*ƳA KO JIKA?*
*SAFNAH ALIYU JAWABI (HIS NOOR)*🥰
*PERFECT WRITERS ASSOCIATION*
Follow the PERFECT WRITERS ASSOCIATION channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vad1bE05a249vbEcab0r
'''Ga link nan na kungiyar mu mai suna Perfect writers ku shiga domin samun sabbi da kuma tsofaffin littatafan mu.
Ku kasance a tare damu lallai ba za kuyi da kun sani ba.'''
*Mabuɗi*
Masu kaifin ƙwaƙwalwa da hangen nesa sukan gane hikimar da ke cikin ilmin gaibu, musamman yadda Allah buwayi gagara koyo ya ɓoye wa 'ya'yan Adamu makomarsu ta lahira. Domin dai, da a ce kowa ya san ƙaddararsa, to da tilas abubuwa biyu za su faru: Na farko waɗanda suka gane makomarsu mummuna ce, za su shiga tashin hankalin da za su hana duniya sakat, su kawar da nutsuwar da ke cikinta. Na biyu, a yadda imaninmu ke hawa da sauka tamkar farashin man fetur a Nijeriya, abu ne mai sauƙi waɗanda suka san suna da kyakkyawar makoma su shagala, su daina ibada, su daina duk wasu nagartattun halaye.
Hakan ce ta faru a gidan Alhaji Mamman Bukar, ta yadda a wurinsa da wajen mutanen unguwa tagwayen 'ya'yansa wato Amir da Amira su ne 'ya'ya mafi nagarta, 'ya'yan da kowane iyaye ke burin samun irinsu. Sai dai, a iya cewa su ɗin irin mutanen nan ne da ake cewa Musa a baki, Fir'auna a zuciya, ko kuwa a ce macijin masussuka, sari-ka-noƙe. Domin ƙwararru ne wurin safarar miyagun ƙwayoyi; amma da yake suna amfani da wani salo na ɓad-da-bami, ko kuwa a ce shashatau, sai ya kasance ba a yi walƙiyar da ta haska su a ainahin kalarsu ba.
Alhaji Mamman Bukar ɗaya ne daga cikin manya a Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, (NDLEA). Matarsa kuwa Hajiya Jummai likita ce. Yayin da babban ɗansa Amir ya kasance malami a jami'a. Ita kuwa 'yar’uwarsa tun da ta kammala makarantar koyon kiwon lafiya, sai ta buɗe kemis inda take bayar da magunguna. Ba iya wannan gudunmawar kaɗai wannan ahali suke ba wa al'umma ba, domin sai da suka haɗa ƙarfi da ƙarfe suka samar da gidauniyar tallafa wa al'umma musamman marasa lafiya da masu ƙaramin ƙarfi.
****
Misalin ƙarfe bakwai da minti arba'in da biyar na safiyar ranar wata asabar, Alhaji Mamman Bukar da matarsa Hajiya Jummai suna zaune a falo suna hutawa, Amir da Amira suka fito, shi yana dariya yana zolayarta, ita kuwa ta haɗe fuska da alama shagwaɓa take ji da ita. Gaishe da iyayen nasu suka yi cike da girmamawa kamar yadda suka saba, sannan Amira ta ce:
"Dadi ka ga wai Yaya ba zai kai ni kemis ba."Tana dasa aya Amir ya karɓe zancen da cewa, "Dadi kada ka saurare ta, rigimarta ce ta fi ƙarfinta, na faɗa mata sauri nake zan je ɗaurin auren abokina."
Amira ta turo baki za ta ci gaba da shagwaɓa, Abba ya tari numfashinta da cewa:
"Rabu da shi shalelena, daɗin abin kin wuce gorin mota tun da mahaifinki yana da ita."
Murmushi na jin daɗi ya suɓuce mata, shi kuwa da ya lura da haka sai ya ɗauko mukullin motarsa ya miƙa mata.
"Karɓi mukullin motata, ki je."
