MENENE ILLA TA ?
9
"Ni dai kai kaɗai nake so na Aura ya Idrissa, idan har bakai ba to ni bana son kowa..." Aminatou tai maganar tana turo baki gaba cikin sangarta.
Kafeta yay da idanu cikin tsoro gamida tashin hankali, yana son ya tabbatar da abinda take faɗa ɗin, tsoro ne ya kamashi a lokacin da ya tabbatar da cewa maganar Aminatou kai tsaye daga ƙasan zuciyarta take fitowa...
Cikin ɗaurewar kai da rashin sanin abinda zece yay saurin rufe bakinsa daya buɗe yana aikin kallonta, daƙyar ya iya tattaro kalaman bakinsa cikin hikima ya dubeta cikin ido yace,"Aminatou kamar yanda na gaya miki a baya zan sake maimaita miki, wllh Aminatou ba ƙinki nakeyi ba soyayyar Aurataiya ce kawai banai miki, inada Buri mai girma akanki kamar yanda nake dashi akan Bintou, sedai burin da nake dashi akanki sam ba irin na Bintou bane."
Lumshe idanunta tayi tana jin wani irin abu me matiƙar ɗaci da raɗaɗi yana taso mata daga ƙahon zuciyarta zuwa maƙoshinta, wanda ƙarancin shekaru ya hanata fahimtar ainihin ma'anarsa, cikin sanyin jiki ta janye idanunta daga kansa bayan ta zame hannunta daga ruƙon da yay mata tace, "Ya Idrissa wani buri kake dashi akaina da kuma Bintou, wadda nakeji a raina tafini komai?" tai maganar cikin matiƙar Sarewa da rashin ƙwarin gwiwa.
Tsananin tausayinta ne ya dabaibayeshi, wanda tunda yake da ita bai taɓa jin hakan a tareda ita ba, wllh da ace yanada ikon canza son da yakewa Bintou a zuciyarsa ya maye gurbinta da Aminatou tabbas da yayi hakan, Amma babu yanda ya iya da abinda Ƙaddara tazo musu dashi, wani dogon fasali yaja cikin son ya kawar da tunaninta akan abinda tai masa tambaya akai yace,"Aminatou Bintou bata fiki da komai ba karki sake ɗora tunaninki akan tafiki kinji ko?"
"wllh ya Idrissa ya Bintou ta fini komai tunda har gashi ka fifita soyayyarta akan tawa, dama na taɓa ji Baba sahura ta ce duk abinda mutum keso yakan iya ɗaukar ko wace kasada don ganin ya mallakin abinda zuciyarsa ke Muradi, taya bazance Bintou ta fini komai ba tunda ita kake so bani ba...?"
"Aminatou keda Bintou kuna da banbanci sosai, idan na Aureki a yanda kike ɗinnan bazan taɓa samun nutsuwar zuciya ba, sabida bazaki iya ɗaukar Lalurata ba Amma ita Bintou zata iyayin hakan tunda shekarunta sunkai."
"baka tunanin nima nan gaba kaɗan idan na ƙara girma zan iya ɗaukar lalurar taka ya Idrissa? Baba Sahura ta koya min duk wasu dabaru da zanyi jinyar mara lafiya, kaga ai zan iya kula da kai idan lalurar taka ta tashi." tai maganar tana tsareshi da fararen kyawawan idanunta.
Tsoro da fargaba ne suka ƙara kamashi, a ransa yana mamakin shegen wayo da kaifin basira irin nata, tabbas nan gaba kaɗan Allah ne kaɗai yasan yanda Aminatou zata zama, don kaifin tunaninta da wayonta ya zarta shekarunta.
Murmushi ya ƙaƙalo bayan ya ƙara janyeta daga jikinsa yace," Aminatou kai tsaye bazance bazan Aureki ba tunda bansan abinda ƙaddarata da taki suke ɗauke dashi ba, nidai fatana a gareki shine ki maida hankali sosai akan karatunki, ta yanda zaki fi kowa na gidan nan ƙoƙari ciki kuwa harda ni."
Lumshe idanunta tayi tace,"Ya idrissa me yasa kake so nayi karatu sosai?"
Jan hancinta yayi kamin ya saki wani kyakkyawan murmushi yace, "Sabida inada kyakkyawan sanya Rai akanki Aminatou, sannan kuma ina matiƙar son naga kinyi karatu mai zurfi hakan zesa na ƙara ƙaunarki, amma nasan ba lallai kiyi hakan ba tunda kinsawa zuciyarki son Auren Idriss Muhammad Kankia"
Da sauri ta kamo hannunsa tana murmushi cike da wauta tace," Wllh ya idrissa zan dage sosai nayi karatu yanda kake so muddin zaka ƙara ƙaunata kaman yanda kace, sannan kuma daga yau bazan ƙara yin kuka akan Auren mu ba zan dage na zurfafa karatuna." tai maganar tana ƙara damƙe hannunta cikin nashi
YOU ARE READING
MENENE ILLA TA?
Non-Fiction"Idan kina ganin hakan shine dai-dai a zuciyarki to kiyi hakan BINTOU. ni kuma nayi alƙawarin cewa bazan taɓa dakatar dake ba, sai dai kafin ki zartar da hukuncin da kike ƙokarin zartarwa ina so kiyi tunani Akan ƴaƴan dake tsakanina dake...." cewar...