59&60

220 10 0
                                    

AHALINA

(Siblings of different fathers )

Book two 'in Aure uku series

      By

CHUCHUJAY

EPISODE 5⃣9⃣◽6⃣0⃣

   Bayan jaddada bincike mai yawa iyayen 'na bagare huɗu suka zauna suka tattauna

Aka tsayar da magana ta Aure tsakanin Ahmed da Nadiya,Abdallah da Hafsa,

Tsaye Nameer yake bakin mirror ɗin dakinsa yana mai sake duba kansa ,

A hankali Jamaimah ta shigo ɗakin hannunta boye a bayanta,

Jingina tayi da bakin kofa tace"honey wannan kyau ɗin da kayi gaskiya ban yarda ba cos ko ranar Aure na dakai ƙananun kayane jikin ka,im hating the method amma bana dana sanin Result ɗin,"

Murmushi yayi 'ya ɗauko hular tangaran ɗin dake kan mudubi 'ya tako gareta,hannu 'ya miƙa mata ,Babu musu ta kama ,juyata yayi ,dariya tasa kana yace "Kar ki damu abar kaunata kar ki damu kullum zanna miki shiga irin wadda kikeso , yanzu dai ki ƙarasa shiryani naje Na karba ma ƙannaki Aure domin idan na cigaba da tsayuwa a cikin gidannan cikin ɗakin nan tare dake To komai nawa zai iya tsayawa na cire wannan farar shaddar nayi making love gareki ta ko wanne fanni,kashe idansa guda ɗaya yayi yace"kinsan dai yarda nake a gado dan ni ɗin baban Dan kwallo ne Dan a yanzu haka na tabbata Na jefa kwallo a raga. "

    Taune lips ɗinta Na ƙasa tayi kan ta karbi hular hannunsa ta ɗora akansa kana ta fesa masa turaren da ta shigo dashi kafun ta kama sajensa tace"ni kuma kasan bana wasa wajen chabe kwallo ,domin a yanzu haka yazo ina da yaƙinin ƙwallanka tayi saiti".

Rufe bakinsa yayi cike da murna yace"you're pregnant?dont tell me this "

Faɗaɗa farin cikinta tayi tace"im telling you This habiby im one month pregnant "

Cike da mirna ya ɗagata sama yana mai fadin"ALHAMDULILLAH 'ya rabbi,kissing fuskarta 'ya fara ta ko ina 'yana mai saka mata albarka,"

Dan janye jikinta tayi tana mai sake gyara masa jikinsa tana cewa"ni dai yanzu kazo ka tafi ɗaurin Auren nan murnar kuma ka bari sai ka dawo kayi iya yinka ,da kyar 'ya hakura ya fita dan da ace ba ɗaurin Auren Abdallah da Nadiya akeyi ba da Babu abunda zai saka 'ya fita yabarta,"

Ɗaurin Auren Nadiya Bilal da Adam Hans aka fara da karfe takwas Na safe kana aka ɗaura 'na Abdallah Hafiz da amaryarsa Hafsat Balarabe wanda aka ɗaura gidan mahaifinta,

Tun a yanayin mutanen da suka zo amsar Auren Hafsa Mama laure ta sare,kai ba ma ita ba, Babu wanda a garin baiyyin yamaɗiɗi da maganar ba mussamman da yakasance Mahaifin Hafsa 'ya nemi da Hafsa ta cigaba da zamanta gidan Innarta shi da kansa zaizo ayi duk wani Abu da za'ayi dan da fari ma a Adamawa yaso a ɗaura Auren Amma Daddy Bulamaa yace kar ya damu Zuwa Adamawa bazai taba zuma musu abu mai wahala ba after All hakkinta ne aje har gidan mahaifinta a amsa Auren ta,

Bayan ɗaurin Aure wanda ya tara jama'ar yankin garin da sukazo shaida wannan ɗaurin Aure ,Malam Balarabe mahaifin Hafsa 'ya shiga gida gurin yan uwansa da suka hallarci bikin da ba amarya domin sake gaisawa dasu,wata Innar Mama laure ce da tazo daga cikin garin katsina ta saka akayi mata magana dashi,

Cike da girmamawa yazo ya duka yace "inna usai gani,"

Ciike da kunmfar baki tace "ai Balarabe ba sai kayi mun mur mur da ido na munafukai ba naji komai,idan ba lalacewa ba ta yaya za'ace Hafsatu na Aure babu ita garin da ubanta yake,bana tunanin ko binciken kirki kayi akan ɗan nan saboda ƙwalama da ka saka a gaba tunda ance Malamine ɗiya masu kuɗi,To bari kaji ko gwamna Hafsatu Ta Aura  Laure ce domin kuwa da bata raineta ba lokacin da uwarta ta mutu ta barta da ba'a Kai nan ba dan kilan ma da tabi uwarta,To ina san kasan Abu ɗaya da bazar Laure Hafsatu ke taka rawa. "

    Da mamaki Malam balarabe 'ya kalli Inna kana yace "amma hala inna kin manta da dukkan ukubar da Laure tayiwa hafsa hala,duk wani cin kashi da azabtar da ita da tayi duk baki gani ba kin manta,To bari kiji na faɗa miki wani abu,duk abunda hafsa ta zama a rayuwa ƙaddarar tace ba tsarin Laure ba domin kuwa da ace Ta Laure ce da yarda taso da tuni Hafsa ta zama ƙaramar bazawara domin kowa yasan wanda tayi niyar Aurawa matsiyacine wanda baisan darajar mutum ba,zaman Ta a chan Adamawa kuwa Nine na saka domin Babu wanda yake da iko mun da ɗiya,idan kuma kuna san ganinta ne sai ku bari idan sunzo bankwana ita da mijinta sai kuyi domin da Allah ya tashi ɗagata bayan wata biyu a Nigeria zasu wuce ƙasa mai tsarki danyin rayuwarsu,idan kuma da mai saƙon da zai faɗa mata cikinku to 'ya bayar danni uban ɗiya zani Adamawa.

