Dedicated to @hajjaris
Da fatan na dan wanke kaina. a userBAYAN SATI UKU
A cikin sati uku salma ta saba da garin marke, kullum safe zuwa azahar suna zuwa makarantar boko, da la'asar su je islamiyya. Ranakun Alhamis da Jumma'a kuma makarantar hadda haka Asabar da Lahadi da safe.
Bata yarda da kowa ba sai kawayenta uku duk da jininsu yafi haɗuwa da Ummita kasancewar halayensu kusan daya ne.
"Salma kalli tafiyan malam Aliyu, ashe chogane kafa yake yi "Ummita ta faɗi tana dariya haɗe da kwatantawa.
" Bari kiga na malam yahaya, shi haka yake tafiya kamar zai kwatanta, se kiji yana "heys heys you oba ziye" Ko turancin ma bai iya sosai ba" Ta karasa tana dariya haɗe da kwatantawa itama.
Shirun da ta ji sunyi ne yasa ta waigawa aiko karaf idanunta suka haɗu da na malamin english. Bata jira komi ba ta ari na kare tayi cikin ɗalibai masu siyan kayan tara."Ni kuma ya nake tafiya? Tashi ki kwatanta ko na zane ki" Ya faɗi ya na kallon Ummita,
"Ai ban iya ba tukuna, bara in kira salma tayi" kafin ya ankara itama ta sheka, nan ta iske ta a maɓoyar su, suka cigaba da dariya.
"Ashe baku ji nasihar da nai muku ba rannan, duk da na ga ku biyu kamar ba ruwanku, amma Allah kaɗai ya san abinda za ku shuka inda ace ban zo ba, ku tashi ku bani waje su kuma ku ce su guji haɗuwar mu. " ajiyar zuciya suka saki ganin ya juya ya tafi.
Tashi su ka yi zuwa inda suke sa ran zasu gan su Ummita, anan suka gansu suna cin gyaɗa hankalinsu a kwance
" wato ku don tsabagen iskanci ku jawo mana masifa amma ku gudu ku barmu ciki, toh wallahi da sake, don ni kam na tuba" fadin jiddo rai a ɓace
"nyayayaya! Sannu muslimat, muminat qanitat, ki ɗauke mu ki jefa mu wuta kawai, ba kiran tuba kawai zakiyi ba, mstww salma mu tafi don Allah" cewar Ummita tana mai jan hannun Salmah.
"ai ni fa na ɗauka laɓɓanta ne suka koma hakanan naga yar uwar ta ta zama kurman karfi da yaji, ai da na san abin da zai ce kenan tawan da ban gudu ba, Kinga yanda yake tafiya" tashi tayi tana kwatantawa har zuwa ajinsu yayinda Ummita ke dariya har da tsugunawa. Rufy da Jiddo kuma sun cika sun yi fam.
Suna gab da shiga aji ta ga Nura saurayin Nafisar ajinsu. Tun suna primary Aka san soyayyar da ke tsakanin masoyan biyu har satin da ya gabata da labarin sa ranan Nafisa ya karaɗe garin. Nan kuwa Ummita ta kwala masa kira gami da ɗaga masa hannu ya zo. Ai ko ba musu ya karaso Wajen.
"Ashe abinda ya faru kenan, ni bakin ciki na cewan da suke wai baka isa aure ba" Ta faɗi cikin Yanayin tausayi. Shiru yayi yana kallonta ganin ya rasa mai zai ce sai ta ɗaura da,
"Shi yasa karatu ke da mahimmanci, kai ka tsaya soyayya, har sunanta ka rubuta a hannu da wuta fa, Allah nura ba'a kyauta maka ba, ka ganka kyakkyawa da kai, in kayi karatu mai zurfi ba karamin gaye za'a yi ba kuma ba wanda zai ce baka isa aure ba lokacin. Allah sa hakan ne Alkhairi " Ta fa ɗi tana dariya, hannun Ummita ta ja suka wuce.
" kai Nura kai banza ne, kalli yar ficilar yarinyar nan ke faɗa maka magana ita a dole manyance ko, Ubanta zamu ci Wallahi" faɗin Jamilu abokin Nura.
"ka ga dai ta fi karfin ka ne shi yasa a
Kake wani kushe ta, se kace ba ita ta hana zuciyar ka sakat ba. Ku muje aji kawai. "faɗin Nura, da haka suka wuce aji.***
Tabuk Saudi ArabiaZaune take gaban fannin kimiyya a jami'ar Tabuk. Karatu take yi amma hankalinta baya tare da ita. Tana shirin zage jakanta don ta ɗauko wani abin ko ta a jiye kawai taji an fisge mata littafin da ta ke karantawa.
"ina kika kai min yara? Shekaru uku kenan nake zaryan ki faɗa min inda suke kinki, kin san dai nafi ki iko a kansu ko" Ya faɗi yana mai daga murya.
"suna Nigeria, don haka don Allah ka fita batu na, abinda ya haɗa mu ya raba mu shekaru da suka wuce." Ta bashi amsa
"inda aka gagara rike ki ne kike tunanin zasu rike nawa, ko ce miki akayi na Gaza kula da ku, ganin sama ta ce wannan don ku mata ba ku san tattali. "
" oho ma ka, ni daina gama magana, ka je chan ka Kara. Ya'ya kuwa sun maka nisa har abada" Ta faɗi tana shirin barin wajen
"Rayhan kar ki damu Ehn! zasu neme ni a duk lokacin da bukatar uba ya taso musu" yana kaiwa nan ya aje mata littafin ta ya juya ya tafi.
Wanda ya ji larabcin da suke yi da zubin ta zai rantse balarabiya ce ba RAHANATU bace ta marke yar gidan malam Tanko da goggo Salame.
Alo yan karanta yi shiru, Haba now haka mukayi da ku, it won't cost you much voting or commenting.
Ejor just click on d star... Den the comment box to say urs...
Loving yhu
Ummu-Abdoul
KAMU SEDANG MEMBACA
SILAR AJALI
Fiksi UmumDuk manoman dake wucewa zuwa gona a KAUYEN MARKE idan lokacin damina ne sun shaida fuskar RAHANATU . sun tabbatar da itace wadda tafi duk wani dan adama bi ta hanyar.... Saboda nanne hanyarta ta zuwa makaranta. Dabi'arta ce zuwa makaranta, duk wani...