The Great Conglomerate

1 1 0
                                    


It's Fatoumspassions INTENSE LOVE🔥

TSANANIN SO

Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM.

Chapter 0⃣1⃣

(The Great Conglomerates)

Azaune take qasan lallausan carpet din dake malale acikin parlour wanda yake fari tass kmr ki lashe, idanuwanta suna zubar da hawaye sakamakon zagin cin mutuncin da mahaifinnata ke mata wani dan qareran ashar ya danqara mata yana cigaba da xagaye parlour ya cikuikuye takardar dake hannunsa kafin ya jefo kan fuskar kyakkyawar budurwar dake shashsheqa tana zunbura baki gaba cikin tsantsar sakalci da shagwaba, kana ganin yanayin hawayen da kukan zakafi kiransa da na rainin wayo da shagwaba.

cikin wata irin tsawar dabe taba mataba aduniya yake fadin

"Asirina kikeso kitona SURAYYA, aurenki dududu saura sati 3 zakizo min da mgnr banza, toh wllh ko ki fadamin ubanda yay miki ciki kona illataki kowa yarasa mara mutunci kawai"

matar dake kashingide kan 3seater royal chair dake parlour ce tafashe da kukan wanda xakafi kiransa dana makirci cikin rawar murya tace

" don kinga mahaifiyarki bata raye sokike kijamin zagi abakin duniya SURAYYA kinsan dama dangin uwarki ba kaunata suke ba zasuce nice na lalata ki,yanzu surayya banda sakarci ko iskanci xakiyi seki dauki cikin shege kikawomana Shi gida anasaura sati biyu aurenki dan rashin arziqi"

taqarasa tana kaimata duka aibata kaiga dukan nataba tamiqe dasauri tana dire kafa aqasa cikin kunkuni irin na yaran masu kudi marasa jin mgn tana fadin

"ni cikina bashege bane da ubansa kuma wllh kuka auramin ya nazy sena cigaba da bibiyar uban dancikina sbd shi nakeso nafada maku tuntuni aikun qi yarda ku auraminshi, sena haifamaku shi kunrene Shi tunda kune kuka jamin"

kwasheta da Marin da abbanta yay yasanya taiwani irin jaaa dabaya domin jinta dauke wa yay nadan lokacin,

tana dafe kuncinta xata kife tajita cikin faffadan kirjinsa yaymata rumfa yana hanata faduwar,

ahankali tadago tana kallon kwayar idanunshi dake dara dara amman kalar idanuwan da akasarin mutanenmu ke kirada sexy eyes gareshi, yana ashanye ne kamar mejin barci ko wandaa yasha yay mankas kwayar idanun baka ce sosai wacca tadace da zara zaran gashin idanuwansa dakyakkyawar farar fuskarsa medauke da dogon siririn hanci, lips dinsa yan kanana jajir dasu kai kace lipgloss yasaka tsabar yajja suke kyalli.

ahankali yadagota yana daura kanta akafadarsa bakunya ta kankameshi tana rushe mai dakuka tana nuna masa abbanta cikeda shagwaba,

yakalli abban yana furta

" abba yanzu sury din ka mara she's a baby fa metai harhaka daxafi da zaka daga hannu kadaketa Abba"

ya fada cikeda murya maitaushi da tausasawa yaqara dacewa

"Abba inlefi tai don Allah amata fada Amman banda duka"

mamace tai charaf tana fadin

"hmmmm nazeeru kenan aiyau inkaji me yarinyar nan ta aikata, qila sekasa bulala kai,uhum kaduba yau aurennan naku saura sati biyu kacal tadakko mana abun kunya waiciki fatai"

Tafada cikeda son kai tsegumi tanason taji yajja Abba ze aurar da SURAYYA AHAKA

yatsine fuska yay irin ba adamunnan ba yake fadin

"wadin?

sury din?

ciki waihaka?

Yafada da sigar tambaya yadagota yana kallon idanuwanta,qifi qifi tai da ido irin na marasa gaskiya,yay murmushi kawai sanin halin qanwar tasa fiyeda tinani duk tana hakanne don afasa aurennasu,betaba tinanin kin auren datakeyi har yakai ta kirkiri wannan babban karyar tafadawa mahaifinta duk don afasa, which koyasha giyar wake baxe bari hakan tafaruba cikin bagarar daxancen yake fadin

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: 6 days ago ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

TSANANIN SO (INTENSE LOVE)Where stories live. Discover now