Babi Na Goma

1.7K 245 46
                                    

Ganin sun watse ne ya fahimci abin da ke faruwa a wajen, nan ya saki dariyar da shi kan shi ya manta rabon da yayi irin sa. Ganin yana kafirin dariya yasa tsirarrun da suka rage ɓacewa da gudunsu.  Shima bai ɓata lokaci ba ya tafi zuwa inda su ka yi da Haroon zasu jira shi.

Tafawa su ka yi da ya isa nan ya fara ba Haroon labarin abin da aka yi bayan ficewarsu. Sakin baki galala RAHANATU tayi tana kallonsu suna larabci. Nan kuma sai tsoro ya shige ta "kar dai ya zo aljanu ne" wani sashi na zuciyar ta ya sanar mata da hakan. Kawai sai ji lema tayi a matse-matsinta, shar sai ga hawaye,  nan kuma sai ta kasa ɗaga kafafunta ta daskare a wajen. Tsayawa sukayi suna kallonta ganin ta tsaya cak.

"Baiwar Allah lafiya me ya faru? " Haroon ya tambaye ta.

Saukar fitsarin da ta ke makewa ne ya sa Haroon fahimtar a tsorace take,  se ya cire kanbas ɗin da ke kafarsa ya nuna mata da yatsa.

" kingani ba kofato garemu ba,  mutane ne kamar ki.  Gidanmu zan kaiki wajen babata, ina da kanni kamar ki sai kiyi kawaye kinji" Ya karasa yana mai lallashin ta.  Nan ya juya ga Imran ya yare masa abin da ya wakana da larabci.  Dariya yayi shima, yana kallonta yana dariya har suka isa gida.

Ɗakin babarsa ya kaita nan ya iske mahaifinsa na cin kwaɗon zogala, nan ya takaita masu abin da ya faru da kuma yanda Imran ya ce aurenta zai yi.

"kana ganin ma barshi ya auri karuwa?  Ina laifi ma y zaɓo ta gari a aura masa. Ni dai anya kar mu yi sanadin abin da gaba zamu zo muna dana sani" Ta faɗa tana jifan Haroon da harara.

"Kinga Binta tsaya, shin kinfi shi sanin karuwa zai aura,  ni a gani na jihadi zai yi sai dai kafin nan ke faɗa mana gaskiya me ya haɗa ki da gidan da aka tsinto ki" Ya karasa yana mai kallonta.

Jikinta na makyarkyata ta labarta masa labarin ta sama sama tun daga fyaɗen da Hadi yayi mata, zuwa mutuwar mahaifinta da haɗuwarta da Laraba. Nan take jikin mahaifiyar Haroon yai sanyi, 

"kin ji dai abin da yayanki yace, abokinsa ya ce aurenki zai yi.  In kin amince amma sai na je can garin naku in tabbatar da maganar da kika faɗa.  Na san cewa duk abin da mace tayi zunubi ne amma sak ɗinsa ga namiji ado ne.  Zuwa jibi zani garin in Allah ya yarda, ko kuma zan ma malam Audu mai gadi  magana in za shi ganin gida sai in bi shi, don wancan satin ya dawo, kuma yana cewa ba zai daɗe ba zai koma, sai mu koma insha Allah"

Da haka aka kira kanwar Haroon laminde ta yi ma RAHANATU jagora zuwa ɗakin kwanarsu.  Sannan ya aika a kira Imran.  Nan ma nasiha yai masa sannan ya faɗa masa abin da ya yanke. Yai godiya sannan duk akai haramar kwanciya.

                           ***
Sai bayan kwana biyu sannan Mahaifin Haroon ya samu damar haɗuwa da  malam Audu mai gadi.  Bayan sun gaisa ya ce da shi

"Nayi tsintuwar wata budurwa yar garinku,  wai an koro ta ne daga can shine nake so in zaka koma zamu je tare don karin bincike " Ya faɗi  fuskarsa a sake wanda hakan ɗabi'ar sa ce,  da wuya mutum ya faɗi lokacin da ya ganshi cikin ɓacin rai.

"kar dai ace yar gidan malam Tanko ce,  Shegiyar yarinya duk da laifin uban ne,  wai a dole sai tayi boko,  ko anan zan iya kidaya matan da ake bari zuwa boko.  Toh garin yawon boko Hadi yayi mata fyaɗe,  shine ta kunsa ciki. Da ta haife abin kunya aka kora ta,  wallahi kar ka bari ta haife maka bala'i a gida don me za'a yi da wacce ta bari har namiji yayi sha'awa, ta sa shi yi mata fyaɗe.  Ni ba zani marke ba sai nan da wata biyu" Ya faɗi  yana kumfar baki, zuciyar sa kirin fiye da bakin gawayi.

Mahaifin Haroon bai iya ce masa komi ba sai shafa masa baya da yayi yana murmushi ya wuce ta gefen sa ya wuce gida.  Nan ya sa aka kira RAHANATU,  ta shigo a sanyaye duk da ta dan fara saba wa da mutanen gidan amma duk da haka a tsorace take don gani take suma zasu kyamace ta kamar sauran mutanen garinsu.

"Na haɗu da malam Audu megadi. Ya faɗi daidai abin da kika faɗi.  Zan gaggauta aurar da ke ga Imran don ko ba komi mun shaidi halinsa. Tun kafin a ɓata miki suna a garin nan don na lura malam Audu a fusace yake da ke,  ki sa a ranki baki da kowa sai Allah sai kuma mijinki. Ki masa biyayya, ki kuma rike sana'a, sadakinki ya ishe ki jari, sana'ar ki shine mutucinki.  Bani bani shi ke fara kawo matsala a auratayya.  Ubangiji Allah ya sa albarka a aurenku,  ya baku ikon hakuri da juna" Ya karasa yana jin radadi da tausayinta a ransa.

Bayan tafiyar ta ya kira Imran shi ma.  Sai da ya gama tsokanarsa sannan yace da shi

"kasan a musulunci namiji na amsar ma kan shi aure ko,  mu a al'adanmu wanda bai ci karo da addini ba namiji na tura wakili ne.  Mace kuwa dole sai da waliyyi  wanda dole sai ya kasance musulmi,  balagagge mai hankali.  Dole ya kasance mahaifinta in yana raye ko wakilin Mahaifin (wanda uban ya yarda ya wakilce shi)  ko danginsa a lokutan da bai da rai.  An yarda da limami ko alkali ya zama waliyyi a lokutan da mahaifi da danginsa suke kafirai ko kuma lokutan da ba'a san dangin yarinya ba, da dai sauran lokutan lalura.  Toh Kaga ba'a san dangin mahaifinta ba,  asali ma su suka kora ta,  ni yanzu tana karkashin kulawa na don haka musulunci ya bani damar in aurar da ita matukar tana sonka.

Ko bayan auren ina mai maka nasiha da ka ji tsoron Allah ka rike ta amana. Wajibi a gare ka ne cinta, shanta, tufafinta da karatunta. Allah baka ikon rike amana ya baku zama lfy. " godiya Imran yake zubawa don har ya cire rai ganin ba'a ce masa komi ba tun ranar farko sai ma ɓoye ta da babar Haroon keyi.

Please bear with me... 

I love you, do you??  Oya if yes;

Comment
Vote
Recommend
Share

SILAR AJALI Where stories live. Discover now