AMRAH........
A nitse Ta shiga Cikin Conference Hall na company din "AA INNOVATIONS" da kyawawan Idonta cike da fargaba da kokonta ta ke Scanning dakin , kafun Ta samu Seat Ta zauna.
Daga Ido tayi ta kalli Ammar CEO kuma Founder na "AA INNOVATIONS" Kyakkyawan Matashi Mai cikar Zati Tare da Quruciya. Sauke Idonta tayi akan System din gabanta ba tare da nuna alamar Kamanninsa Sunyi Tasiri akanta bah. Ta riga ta gina Katanga me tsayi A zuciyarta wanda kamani, kyawu koh wani charisma na 'Da Namiji ba zae iya rushe su bah.
Ammar Ya fara Gabatar da Taron Da Sallama Sannan ya cigaba d bayani akan abun Da ya tarasu Na sabon Project dinsu da zasu fara, Amrah ta ba da dukan nitsuwarta gurin sauraro..!
Bayan gama jawabi Ammar Ya buqaci da ta tashi ta gabatar da kanta wa Sauran Ma'aikata kasancewar Yau Ranar ta ta farko a gurin Aiki.A nitse Ta tashi ta gabatar da kanta Sunana "AMRAH ABUBAKAR SIDDIQ"
Ni Computer Scientist ceh Mai Ra'ayin Bincike da Qirqira , Rayuwarmu A Yau Gaba Dayanta Ta koma Digital, Duk mai Son Cigaba Dole ya rungumi wannan Sauyi .......Haka ta cigaba da Expressing Idea dinta akan Sabon Project din da Suka saka a gaba ba tare da Shakka ko 'Dar d'ar bah Idanunsu neh Ya hadu da Na Ammar Amma Bata nuna Alamun Tasirin Hakan akanta bah ta cigaba Da Bayaninta a nitse kuma cike da Confidence.
Bayan Gama Taron, Ammar ya je Gabanta Ya Tsaya.....
"Nagode da Wannan Tarba A Rana ta ta Farko Ina Farin ciki Fara Aiki daku, Fatan Allah Ya Bamu Sa'a A Project din da muka Saka a gaba" Ta fada a nite Amma Cike da basarwa da nuna Bata buqatar Dogon Magana.'Dage gira Ammar Yayi Cike Da Mamakin Basarwan nata, Ya Saba Da yanda kowa ke Zumudi Da Rawan kan Magana Dashi Wanda ita ya fiskanci ba Hakan bane wanda Hakan Ya masa Amma Sai Shima Ya basar Yace , " I'm Looking Forward to seeing your work Amrah , Don't Hesitate to reach out if you need Anything".
Kada Kai Kawae Tayi Ta Dauki Jakar ta Ta fice Dogon Hijabinta da yaje har Qasa N binta.
Mamaki ne Ya cika Ammar na wannan Dabi'a.
Sai dae Kash , A Bayan Wannan Fuskan Quncine Da Baqin ciki Amrah Ke boye Wa , Tare Da Mugun Qiyayyar ta Ga Soyayya.
Shin Ya zata Kaya Tsakaninsu...??
Wacece Amrah?
Wannene Ammar...??Tambayoyi Masu Yawa Zasu Yi Ta kewaye a Zukatanku Karku Damu Wannan Dandano neh Kawae Shafin Farko kenan Na littafin "Love Beyond Scars"..........!!!!!!
Ku biyo ni ......!!
TheHalalWriter.......!!!!

YOU ARE READING
LOVE BEYOND SCARS
FanfictionIn the vibrant city of Kano, Northern Nigeria, Amrah, a bright and resilient computer science graduate, has built walls around her heart. Her tumultuous childhood, marked by her parents' separation, has taught her to fear love. With a quick wit and...