""MERI JAAN😍❣️""

2 1 0
                                    

Bismillahirrahmanirraheem
Godiya ta tavvata ga allah ubangijin talikae ubangijin annabinmu annabi muhammad (s a w) Allah kakaro dubun salati wanda ya xarce halittunka ga annabinka habibinka dan gatanka masoyinka kuma amininka muhammadur rasulallah sallallahu alaihi wassalam ❤️ ameenci da rahma sutabbata agareshi ameen y ravvu 🤲

  Ya Allah wannan shine littafina na uku wanda na rubuta Allah ka tallafamin badan halayenaba kuma badanniba sae dan dan gatanka habibinka muhammadur rasulallah sallallahu alaihi wassalam ina kamun kafa dashi y allah
  Ya Allah idan abinda xan rubuta baxae amfani al ummaba baxae faranta masuba allah karka bani ikon rubutawa yah Allah 🤲
  Allahumma salli ala sayyidina muhammad wa ala ali muhammad kama sallaeta ala ibraheem wa ala ali ibraheem innaka hamidun majeed
    
    {Ayshat fareeda mouser autar marubuta wacce akafi sani da 'yar gatan ma aeki 💗❤️}
 
Part 01

Bismillahirrahmanirraheem
______________________________________
_
   Wani jibgegen mutum nagani akan two seater irin wacce ake ajyewa a office dinnan sae wani kyakkayawan matashi yana gefensa kansa a kasa yana sauraran bayanan wannan mutumin "wannan shine next assignment dinku inada hope akan zaku iya"
  "Insha allah Sir we will",wannan matashin saurayin ya fada,
"That's good May Allah help and protect you",
"Ameen sir"saurayin ya sake fada "you can go"
   Sallama matashin yayi masa sannan ya nupi compound din gurin inda motarsa take sannan ya bude baya ya saka file din hannunsa ya zagaya mazaunin driver yashiga ya tada motar sae unguwan yan majalissu yana zuwa daedae wani dan karami gida me matukar kyau sosae,(miyau har yana zubomin daga baki ) Horn yayi gateman ya bude masa ya dannan hancin motar gidan (( hmm anannema nace wow 😲 wow ashe awaje babu abinda nagani chab ae idan nace maku xan gaya maku yadda wannan gidan ya tsaru wannan dan littafin nawa sae ya cika ban gama baku labarin komaeba inada wannan gidan yooni kudinme xan dinga nema uhm nayinan nabar tsegumin🚶))
 
Parking space yanufa inda jerin motocinsa ke ciki nan ya ajye motar kana y fito y bude backseat y dauki pile din yayi kofar parlour hannu yasaka akan madannin door din saeda yayi scanning dinsa sannan kofar ya bude shiga yayi hadida kunna hasken parlourn ((kae parlourn y tafi dani gaskiya)),, wucewa yayi upstair bedroom y shiga sannan ya ajye file din hannunsa da agogo da wayarsa a kan table din dakin yayi hanyan toilet y shiga, after fifteen minutes sae gashi  ya fito daureda towel da alama wanka yayi, wardrobe ya bude ya dauki kananan kaya rigada dogon wando yasaka yaje gaban mirror kamar wani mace yafara shafe_ shafe da fesha_feshe ya dau kusan minti 20 yana abu daya saeda yaji kiran wayarsane tukunna ya dakata yaje ya dauki wayar ya zauna a 2 seater kana ya kara wayar a kunnansa "hello",aka fada daga wanchen bangaren "hello"shima ya fada abinda aka fada din "am good ev..." "wait ngd ina lpy munada assignment indiya mumbai,inada bukatarku keda Irfan a get house dina yan majalissu karku dade gida xan wuce yanxunnan","ok sir gamunan xuwa", kit ya kashe wayarsa sannan ya dannan landline na kitchen ba,afi minti 3 ba akae noking kofar "yes coming ", yafada chan kasa kasa shigowa kukun yayi cikin ladabi ya gaishesa amsa masa yayi da kae,kukun ya ajye masa coffee ☕ mae zafi kana yayi tafiyarsa,tashi yayi ya dauko laptop dinsa ya koma y zauna,y kunnata yanata danne danne,chan kuma ya dauki coffee dinsa yana sha yana danna laptop dinsa,
  minti 25 dayin wayarsa aka danna kararrawa,masu aekin gidanne suka bude,shikuma ogan laptop dinsa ya dauka tareda wayarsa da abubuwan da zae bukata don bayason sake dawowa daga chan zae wuce gida
Yana sauka yaga iffah da Irfan suna ta washe mae baki,guri yanema ya zauna hadida ajye laptop din akan center table din parlourn,"hye mutumin", Irfan yafada hadida mikamae hannu suka gaisa,itama iffah gaisawa sukayi,kuku yakawo masu abinchi, Irfan ne yake tsokanarsa da,"kae mutumin kaki aure yanxu da babynka ita zata kawo mana wa innan kayan ba wani gardiba." "Hye aurannan lokacine fha nima very soon zan samu zuqeqiya na aura wacce zakuyi mamaki ammafa bayanxuba danni matata koh haifarta ba,ayiba." "Hhhhhhh wallahi harkaban dariya Ina tinanin kasameta nemafa haka zakaeta zama har sae kyawawan sun kare irinsu my iffah koh?" Cikin jin kunya ta daga jar.shiko gogan ta'be baki kawae yayi yana tsaki chan kuma ya ja numfashi yace:"back to business yanxu ga assignment dinda aka bamu zaku iya dubawa ina tinanin 1 weak xamu tafi"
"Oh ni Irfan naga ta yau waishi wannan me katon kan baxae barmu mu hutaba shi besan muna shan wahala baneba yaushe muka dawo daga saudiya amma yanxu har yasake turamu wani wae indiya karma harda wani karbowa dawani kanta kamar na zakichand!" "Toh kadakeni" ya fada kamar bashiba "kana ganin bazan iya baneba?" Banza yamae.iffa ce tace:" love mugani" amsa tayi tana dubawa kafin tace:"ae assignment dinma bashida wani tsayi sosae baza mufi 5month ba indae munsamu abinda mukeso,waeni Bashir khan dinnan ba yataba koyarwa a iman academic ba oga farhan?" "Yes yayi chuta dayawa sannan kuma akwae zarginda ake masa shiyasa akeson mu binchikashi mu bayyana gaskiya." "Ok toh amma oga farhan ya kake ganin tafiyar tamu?" "Eh today is Monday I think by Monday insha allah." "Ok toh Allah y kaemu yau xan fara shiryawa dan ni wallahi inama san indiya sosae." "Uhm tinda kinason india ae sae kitafi yanxuma nibabu inda zani."
"Oh allah bazakaba rantseda allah." "Ni ae basae narantseba aurena da My iffah nakeso afara maganar amma tsohonnan yaki barina na nutsu mtss." "Is okay nidae nasallami kowa ruwanka kaje ko aa inason nayi sallah yau a family mosque kuma yanxu saura 45 minutes ae sallah." "Toh sarkin ibada ae munsan kanason ibada basae ka mana iyayiba,tashi iffah na maedake gida sannan nima daga chan family house zan nufa." Fita sukayi dukkansu kowa yayi gurin motarsa iffah da Irfan dama mortor daya suka tawo shikuma ya dauki wata motar ba wacce yazoda itaba,suka bar gidan gaba daya, get Man nata daga musu hannu..
________________________________

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 26 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

""Meri Jaan😍❣️""Where stories live. Discover now