Babi Na Biyu

2.5K 256 67
                                    

Silar Ajali
Alkalamin Safiyyah Ummu-Abdoul

Babi na biyu

Sai karfe tara na dare suka samu isa gidan Goggo Salame kamar yanda mutane suke kiranta. Tafiya ce mai tsawo daga Katsina zuwa marke, ga rashin sanin takamaiman wajen zuwa hakan ya haddasa ma Salman damuwa ga yunwa yana ji hakan ya sa siraran hawaye gangarowa daga idanunsa. Da tambaya da ɓatan hanya suka iso gidan Goggo Salame wacce da farko kin sauraransu tayi sai da suka faɗa mata daga inda suke.
Faɗi take
"oh ni Salame, yanzu duk tsawon lokacin nan kuna wajen Amina bata taɓa nuna min ba. Ita uwar taku kuma abinda ta zaɓa ma kanta kenan. Allah ya shirya"

Ta sa musu tuwo da miyan kuka bayan ta tabbatar da sun watsa ruwa don kauda dauɗan da su kayi. Ci suke kamar wanda suka Share Shekaru babu abinci, nan take tausayinsu ya dira a zuciyar ta karo na farko tun bayan isowarsu gidanta. Bayan sun gama ci ta mika musu tabarma sannan tayi masu jagora zuwa ɗaya ɗakin da ke kallon tsakar gida. Suna godiya gaba ɗaya suka shige ba tare da ɗaukan lokaci ba barci ɓarawo yayi awon gaba dasu.

***
Washegari, tun bayan asuba Salma bata koma ba, gari na yin haske ta fito ta Share tsakar gidan tas, sai a lokacin ta kare ma gidan kallo. Tsakar gida ne sai ɗaura biyu da ke kallon tsakar gidan, chan daga yamma kuma akwai ɗaki amma da gani rabon da ɗakin ya amshi bakoncin mutane an manta.

"Haba, Salama, kya bari ki huta mana , ai kin san kina cike da gajiyan jiya kin fito kina ta aiki" Goggo ta faɗi tana kallon Salma.

Fara ce siririya, shekarunta basu wuce goma sha biyu ba, amma tsawon kafarta ya zarce na sa'o'inta. Gashin ta ya leko ta Kasar kallabinta, murmushin da Salma tayi don ba Goggo ansa ya sa kumatunta lotsawa nan take hawaye ya fara sintiri a idon Goggo tunawa da mijinta da tayi saboda wajen sa Rahanatu ta yi gado gashi ya bayyana a jikin jininta. An take bakin ciki ya cika mata zuciya tunawa da tayi da SILAR AJALIN mai gidanta masoyinta.

Juyawa tayi fuuuuu zuwa cikin daki kamar guguwa, sakin tsintsiya Salma tayi ta bita da na mujiya, in har ba idon ta ya gwada mata karya ba hawaye ta gani a idon tsohuwar. Toh ko me yasa? Taɓe baki tayi ta ɗauki tsintsiyar ta cigaba da shara. Sai da ta Share gidan tsaf sannan ta yi wanka ta chanza kaya, haka ma sauran yan uwanta.

Bayan sun gama cin abinci Goggo ta sa suka shirya ta kai su gidan yayanta hakimin Marke Alh Yunusa Ladan, ko da suka shiga, falonsa ta wuce bayan ta gaisa da matan sa, da sallama suka shiga falonsa, bayan sun gaisa ne take ce da shi,

"sai ka ganni da yara ko? Yaran yarinyar nan ne, jiya Amina ta turo su da yake chan wajenta ta kai su a Kano, wai mijinta ya gaji da rikonsu" ta faɗi cikin Yanayin ɓacin rai ko a ce bata son magantawa

"Dama kin san da zaman su ne, ina ce tun Shekaru goma sha takwas da ta bar garin nan bata sake dawowa ba, ko ta dawo ne bani da labari, kuma ina ta samo yaran da zata turo miki ki amsa" ya faɗi rai a ɓace. Bai tsaya jin ta bakin ta ba ya cigaba da cewa,

"ko akanta aka fara fyaɗe, duk wanda aka mawa shiru suke yi su rufa ma kansu da iyayensu asiri, amma ta kunso ciki sannan a ce fyaɗe, amsa min salame dama kin san da zaman su ne ko kuwa kin san da auren da tayi ta haife su" ya faɗi yana kara huhhura hanci da zare idanu.

Numfashi ma a tsorace su Salma ke fitarwa Salman ne mai karfin hali da jarunta, kukan da suka saki ya kara ankarar dashi zaman su a wajen.

"ku fita ku ban waje yayan gaba da Fatiha" ya faɗi a tsawace yana mai nuna musu hanyar kofa. Cirko Cirko suka taradda matan gidan a tsakar gida kasancewar sun ji duk abin da ya ke faɗi a ɗakin.

"Yaya ban san da zaman su ba sai zuwan da Amina ta yi bara wancan, kasan cewa gwamnati ta biya musu aikin haji, a can suka haɗu da RAHANATU ɗin wai tayi aure, da zuria. Kasancewar tsadar rayuwa a can ba irin na mu na nan bane bayan dawowarsu da yan kwanaki ta turo yaran. Yanzu shekaran su biyu kenan da dawowa. Kayi hakuri yaya, bani son ranka ya ɓaci sannan ni kaina ban ɗauki zancen Rahanen da mahimmanci ba wallahi. Kayi hakuri" ta faɗi tana kankantar da kai alamun neman gafara.

"in ba zata zo ba inaga za'a tura mata Yaranta. Bana son shiririta, a yi rainonta ayi na Yaranta, Sam ba zai faru ba" ya karasa alamun nuna ya sauko daga Fushin.