Durƙusawa ta yi har ƙasa ta karɓa sannan ta yi murmushi ta ce, "Na gode Dadi, Allah Ya ƙara buɗi."
"Ameen," ya faɗa yana murmushi. Shi kam yana matuƙar ƙaunar ɗiyarsa, komai nata burge shi yake yi.
Hajiya Jummai ta taɓe baki ta ce, "Ba za a burge mu ba sai an bar mata motar."
Amira ta buɗe baki za ta yi magana, Abba ya katse ta: "Rabu da su shalelena, idan aka fara yi wa mutum adawa tun daga gida, alamu ne na ya yi nasara." Ya faɗa cike da zolaya.
"Daga baya ke nan, wai an yi sadaka da bazawara." Cewar Umma sannan ta cigaba:
"Ni nawa ɗan ai tasa motar ce da shi, ya wuce aro."
"Faɗa masu dai Ummana," cewar Amir yana yi wa Amira gwalo.
"Malam ba cewa ka yi ka makara ba ? Maza ka ɓace mini a nan kada ka ɓata wa shalelena rai na ƙwace motar na ba ta." In ji Alhaji.
Umma ta ce "Saboda mulkin mallaka ake yi?"
Suka yi dariya gaba-ɗaya, sannan iyayen nasu suka masu fatan alkhairi, suka fita tare.
Lokuta da dama idan suna so su karɓi motar mahaifin nasu haka suke yi masa. Shi kuwa idan yana da rauni, to bai wuce a kan Amira ba, ko kaɗan ba ya son ɓacin ranta. Sai dai da a ce ya san suna karɓar motarsa ne don gudanar da baƙar kasuwarsu cikin nasara, da ya gwammace ɓacin ran ɗiyar tasa, fiye da ba ta motar. Domin suna amfani da motar ne wurin shigo da hodar iblis, musamman saboda sanin halin akasarin jami'an tsaronmu da suke da sakaci, ta yadda idan sun ga motar babban ma'aikaci ba za su bincike ta ba, sai su bari a wuce salin-alin, wai karatun yankan jaki.
Yanzu ma da suka karɓi motar gaɓar teku suka nufa kasancewar ba su da nisa, inda za su ɗauko wata hodar iblis da aka yo masu oda, wadda darajarta ta kai Naira miliyan talatin da biyar. Tun farko Amir ne ya fara shiga cikin wannan kasuwancin, da yake ba ya aiwatar da komai sai da haɗin kan 'yar'uwarsa, sai ya yi mata tayi. Ita kuwa kasancewarta irin matan nan da take da son kuɗi fiye da ƙima, ba tare da ta yi tunanin abin da zai je ya dawo ba, sai ta amince. Musamman da yake a farko sun fara ne da safarar ƙwayoyi da sauran magungunan mura waɗanda ake amfani da su suna kawar da hankali da tunani, ba ta da wata faɗuwar gaba idan an kama ta da waɗannan magunguna saboda an san tana sayar da magani, shi ya sa ko a motarsa tana ɗauko kaya irinsu.
*****
Bayan sun fita sai Amir ya ajiye motarsa a gidan abokinsa suka hau motar mahaifin nasu suka nufi kasuwancinsu. Suna tafiya Amir yana ta jan Amira da hira, sai ya lura kamar jikinta a sanyaye yake, don haka ya ce da ita:
"Ƴar'uwa, lafiya kuwa? Me yake damun ki ne ?"
"Yaya kawai ina ganin ya kamata mu dakatar da wannan ƙazamin cinikin da muke yi."
Tamkar wanda wutar lantarki ta ja haka ya dube ta a razane sannan ya ce, "Me ya sa kike wannan tunanin?"
"Dalilai ne da yawa! Na farko, ka ga dai duk kuɗin da muke buƙata mun samu, muna da isassun kuɗin da za su isa mu kafa halastaccen jari wanda ba ma buƙatar kasuwanci a ɓoye. Na biyu, matsawar muka ci gaba, tilas wata rana asirinmu zai tonu, domin dai komai girman gona tabbas tana da kuyyar ƙarshe. Ka tuna irin kallon da al'umma suke yi wa ahalinmu, ka tuna halin baƙin cikin da iyayenmu za su shiga idan suka samu labarin an kama mu a wannan baƙar hanyar."