Tashi yayi dan barin gurin muryar Laure ta katse sa ta hanyar faɗin"kazata bamu san ubansa Dan fashi Bane,uwarsa kuma mai biye biye ce Dan da ta fara irga Aure sai da tayi goma,idan da ƙwadayi ai da wahala."

Murmushi Yayi yace"nine da godiya Laure sannan waɗannan da kike lissafi haka akansu su 'na zaba 'na bawa ɗiyata kiyi abunda zakiyi ita yarki da kike san Aurawa Dan mai gari gashi ai 'ya mata ciki 'ya gudu ya barta "

Bai jira cewarta ba ya bar gurin Dan Tafiya Adamawa,banbami da sumbatu Mama Laure ta ɗingayi tana zagin malam Balarabe wanda ko ta kanta baibi b inda 'yan uwanta suka dinga tayata suna tsinewa Balarabe da yarsa .

       Jirgi Papa yayi ma Mahaifin Hafsa zuwa Adamawa wanda babu wani bata lokaci ya sauka a Adamawa wanda driver yana nan yana jiransa,inda 'ya nemi su kaisa nan suka ajesa wato gida Inna,koda aka ajesa Yayi mamakin ganin yan uwa na kusa da nesaa da suka masa kara ,tabbas ya yarda Laure ce Babbar mutum wadda ta ja katangar karfe tsakaanisa da yan uwansa ,chan ya haɗu da amaryar ɗiyarsa wadda dukkan wani nauyin gyarata Aunty shatuh ta dauka 'dan sai ana gobe daurin Auren ma ta koma gidan Innarta,karamci iya karamci Aunty shatuh ta nuna masu domin komai na hafsa ita ta daukesa ,

Dukkan wani kuɗi da ta samu tsakanin Innarta da mahaifinta ta raba su wanda da kyar suka karba, musamman ma inna da aka dauke mata karatun Muhammadu har ya gama,

Da rana dangin Abdallah sukazo 'dan tafiya da ita family house ɗinsu wanda nan zata fara zama kafun su wuce ita da mijinta,nasiha sosai mahaifinta yayi mata mai ratsa jiki,kuka sosai take yi haka zalika shima mahaifin nata wanda ya kasa riƙe hawayen da ke neman kwace masa,tabbas Aure yana kai mace ko ina amma baiyyi tunanin zai ɗauke hafsa da ƙasarta ta haihuwa ba.

                                ***

Ya maganar gidansu Amaryaa Nadiya kumafa?

Tun a wajen gidan Dr Imam da Dr Umaimah zaka san ana bikin kuɗi a gida ,shige da fice shine abu n'a farko da zai faɗa maka Hakan ,yan uwa na kusa da nesa duk sunzo ciki kuwa harda su Fawza,Fawzan,Fawha wadanda suka baro karatunsu domin zuwa taya yan uwansu murna domin abun murna ne a yi masu yasan mutum biyu a gida ,

Bikine akayi gangariya n'a gani na faɗa wanda ya yaɗa kasa da ketarenta baki ɗaya,mahaifin Nadiya yazo amma cikin bakin daurin Aure wanda babu wanda ya nuna masa wani abu face karamci wanda babu daɗewa ya bar gurin domin zaren ba kalar yadin Bane domin kuwa yasani ya rasa Nadiya da mahmud har abada,

Gagarumun liyafar da aka haɗa wa amaren da angwayen an haɗa tane cikin gidan Dr Imam wanda aka haɗe da baby shower Na Jamaimah wadda bata samu wani liyafa ba na Aure 'dan haka itama aka tsantsarata cikin shiya irin ta amaren hakazalika Nameer wanda shima ya haɗe cikin shiga irinta Angwayen ,bada labari na yarda wannan taron Ya haɗu bata lokacin domin kuwa iya haduwa Ya hadu,abune akefa na sanannu a ƙasa ,media babu abunda take sai ihunsu dan kuwa abu ya ƙayattar musamman ta hanyar da baƙi suke samun ƙyaut ta ban mamaki wadda basu tsammanin samu 'dan kuwa kowa a AHALIN Ya saki bakin Aljihu .

   Bayan taro Ya watse Nadiya suka fara tafiya da mijinta da Aunty shatuh da Affan ƙanin Dr Imam domin kaita gidan mijinta dake cikin garin Kaduna wanda ita dashi suka zabi gari for a Good change,cikin unguwar marafa,a yayinda Aka kai Hafsa sashe mijinta dake cikin Gidan iyayensa wanda aka gyara sosai duk da kuwa ba zama ne na daɗewa ba

Haka zalika ango da amaryarsa mai cikin wata ɗaya suka nufi gidansu domin sake rubuta soyayyarsu dake shirin zama tsakanin mutum uku.

Bari na kama hannayenku domin kaima sabbabin Auren nan ziyara.

Mu haɗu a page na gaba 'dan jin Ya zata kaya sannan ina farin cikin sanar daku sauranmu bai wuce kaɗan ba.

Kusha ruwa Lafiya.

Nice taku a kullum.

CHUCHUJAY ✍️

ummumahnoor...

AHALINA(book 2 in Aure uku series)✔Where stories live. Discover now