MENENE ILLA TA ?
10
Tunda Aminatu ta taso bata ta'ba kukan da ya shiga ransa ya sosa mishi zuciya irin wannan ba, kuka take sosai tana shesshe'ka lokaci guda kuma tana ro'konsa da Allah ya amince da aurenta, hajiya yaya kanta saida ta tausayawa Aminatu wanda ya sanya ta fito ta janye Aminatun daga jikin idrissa domin 'kan'kameshi tayi shi kuwa yayi mutuwar tsaye.
'Daki hajiya yaya ta kaita suka zauna a gado jikin Aminatu sai 'bari yake ga d'ankwalinta a hannu lallausan gashin kanta da baba sahura ta tufke domin sam ta'ki zama a mata kitso ya bayyana, d'ago rinannun idanuwanta tayi tace "hajiya yaya menene nake yi wanda yasa ya idrissa ya tsaneni? Hajiya yaya naji ance idan namiji ya'ki auren mace tanada wani mummunan hali ne nima kenan inada shi?"
Kwanciya tayi a 'kirjin hajiya yaya ta cigaba da rera kukanta ba tareda ta jira amsa ba, saida hajiya yaya ta bari ta sauko tukun cikin lallashi tace "Aminatu bakida wani mummuna hali kinji? Kuma yayanki ba tsanarki yayi ba inada tabbacin yafi sonki a kan su sulemanu wannan dalilin yasa ya nuna baya so ya aureki, yana miki soyayya ne a matsayin 'yar uwarsa da yake son kulawa da ita ba matar da zai aura ba, ki dena ro'konsa ya aureki mace bata ro'kon namiji ya aureta kinji?"
"Inaso ya aureni ne hajiya yaya banaso ya auri kowa sai ni dan Allah kice ya aureni kinji hajiya ai zaki iya ko?" Hajiya yaya bata d'auki maganganin Aminatu da muhimmanci ba domin a lissafinta yarinta ce kawai take d'awainiya da ita babu abinda ta sani kuma kwana kad'an zata shiga harkokinta ta manta, hakan yasa ta amsa mata cikin murmushi tace "to shikenan zan fad'a mishi amma kema sai kin fara hali irin na manya kinji? Ki dinga rufe jikinki yanda ya kamata sannan ki dena kuka na rashin dalili ki nutsu sosai kinji?"
"To Hajiya". Ta jima tana kuka a jikin hajiya yaya har saida bacci ya d'auketa da dabara hajiya yaya ta yakice ta ta kwantar da ita tareda zuba mata idanu, tsananin tausayin yarinyar take ji domin bata san komai a kan rayuwa ba, tunaninta baiyi cikar da za'a ce ta fahimci abinda ke wakana ba, soyayyar da ke tsakaninsu ta 'yan uwantaka ta saka take ganin auren ma kamar haka yake, tana da tabbacin kwana kad'an zata warware da zarar idrissa ya dena d'aure mata fuska.
Tana wannan tunani baba sahura ta shigo d'akin tareda sallama ta samu wuri ta zauna a hankali kar ta tashi Aminatu, duk darun Aminatu ta sani wannan dalilin yasa ta shigo suyi magana da hajiya yaya.
" sarkin daru tayi bacci kenan". Baba sahurs ta furta tana goge gumin da ya karyo fuskar Aminatu, amsa mata hajiya yaya tayi tace "um ta gama Allah yasa kar ta tashi da abun a ranta".
Lura baba sahura tayi da damuwar dake fuskar Hajiya yaya ta gyara murya tace "Hajiya yaya naji duk maganar da ta fito daga bakin Aminatu amma kar ki damu kanki saboda hakan, kalaman Aminatu babu komai ciki sai yarinta".
Girgiza kai hajiya yaya tayi tace "ba zallar yarinta bace sahura, kalamai ne da suke fitowa daga zuciyarta dukda nasan a yanzu bata san menene so ba, amma wannan abun zai iya zamowa tabo a zuciyarta har lokacin da zata girma. Wallahi ba da wata manufa na'ki amincewa da auren idrissa da Aminatu ba, sai dan duban da nayi da yanayinta, sahura wannan abar za'a aurar kuma a aurawa idrissa? Ai yanayin jikinsu ma ba d'aya bane. tayi 'kan'kanta ace za'a baiwa mutum mai shekaru irin na Idirisa, bugu da ƙari ga yarinta ga kuma karatun da ta fara. idan aka aurar da ita yanzu komai nata zai lalace ne, sannan na san halin idrissa tunda ya kafe kan Bintu aurensa da Aminatu zai iya kawo watsewar da kowa zaiji kunya domin 'yarki ce, duk abinda ya sameta bazan iya d'aga idanu na kalleki ba".
Murmushi sahura tayi tace "ni kaina nayi mamakin wannan had'i na mai babban allo saboda a yanayin jikin Aminatu nan da wasu shekaru goma gaba ma idan batayi aure ba babu wanda zaice ta kai shekarunta, yanayi ne irin na mahaifiyarta Allah ya ji'kan rai. Sannan idrissa nima d'ana ne bazan so a masa dole a aure ba domin naga illar auren dole a kan 'kanina hamisu, tunda matar ta yanke ta fita har yau babu d'uriyarta saboda an aura mata shi a dole. Muyi addu'a kawai sannan ki taushi mai babban allo Allah ya za'ba abinda yafi alkhairi ".
YOU ARE READING
MENENE ILLA TA?
Non-Fiction"Idan kina ganin hakan shine dai-dai a zuciyarki to kiyi hakan BINTOU. ni kuma nayi alƙawarin cewa bazan taɓa dakatar dake ba, sai dai kafin ki zartar da hukuncin da kike ƙokarin zartarwa ina so kiyi tunani Akan ƴaƴan dake tsakanina dake...." cewar...