MENENE ILLA TA?
14
A wannan Rana kusan Raba dare Aminatou tayi tana tunani mai zurfi akan maganganun da mami ta gaya mata, juyi kawai takeyi a saman lafiyayyen gadonta tana tunanin makomar rayuwar yaran, Ajiyar Zuciya ta sauke mai nauyin gaske. lokaci guda ta migina zuwa gefanta tana kallon Fuskar Mami wadda keta kwasar baccinta hankali kwance.
Gabaɗaya sai taji tausayin yarinyar yai mata dirar mikiya zuciyarta, a yanda take jin ƙaunar yarinyar a ranta Bai kamata ta barta da gurbin kewar mahaifiya a tareda ita ba, idan har ƙaunar da takema yarinyar gaskiya ce to ya zame mata wajibi ta zame mata majingina tunda Ubangiji haka ya ƙaddara mata.
Lumshe idanunta tayi a hankali tana jin yanda zuciyarta ke dunƙulewa a tsakanin ƙirjinta, A haka bacci mai nauyi ya ɗauketa ba tareda ta sani ba har sai da ta makara sallar Asuba, Baba Sahura ce ta ƙwanƙwasa musu ƙofa jin shirun yayi yawa, Aminatou Bata fito ba gashi kuma zataje aiki yasa tazo ta buga mata ƙofar.
Cikin mamaki da al'ajabin baccin daya ɗauketa Aminatou ta bufe fararen idanunta tana karanto addu'ar tashi daga bacci kamar yanda annabin Rahama ya koyar, sannan ta tashi zaune tana kallon Mami da har lokacin take sauke numfashinta cikin Kwanciyar hankali, a nitse takai hannunta saman fuskar yarinyar tana ɗan taping chicks ɗinta a hankali ta ce"Mami... Mami Mami.. Daure ki tashi lokacin Sallah ya wuce."
Ɗan turo baki mami tayi cikin mayen Bacci ta ce," Aunty Aminatou don Allah ki bari inɗan ƙara kaɗan Allah baccin bai isheni ba plsss."
Miƙewa Aminatou tayi ta shiga toilet don tasan idan ta biyema Mami haka lokaci zai tafi ya barsu ba tareda sunyi abin kirki ba, alwala ta ɗauro a gaggauce sannan ta fito ta ƙara tashin Mami kamin ta tayar da Sallah.
Suna breakfast Mami ta nufi d’akinsu domin ta shirya, maryam ta tarar tana waya tunda taji tana magana ‘kasa-‘kasa tasan da momynsu take waya, kayanta ta cire ta d’aura towel ta shiga toilet domin tayi wanka.
“Muna kankia”. Maryam ta furta a hankali cikin wayarta domin bata so Mami ta san da momynsu take waya ta lura ko hirar mahaifiyar tasu Mami bata so suyi.
Wani tsaki Bintu ta ja cikin wayar ta ce “uban me kuma ya kaiku kankia a wannan lokacin? Ina makarantar?”
Numfashi Maryam ta ja tace “momy ai lectures basu kankama ba tukuna, ban koma ba kaida sai next week dady yace zamu sayo abubuwan da zan koma makaranta dasu, banida matsalar hostel har nayi payment ma tun kafin a koma, kuma momy friend ɗita ta kama min gado”.“Naji amma wannan ba hujja bace da zaki dinga biye mishi kina wasa da da karatunki, saboda shi be maida hankali yayi karatu mai zurfi ba shine yake so yay miki baƙin ciki ko?" Bintu ta firta hakan cikin son ta ɓarar da darajar Idris a zuciyar yarinyar
"Momy baƙin ciki kuma?" maryam ta faɗi hakan cikin rshin jin daɗin abinda mahaifiyar nasu ta ce.
" in ba baƙin ciki ba to ubam me yake maki? koda yake nasan meyasa yake wannan ƙafafar, baze wuce don nace kada ki karanta karamci abinda yace bane tun farko. Kuma wllh da raina da lafiyata bai isa yasa ki karanta international Relations ba, shirman banza, yana fama da wani ƙaramin digree ɗinsa da baifi cikin cokali ba.""ita da nata ilimin yafi cikin cokalin ai sai ki koma gurinta da zama Maryam, in yaso saita baki abinda Daddy ya gaza baki a rayuwarki. Wllh maryam indai kikaci gaba da jefa kanki cikin sha'anin momy wllh nan gaba sai kinyi kukan da sai kin rasa mai rarrashinki......" mami ta faɗi hakan cikin fishi da ɗaga murya, sannan ta fice daga ɗakin zuciyarta a wuya.
Ƙuri maryam tayi tana bin hanyar da mami tabi da kallo zuciyarta na harbawa, daga can ɓangaren Bintu ta ce,"au dama wannan mara kunyar tana kusa dake shine kika barni naketa sakin zance?"
YOU ARE READING
MENENE ILLA TA?
Non-Fiction"Idan kina ganin hakan shine dai-dai a zuciyarki to kiyi hakan BINTOU. ni kuma nayi alƙawarin cewa bazan taɓa dakatar dake ba, sai dai kafin ki zartar da hukuncin da kike ƙokarin zartarwa ina so kiyi tunani Akan ƴaƴan dake tsakanina dake...." cewar...