MENENE ILLA TA 13

16 5 0
                                    

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Allah yana buɗawa idrissa. Dalilin ya samu mutane wanda suka san kan kasuwanci fiye dashi, kusan komai su suke gudanarwa har Allah yasa ya ɗauki bintu suka koma cikin garin kaduna da zama saboda ya samu sauƙin maida hankali akan kasuwancinsa. A garin kaduna bayan komawarsu da shekara biyu Bintu ta haifi ƴarta ta biyu Bilkisu wadda ake kira da Mami saboda sunan hajiya yaya da taci, daga nan haihuwa ta tsayawa Bintu dukda ba haka taso ba, domin ganin yanda arzuƙin Idrissa ke haɓaka taso ace ta tara ƴaƴa da yawa don ta mamaye komai.
Dan Sosai kuɗin Idrissa ya tsone ma Bintu idanu domin a lokacin ta fara bayyanar da tsantsar son zuciyarta akan dukiyarsa. sedai Idrissa bai taba nuna ya damu da hakan ba, illama ƙara wadata da yayi.

Ta kan bijiro da buƙatu da dama wanda basu da amfani haka zai biya mata ba tareda dogon tunani ba. idan kuwa yaso yayi jayayya ta kan cusa masa wani abu ta hanyar faɗin yanda ta zauna dashi dukda danginsa basa ƙaunarta, yanda ta sadaukar da iyayenta ta biyoshi garin da bata san komai ba. Wannan yake sanyashi tausayinta sosai yayi mata abinda takeso.

Ta ɓangaren Hajiya yaya kuwa tunda zama ya mi'ka ta fara ganin banbanci sosai dalilin zawarcinta, tayi tunanin idan aka d'auki watanni Mai babban Allo zai maidata amma shiru har aka tafi shekara da faruwar abin, tun mahaifinta na yiwa Mai babban Allo alamu a ɓoye saboda kawaici har saida ya fito masa a mutum ya tambayeshi shi ko ze iya maida bilkisu ba?
Nan dai mai babban Allo ya goge idanunsa yace shi fa zama ya ƙare tsakaninsa da Bilkisu. Har tayin wata ƴar dangin mahaifin hajiya yaya sukaiwa mai babban Allo amma ya ce bashida shirin ƙara aure a wannan lokacin. Kawai suci gaba da tayashi da addu'a, amma shi kansa ya rasa wacce irin zuciya gareshi da ya kasa maida matarsa da yake matuƙar ƙauna fiyeda komai, kuma baya tunanin zai iya zama da wata matar idan ba ita ba.

Hajiya yaya ta shiga takura sosai domin matuƙar rana zata fito ta fad'i sai an maimaita mata nadamar dake cinta azuciyarta, tamkar ana sake hura mata wutar ƙaunar mijinta haka take ji, mahaifinta bashida maganar da ta wuce kashe aurenta da tayi gashi taƙi tayi wani auren, haka ma mahaifiyarta. Ta shiga takura sosai wanda har idrissa dake kawo mata ziyara akai akai saida ya fahimta. Lokacin da kasuwancinsa ya haɓaka ne ya nemi izinin zai d'auki mahaifiyarsa ta zauna dashi. babu wanda ya musa masa domin a wurin iyayenta da zaman zawarci da takeyi tana ja musu magana a gari gara taje ta zauna da ɗan nata a can kadunan

Komawar Hajiya yaya kaduna ya kusan zamo fitina a zamanta da Bintu, duk haƙuri da kauda kai irin na Hajiya yaya saida ta kawar ta yiwa Bintu magana kan wasu halaye da taga tana aikatawa. daga nan bintu ta d'aukewa Hajiya yaya fuska, wulaƙanci da rashin kunya suka samu gurbin zama a tsakaninta da uwar mijinta, fitsarar yau daban ta gobe daban. Ƙiriƙiri take hora Hajiya da yunwa domin shi Idrissa ba mazaunin gida bane, sam baya dawowa da wuri sai dare, wannan yasa hajiya yaya bata da damar cin abincin rana a gidan haka Bintu zata dafa taci har ta baiwa maƙwabta Hajiya yaya na kallo, duk da wannan bata taɓa nunawa Idrissa abubuwan da Bintu ke mata ba sai addu'a take tana mata fatan shiriya. Sosai take nadamar amincewa da auren Bintu da tayi har tayi sanadiyyar nata auren gashi tana zaman wulaƙanci tareda wadda bata san darajar uwa ba. Ganin abubuwa sai gaba sukeyi ya sanya ta nemi Idrissa ya raba mata gida da Bintu.

Idrissa ya shiga damuwa sosai a kan haka amma ta nuna mishi ba wani matsala bane. Kawai bata son takura musu ne yasa ta zaɓi hakan, a ɓangaren Bintu nunawa tayi bata son tafiyar hajiya yaya amma yana fita harda shewarta, daga baya ganin yaƙi amincewa Bintu da kanta ta bashi shawarar ya baiwa hajiya abinda take so yace zaiyi tunani akaim domin aikinsa a ko wani lokaci zai iya koma birnin taraiyya Abuja, sabida suna shirin buɗe sabon kamfaninsu a can.

Saida hajiya yaya ta ƙara shekaru uku cikin wannan ƙuncin sannan Allah ya nufi komawar Idrissa Abuja. ya raba musu gida wanda shine karo na farko da hajiya yaya ta samu ƴanci bayan rabuwarta da mai babban Allo.

MENENE ILLA TA?Where stories live. Discover now