyar dakin aslam hankali tashe tsuru suka tsaya a falonshi ganin ya sauke tv ya fasa ya hargitsa falon gaba daya hankali tashe mom ta qarasa dakin tana qwala mai kira koh da suka shiga dakin ya fasa dressing mirror inshi ya hargitsa koh hannunshi ma ya fashe yana jini
Feedy ce taje gurinshi da gudu tana fadin yaya plz stop it u are hurt tana kuka da muryar yara tana riqe mai hannu hankali tashe bangaje ta yayi yana fadi get out of my sight cikin tsawa da sauri mom ta ruqota kafin takai qasa
Cikin tsawa shima ABBA yace kana da hankali kuwa?koh me aka maka meye na wnn?sai kace ka haukace I won't take this beta get to ur senses bana san hauka juyowa yayi yana kalla inda dad yake idan ka kalleshi zaka dauka dar yana gani amma idan ka tunkaro shi sai dai yaji motsi da dishi dishi yake hangen mutum wani marayan kuka ya saki yana fadin ABBA why?why?meyasa haka zata faru dani wllh NA TSANI MATA daga ABBA har mom freezing sukayi kafin ya fashe musu da kuka

Am sorry fans I kept u waiting for long insha Allah zan dunga qoqarin yin update idan na sama time kunsan abun sai a hankali dole sai ka bada nutsuwa ka tattare komai a gefe ga karatu so plz bear with me

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Mar 17 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

NA TSANI MATA😠Where stories live. Discover now