Babi Na Goma Sha Daya

1.7K 275 40
                                    

                ALKAWARIN ALLAH

Sati biyu kawai aka kara kafin a ɗaura auren Imran da Rahanatu.  Ba'a yi wani shagali ba amma cikin sati biyun nan baba (mahaifiyar Haroon) ta kintsa ta da duk wani abin da ta san na gyaran jiki ne.  Fatar ta ya sha lalle don sati tayi tana Wanka cikin ruwan lalle. 
Mata ke ta shiga da fice wanda mafi yawansu yan uwa da makota ne da Baba ta gayyata.  Bayan sallar isha'i aka ɗauke ta zuwa ɗakin da aka ware ma Imran a cikin gidan.  Tana kuka inna mairo kanwar baba ta riko ta. Faɗi take "shiga da kafar dama kina mai ambatar bismillah"  haka suka shiga ɗakin da ya sha daɓe da fentin farar kasa.

Anyi kwanan amarci, amare da kawayenta, wa'inda duk kawayensu laminde ne. Washe gari daga cikin gida aka kawo masu abin kari, da kuma na rana,  bayan nan ne aka yi buɗan kai.  Da dare abokan ango suka shigo aka siya baki kafin a watse a barsu. Nan ne fa maganar kurame ya tashi don daga ita har shi ba wanda ke jin yaren wani.

Da safe baba ta tada su,  nan ta fito da farar zanen da basu san da zaman shi a ɗakin ba. "kwanta kar ki kuskura ki fito ɗakin nan,  mutuncinki zan nema miki a unguwar nan" Ta faɗi cikin raɗa.

Guɗa ta saki sanda ta fito daga ɗakin. Nan makota da sauran yan biki da basu tafi ba suka yi tururuwan shigowa. Da sauri matar megadi ta ɗaga zanin don ta tabbatar ma wainda ta ba labarin Rahanatu gaskiyarta amma sai aka samu abin da ba ta taɓa tunanin zata gani ba,  take ko ta furta "jini"  Sai kuma ta tuna tayi saurin kama bakin ta.

Nan fa gaɗa ya tashi, mata sai rera mata wakokin yabo suke, nan aka haɗa mata ruwan wanka na musamman, baba ta shiga ta chuɗata. Da zasu fito ta rungumo ta,  ita kuma ta langwaɓe kamar mai ciwo dagaske.

"Yarinya kin zama babba,  haka duk wata ya ta gari da ta mika ma mijinta mutuncin ta ke ji,  Ubangiji Allah ya sa wajen zamanki ne,  yasa abokinki ne ya tona asirin darare" faɗin wata dattijuwa tare da mika turmin atamfa mai igiyar shanya.  Daga nan mutane su ka yi ta mika mata kyaututtukansu ana shi mata albarka.

                           ****
Cikin wata uku da aurensu Rahanatu tayi ɓul-ɓul abinta, ta kara haske da cikowa.  Sa kanta da ta yi wajen koyon larabci ya sa take tsinta,  takan fahimci yaren amma maidawa kanyi mata wuya. Sun kasance karkashin gandun Mahaifin Haroon. Amma ta kan fita tare da su laminde su yi aikin wanke wanke da shara acikin gidan.

Duk zaman su babu abin da ya gitta tsakanin ta da mijinta sai dai duk wani kulawa da ake ba mutum ya zama ɗan gata tana samu hakan yasa ba ta san lokacin da son Imran ya shige ta ba, ta wani gari ne kawai ta tsinci kanta cikin halin matsanancin sonsa. Babu abin da tafi so sama da kasancewa tare dashi yana koyar da ita duk da bai sa wani isasshen lokaci don ya fara aiki a jami'ar Bayero da ke garin na Kano amma hakan yake sama maia lokacin karatunta. Hakan ya sata kara jajircewa wajen son koyon ilimin addini Dana boko.

                          ***
A Kwana a tashi ba wuya wajen Allah,  shekara ɗaya da auren Rahanatu kenan, hankalinta da na mijinta kwance suna masu kaunar junansu, tun bayan da ya samu aiki ya saka ta a firamaren matan aure ta higher islam take zuwa. Idan tana larabci sai ka rantse balarabiya ce haka in tana hausa ba ma zaka sa ta  jerin masu jin wani yare banda hausa ba.

Yau ma kamar kullum ya dawo bayan sallan la'asar, tankaɗe take a tsakar gidan suna hira da laure (kanwar laminde)  wacce ta kasance abokiyar aikinta tun bayan da aka wanke laminde.  Da sallamar sa ya shiga,  suka amsa masa  tare

  "marhabanbika ya rafiqie"  Ta faɗi tana murmushi. 