Murmushi ya yi sannan ya fara magana cike da ƙarfin gwiwa, "Kwantar da hankalinki 'yar'uwa, babu yadda za a yi asirinmu ya tonu matsawar mun cigaba da samun motar Abba, domin ita kaɗai wata babbar garkuwa ce a gare mu. Ba ki lura da yadda jami'an tsaro suke buɗe mana hanya silar motar ba?"
Ya mayar da hankalinsa a kan titi sannan ya sake dubanta, ya ce: "Allah na tuba ma ai bai dace ki ji tsoro ba. Domin dai ni nake ɗaukar nauyin rarraba kayan idan sun shigo, waɗanda kike raba wa magunguna ne, wannan kuma babu wanda zai zarge ki. Ina da tabbacin ba za a kama mu ba ko da shekara nawa za mu yi muna kasuwancinmu."
"Yaya." Ta kira sunansa cikin sanyin murya sannan ta ci gaba. "Idan mun tsere wa kamu a duniya, ka san dai babu hanyar da za mu tsere kamu a lahira. Mu bar ma ta batun hodar iblis ita wannan a iya cewa masu hali ne suke saye, mu kalli yadda son zuciyarmu mu da ire-iren mu ya sa muka bayar da babbar gudunmawa wurin ƙara karya tattalin arziƙin ƙasa, ta yadda muka jawo magunguna suka yi tashin gwauron zabi, har ta kai ta kawo suna fin ƙarfin talaka. Yara da dama sun rasa rayukansu silar cutar mura, saboda iyayensu ba su da kuɗin da za su sayi maganin tari."
A daidai nan ƙwaƙwalwarsa ta yi gaggawar tuno masa wani yanki na huɗubar da aka yi a masallacin juma'a inda limamin ya fayyace nauyin zunubin da mutum ke dako yayin da ya yi silar mutuwar wani. Ya tuna yadda aka kamanta kashe ran mumini ɗaya daidai yake da kashe duniya gaba-ɗaya. Tabbas zuciyarsa ta fara karaya, sai dai kuma a daidai nan ne shaiɗan ya ɗaura ɗamara ya fara yaƙi da zuciyarsa. 'Komai girman laifin da kuka yi Allah Yana yafewa matsawar kuka tuba. Ka tuna aikin da kake yi, da yadda albashinka yake, sannan ka kwatanta shi da manyan kuɗaɗen da kuke samu a wannan kasuwancin; babu shakka ko ba a gwada ba, ai linzami ya fi ƙarfin bakin kaza. Haka nan, kana da burin sauya mota, ka gina gida, ka yi aure; ta ya albashinka zai isa ka yi duk waɗannan abubuwan? Duk ma ba wannan ba, ka ƙaddara....'
Zaren tunanin da yake saƙawa ya tsinke sakamakon jiyo muryar ƙanwarsa ta ɗora faɗin:
"Ban da waɗanda muka yi silar fitar da su daga hankalinsu, suka yi aikin da-na-sani."
Ta tsahirta tana dubansa ta ga kamar jikinsa ya yi sanyi sannan ta ɗora: "Yaya, ya kamata mu dakatar da wannan abin haka."
"Shi ke nan ƙanwata. Duk yadda kika ce haka za a yi." cewar Amir.
Murmushi na jin daɗi ta yi, shi kuma ya ce: "Daga mun ɗauko wannan mun rabar da ita, shi ke nan ba za mu ƙara ba."
Ya faɗa a zahiri, duk da dai shi kansa ya san ba zuciyarsa ce ta furta hakan ba, hasali ma ba ta tare da wannan furuci nasa.
******
*SAFNAH ALIYU JAWABI*(*HIS NOOR*)🥰🥰🥰