"kun ga kuyi hakuri ku yi shiru, in Goggo ta kore mu bamu da wajen zuwa, kun san dai sai an shiga jirgi za'a je inda innarmu ta ke, kuma ko a chan ɗin babu wani tsaro, amma ai tace mana zata zo ai ko" Salman kenan yake rarrashin Salma da Suhayl da suke ta kuka tun tsawan da ɗan uwan Goggo yayi musu, nan suka ɗaga masa kai alamun gamsuwa, shi kuma ya cigaba da cewa,

"Kunga in ta dawo baza mu yarda ta koma ba sai da mu, kuyi hakuri banda kuka banda riko, ba zaku gane gatan da Goggo tayi mana ba sai a gaba. Kunga dole muyi hakuri da ita "

Tashi su ka yi zuwa gareshi ya rungomo su. Haj Aziza uwargidan yayan Goggo nan take ta ji tausayin su da kaunar su ya mamaye ta, ba tare da ɓata lokaci ba ta ja su zuwa ɗakin ta. Sannan ta karɓa musu zoɓo da atine amarya ke siyarwa ta ba su suka sha.
"kar ku damu kunji nan gidan kakanku ne, dangin mqhaifiyarku kenan bata da kamar mu haka ku ma, Insha Allahu ba zaku yi dana sanin dawowa nan ba kunji. Duk abin da kuke so ku zo waje na kunji. Ba kuma zaku rasa ba Matukar bai fi karfi na ba."
Nan take zuciyar su ta fara haske, murmushi ya bayyana a fuskokinsu hakan ya sa ta cikin farin cikin da bata san dalilin sa ba.

Ko da Goggo ta shigo ɗakin bayan sun gama tattaunawa da Yayan ta hakimi, zama tayi suka sake sabon gaisuwa da hajiya.

"Yaran nan dai amana ne a gare ki da mu duka, in kika yarda aka raba ki dasu kamar yanda aka raba ki da uwar su ke kika so, don na lura har yanzu Sam baki san 'yancin da musulunci ya baki a matsayin mutum ba. Shi da ya aikata mugun aikin ba wanda ya tsangwama ma rayuwarsa sai su da ya nakasa" faɗin Hajja Aziza bayan sun gama gaisawa.

"kai matar yaya, kullum ke dai maganar ki yancin mata, ai musulunci bai yarda mu dinga fito na fito da maza ba, namu ko da yaushe hakuri ne, shi da ya yi fyaden ai ado ne macece dai bai kamata ta fita ba balle har a ganta ayi mata fyade, kin manta har haddi aka yanke ma malam, Allah ya masa rahma" ta faɗi tana murmushin da kallo ɗaya zaka masa ka san cewa iyakarta fatar bakinta..

"Musulunci ya ba maza da mata yancin neman ilimi, haka zalika fita aiki. Matsalar mu mata ba ma zurfafa ilimi sai ayi amfani da al'ada a dankwafar da mu da sunan addini. Laifin RAHANATU fita neman ilimi ko a ina aka karanta mata kar su nemi ilimi, mata sun rike mukamai a zamanin annabi ke mace sai da ta zama shugaban kasuwa, Umar ibn Al-Khattab da kansa ya zaɓi Samrah bint Nuhaik ta shugabanci kasuwa, Khadija yar kasuwa ce amma annabi bai hanata ba, Nusayba bnt kaab Alansariyya jaruma ce da ta fita jihadi da takobi. Ai da sai annabi yace mata basa fita aiki ko karatu, Kawla bint Azwar taje yakin Yarmuk tare da Khalid bn Walid, Aishat ummul muminin makaranta gareta a gida, Zainab bnt Ali itama tayi jihadi da ɗan uwanta Hussain. Kinga kaɗan daga cikin fita da mata suka yi a lokacin annabi. Al'adanmu ce hana mata fita, ko mai mace tayi don samun cigaban al'umma sai a hana ta saboda ana mata kallon mai rauni. Ɗaukakan kowace al'umma yana ga samun mata masu ilimi da nagarta.

Shi yanzu ya mata fyade, tsoron tsangwama yasa tayi shiru, ina ce satin da aka fahimci tana da ciki aka kama shi a ɗakin Amaryar kawunsa yana shirin mata fyade, ihun da tayi don tsabagen son rai ya ja mata saki daga Kawun nashi. Ke ba zaki ja taki jiki ba kin tsaya biye ta alhaji. Kar inji kin yi abin da ya ce, in ita ta dawo don kanta fabi Ni'ima amma in bata dawo ba fatan Allah ya albarkace aurenta da zuri'ar su. "

" Aameen ya rabbi, hajiya na gode, zan dinga zuwa kina bani tarihin mata sahabbai, don na lura ba boko ya wayar miki da kai ba, ilimin tarihin annabi da sahabbai ne ya buɗe miki idanu har ake ganin kin waye da yawa ashe tsabagen sanin yancin da musulunci ya tanadar miki a matsayin ki na mace mutum kamar kowa" Goggo ta faɗi tana dariya.

"kai Salame kenan, Toh akwai gatan da ya wuce wanda musulunci ya bamu, kawai al'ada muke ba fifiko shi yasa muke wahala.
Yanzu misali na RAHANATU, a dole akai zina da ita Kinga a musulunci ba ta da zunubi amma a al'ada tayi gagarumin abin kunya, hakan ya sa aka kore ta, maimakon a hukunta shi wanda ya fi karfinta yayi zina da ita. Yanzu dai ga gudunmuwa ta nan a sa su a islamiyya anjima. Allah ya raya mana su" ta karasa tana mai mika mata naira dubu uku. Nan ta karɓa tana godiya sannan suka yi sallama suka kama hanyar gida.

SILAR AJALI Donde viven las historias. Descúbrelo ahora