BA DUK ƘYALLI BANE GWAL
(When their hearts collide)
Na
CHUCHUJAY ✍️
CHAPTER 5
Koda Asiya ta shiga ɗakin su idanun ta na sauka kan Sa'adatu ba tayi wata wata ba ta hau kanta ta fara jinbga tana tsine mata,Maryam dake Babban ɗakin wadda a ƙalla zata yi shekaru Ashirin da tara ta shigo taga Asiya na Aikin jibgar Sa'adatu,da gudu tayi kan su ta janye Asiya da ƙyar kafin tace"wane irin hauka ne wannan,Hala kin shirya kashe ta ne?".Cikin wani irin kuka mai cin Rai Asiya tace"Aunty Maryam ki barni kawai na kashe ta ɗin dan ni ta riga ta kashe ni,kamar yanzu ke ce yarda kika kusa talatin ɗin nan babu wani tsayayyen,ki samu wani yazo ya ɓata miki ya zaki ji? "Haɗe rai Aunty maryam tayi sosai tace"bana san iskanci kuma,kada ki zage ni,duk Abinda aka ɓata miki dama baki chan chan ta bane,ita yanzu Sa'adatu mene ta ɓata miki?"cikin yanayi na mutuƙar tunzura Asiya tace"daga aikata ta taho da saurayina Yusuf shikenan ta buɗe wannan bakin nata mai kama da ɗuwawu ta fara faɗa masa maganar da Allah kaɗai yasa daga inda taji ta , Wallahi yau sai ta faɗa mun inda ta jiyo maganar da ta faɗa masa koda kuwa duk garin nan gatan ta ne".kan Sa'adatu ta kuma nufa tana faɗin sai ta kashe ta,cikin kuka da tsoro Sa'adatu tace"na rantse da Allah Aunty Asiya ban faɗa masa komai bai,Ni wallahi Bama Ni naje ɗauko sa ba Nafisa ce sai da suka taho na ƙaraso dashi kuma ki kirata ki tambaye ta".wani irin faɗuwa gaban Asiya yayi kafin tace"dan kutumar ubanki Nafisa na Aika ko ke?ina take ita baƙar shegiyar?wallahi yau sai dai ko ni ko ita"cike da tsawa ta sake maimaita "ina take"?..a tsorace Sa'adatu tace"wallahi ban sani ba amma hanyar sashen maza naga tayi".fuuu Asiya ta fita kamar wata Iska tana faman tafarfasa ɗan yau ko ita ko Nafisa sai ta faɗa mata inda ta san gagarumin Sirrin ta.
Wai ina Nafisa kam?
Tun rabuwar Nafisa da Yusuf da sa'adatu kai tsaye sashen maza tayi dan ganin Akram duk da kuwa yayi mata kashedi akan zuwa gurin,kamar yarda ta saba tana zuwa ƙofar ɗakin su Akram ba tayi wata wata ba ta yaye labulan da suka sake,da mamakin ganin ta Abubakar ɗaya cikin ƴan ɗakin dake sanye da boxers brief ya tashi da sauri ya jawo riga ya fara kici kicin sawa yayin da Umar dake Kallan cikin wayar Isma'il ya ke Kallan ta da takaici kafin yace"ke wai wacce irin jakar yarinya ce mara nutsuwa da Zaki shigo mana ɗaki babu wani tunani kamar ɗakin Mata?"Isma'il dake Bin ta shima da kallo na takaici ne yace"kada ka sake kiran ta jaka Umar, Nafisa lafiya"?.haɗe rai Umar yayi yace"Amma Brother Isma'il kaima ka sani ba sai na faɗa ba ,yarinyar nan nayi mana Abinda baya dacewa kana kallo dai Yaya Abubakar ko kaya babu jikin sa amma haka nan ta danno kai,mu da ɗakin mu kuma sai ace baza mu zauna yarda muke so ba saboda baƙuwar da bamu tsammani"?.taɓe baki Abubakar yayi yace"to laifin wane idan ba na Akram ba?indai kaga yarinyar nan Rabi mutum rabi Aljan tazo nan ai kasan gurin wanda tazo,ai ya kusa tafiya mugani idan kuma zata fara biyo Isma'il tunda naji shi zai cigaba da mata lesson ɗin da ba'a ɗauka,asara da ɓata lokaci"..kallon su kawai Nafisa take kafin ta kalli Isma'il tace " Ismai'l ,Boda Akram fa?"Ajiyar zuciya yayi kafin yace"Yana garden tare da Safiya , Please Nafisa ki wuce gida idan yazo zan faɗa mashi kinzo neman sa ba sai kinje ba shi zaizo".da mutuƙar Mamaki tace"Aw Allah,Ashe maganar da nake ji na cewa soyayya suke gaskiya ne da har zaije gurin ta a gadin sannan ace mun kada naje,to Wallahi ko shi Boda Akram ɗin bazai iya rabani da shi ba ballantana wata Safiyya duk ƙyanta kuwa,ai ba fina tayi ba". dariya Umar yasa kafin yace"ashe dai kin san ta da kyau ɗin ,kuma ina faɗa miki Sosai Big brother Akram ke Santa,ga kyau ga ilimi,mene zaiyyi dake daƙiƙiya".wani irin Kallon baƙin ciki Nafisa ke binsa dashi kafin tace"bazan tsaya kula matsiyaci irin ka ba,kai ma kuma Abubakar ka sani wallahi nafi ƙarfin ka,idan kuma kace karya ne dan Allah ka cigaba da shiga harka ta,dama idan masoyina ya wuce mai zanzo nayi gurin nan,aikin banza sai faman wari kuke na gardawa".bata sake faɗin wani abu ba kuma bata jira wanda za'a faɗa mata ba ta bar ƙofar ɗakin ta nufi Garden tana tunanin irin tijarar da zata yiwa Safiyya.koda ta isa Garden ɗin kan swing taga Safiyya Gefe guda kuma Akram zaune kan wani dutse dake kusa da ita yana ta faman washe baki .kamar iska haka Nafisa ta isa gurin, kafin suyi aune ta cilla Lilon da Safiyya ke kai da ƙarfi ,wani irin ƙara Safiyya tasa bisa ga rashin shiri da kuma sakan kan cewa kan Lilon,kafin Akram ya farga ta faɗo daga kai,da sauri yayi inda take domin taimaka
![](https://img.wattpad.com/cover/376455671-288-k323342.jpg)
VOCÊ ESTÁ LENDO
NOT ALL GLITTERS ARE GOLD (BDKBG),✓
Conto(When their world collides) Rayuwarsu tayi kamanceceniya, lokaci guda kuma komai yayi ƙokarin tabarbarewa sabida gaskiya akan al'amarin rayuwarsu, ita marainiya ce a yarda ta sani ,wadda aka tsinta a bakin hanya ,shin mai zai faru idan tasan cewa iy...