"Kaif" yace da ita yana kefta mata ido ganin yanda laure ta saki baki tana kallonsu. Bai jira amsar ta ba ya wuce ɗaki.

"ni ko Larabawa basu da kunya da tsare gida,  ji yanda yake wani kashe miki murya da murmushi.  Ai sai ki raina shi" faɗin laure wacce bata taɓa gani tayi shiru. Murmushi kawai Rahanatu tayi, ganin bata da niyyar bata amsa sai ta cigaba

"ko a musulunci ai kunya wajibi ne,  ku ba kwa ko kunyar a san mata da miji ne ku,  ba kwa ganin juna ku kauda ido, abin takaicin ma da yaren da ba mu ji kuke yi" dariyar  da Rahanatu ta yi ne ya tsayar da ita.

"menene kunya a aure in har za'a haihu iyaye da kowa yai murna,  ke ni raba ni don Allah,  miji na ne kuma Lada nake nema ta yi masa murmushi shima in ya min lada zai samu.  Raini kuma da kike magana mace mara tarbiyya babu abin da miji zai mata ta ki raina shi.  Ni zan shiga wajen shi ki karasa tankaɗen" Ta karasa tana mai kakkaɓe jikinta sannan ta wuce ɗakinta.

Nan ma wani sabon gaisuwa tayi masa, maimakon ya amsa ɗaga ta sama yayi yana zagaye da ita.  Sai da ya gaji ya sauke ta ya rungume yana sumbatarta ta ko ina

"mun samu gurbin karatu, zan yi doctur (PhD)  in na je sai in samo miki ighama (resident permit)  da kuma makaranta inda za ki yi sakandire ɗinki." murna ya cika ta don cigaban da mijinta ya samu.  A wani ɓangaren kuma gabata sai faɗi  yake don basu taɓa nesa da juna ba.

Murnar ta bayyana tare da kwararo masa addu'a, nan ya shiga nuna masa takardun tafiyarsa da aka turo masa.  Yana mata bayani wasu ta gane wasu kuma bata fahimtar abin da yake nufi.

"Amma zamu je Sudan kafin ka koma karatun ko, ka ga wancan karan kai kaɗai ka je ya kamata a sanni" Ta faɗi gabanta na faɗi don ta san zancen da ya fi tsana kenan.

"ban sani ba ko ku a al'adanku an amince ma mace ta tambayi namiji dalilin yin abu ko ta umurce shi da yin abu, mu dai a Sudan ba ma haka" Ya faɗi  a hankali amma duk fara'ar da ke kan fuskarsa ya ɓace ɓat kamar anyi walkiya an ɗauke.

Durkusawa tayi tana rokon gafararsa,  tsoron ta ɗaya Fushin miji don malamin su yace ko sallah miji ya hana mace tayi ransa ya ɓaci ta mutu bata nemi gafararsa ba toh wuta zata shiga.  Shafa kanta yayi ya fita ya barta nan durkushe.

                             ***
Sati ɗaya ya kara ya gama haɗa komi na shi na tafiya sannan ya wuce. Tafiyar da ya sa Rahanatu zama shiru shiru,  kewan mijinta ke damunta duk da ya tabbatar mata da watanni kaɗan zai yi ya haɗa mata komi na tafiyar ta itama.

Cikin ikon Allah wata shida kawai ya ɗauka ya gama haɗa komi nata na tafiya.  Ko da ya dawo duk sunyi murna da ganin junansu.  Sai da suka ke ɓe sannan ya ce da ita"lafiya kika rame kikayi baki Rayhan?"  maimakon ta amsa sunan da y kira ta da shi yasa ta jin Daɗi sosai, don ta san shaukinta yake shi yasa ya laka mata suna

"sunanki kenan dashi na miki duk wani rajista, Rayhan T Imran. Hakan zan dinga kiranki don ki saba" Ya ce yana murmushi.

Shirye shirye take yi ba kama hannun yaro,  ta zazzaga mako ta Da suke shiri tayi musu Sallama saboda halin rayuwa.  Ko da ranar tafiyar su ta zo da kuka ta rabu da su Baba don kuwa gani take ta rabu da wani sashi na jikinta.  Karfe na tara na dare jirginsu ya tashi sai Kasar Saudiyya.

How is you.... (Jennifer's english)  hope you are all doing great.  A very big thank you for sticking around.  Silar Ajali is no where without you.  Silent readers biko vote by clicking the star and  comment too filis anz filis...

Loving you

Ummu-Abdoul

SILAR AJALI Donde viven las historias. Descúbrelo ahora