SANSANIN MARUBUTA

114 3 3
                                    

[1/30, 7:56 AM] Mr, smiles😃: ✍🏻 *'''SANSANIN MARUBUTA*'''✍🏻
    ( _Don nishad'antar da marubuta_ )

*Daga Alkalamin:- Abdul Azizu- AAJ da kuma Abdu- Mr, smiles*

               EPISODE 01

*1st FEBRUARY 2017*

OHW (online hausa writer's)
Group ne daya kunshi mutane dadama wanda suka hada jinsi biyu wato maza da mata.
   Group ne mai cike da abubawa kala - kala wanda ake tattaunawa akai Kama daga kan rubutu, ka'idojin rubutu, dakuma taimakon kananun marubuta domin hannunsu ya zauna akan alkamin wayoyinsu,
   Group ne mai cike da d'inbin marubutan yanar gizo sama da mutum 90,
          ***            ***

A yau ranar d'aya ga watan February tunda sassafe misalin karfe 6 na safe,
  Abdul - mr, smiles yaturo wani sabon sako wanda ya saka marubuta dadama cikin farin ciki_ sakon ya kasance kamar haka....

SANARWA

Amadadin 'yan uwana marubuta maza da mata ina yimuku barka da yau,

A yau ranar 1st February Shugaba Muhammad buhari yana gayyatar duk wani marubuci na wannan kungiyar tamu wato OHW domin suzo wurin wani gaggarumun taro wanda za'a gabatar a ranar 3 ga watan February,

Tarone na marubutan Online ne zalla, inda baba buhari zai bayar da aiki ga kowane marubuci domin gwada basirar sa dakuma hazakarsa, wannan aiki yanada riba garemu marubuta domin idan aiki Ya kammala kowanne daga cikinmu yanada kaso 1.5m wato naira million daya da da rabi, wannan damace ga reku marubuta karku bari wannan garabasar ta wuceku,

Taron zai kasance A babbar harabar shugaban kasa wato villa,

Saikunzo

*Sako daga*
grp Admn 😃
           ****        ****
Tun daga lokacin murubta suka fara jera sunayensu acikin wannan shafin inda akalla akasamu marubuci sama da 60,  Labarin yasamo asaline tundaga ranar.....

*Muje labari*

               ***       ***

*GOMBE*

Basma err lele ce ke kai kawo acikin dakinta ita kadai tana nazarin yanda za’ayi taje wurin wannan gagarumin taro na marubuta amma ta kasa samun mafita, tsawon lokaci tad'auka tana wannan jeka ka dawon, saicen ta d'auki wayarta ta kira kawarta Safah wacce take a garin Kano da zama, bayan wayar tayi ringing, batare da bata lokaci ba Safah ta dauka, da hanzari Basma tayi Sallama Safah ta amsa mata, bayan sun gaisa,
    Sannan Basma tace “Safah kin ganni nan nakasa zama narasa hanyar da zan bi wurin fahimtar da iyayena dan su barni naje wurin taron nan”
   Safah taja nunfashi kad'an sannan tace “kin ganni nan shirye-shirye kawai nake na zuwan nan Abuja, rana kawai nake jiran tazo dole mudira FCT” takarasa maganar tana dariya
  Basma tad'an zare edo kamar safah naganinta sannan tace “kenan ke an barki ki je?”
  Safah tayi dariya tace “ bari kai !!! kinsan hutu ake ba’a zuwa school, to shi ne nace zanje Abuja gidan Gwaggo ta a can zanyi holiday dina”
   Basma ta shagwabe fuska kamar zatayi kuka Kafin tace “ke kam abin ya zo miki da sauki, nikam narasa ya zanyi”
   Safah tayi saurin cewa  “akwai yanda zaki yi mana, ina gidan kanen mahaifinki dinan, dakika taba bani labari me zai hana ki nemi yin hutunki a can, domin gaskiya banason kiyi losing zuwa taron nan tunda Raheem ma nasan zai je kinga saikuga juna, koya kike gani”
   Basma tayi murmushi kad'an sannan tace  “Good idea, kin ga kwakwalwata ta toshe tun dazun nan ban kawo wannan tunani ba, inaga haka za’a yi, amma gaskiya nagode sosai Kawata, Allah yabar zumunci”
  Safah tana dariya tace "Ameen, saimun hadu wurin taro"
  Basma tace " yawwa"
Nan sukayi sallama Basma ta kashe wayar,

*KATSINA*

Bayan Rabi’at SK Mash tashigo cikin gidan tayi sallama mutanen gida suka amsa mata, cikin hanzari tagaidasu sannan ta mike bata tsaya ko ina ba sai d'akin Amrah inda ta tarar da ita tana chat a kwance saman gado,  Rabi’at takarasa bakin gado ta zauna, har ta zauna Amrah bata lura da zuwanta ba, saboda hankalinta na wajen chating, saida Rabi’at ta daki  kafanta  sannan Amrah ta zabura ta dawo da hankalinta wurin Rabi’at, cikin yanayin mamaki Rabi’at ta dubi Amrah tace “Wai ke me kike ne? har na shigo ina faman sallama baki amsamin ba?”
   Amrah tatashi zaune tana murmushi “kedai kawata bari kawai, kinfi kowa sanin me nake yi, wallahi ina duba sakon nin mutane ne wad'anda suke aikowa na jinjina garemu akan novel din mu na Dodon Jatau” tana kai karshen maganar takara matsawa kusa da Rabi’at tare da nuna mata wayarta tace “ki duba fa kigani, wannan abin kamar wasa amma ki dubi yanda ya samu karbuwa awurin Jama’a”
  Rabi’at ta janye wayar gefe cike da nuna rashin damuwa da abin, sannan tace “Sis ba wannan abin ya kawo ni ba fa, halam yau baki duba texts na OHW GROUP ba"
Cike da rashin damuwa Amrah tace “A a banduba, Miye ne??”
Rabi'at tace “dazun nan ina hawa whatsApp sai naga group din Online Hausa Writers ya cika da sakonni masu yawa, harna ce bazan bude ba, saikuma kawai wata zuciya tace na bude, budewata keda wuya naga Abdul Mr. Smile ya turo da sanarwa, wacce tayi matukar razana ni, kinsanni game dason shiga abinda baishafanba.”.
Amrah ta ajiye wayarta gefe ta dawo da hankalinta gaba daya wurin Rabi’at, tana kallonta tace “ Sis cigaba ina saurareni”
  Rabi'at tace  “kin san me nagani?”
  Amrah dukta k'agu taji ta daki kafad'ar Rabi’at sannan tace “ sis gaskiya banda jan rai fa, kawai kiyi bayani ba sai kin tambaye ni ba”
  Rabi’at tayi murmushi sannan tace  “Sanarwa nagani wai Shugaban Kasa Baba Buhai yana gayyatar marubuta a duk inda suke, za’a basu wani gagarumin aiki wanda kowa zai iya samun kudi Naira Miliyan  d'aya da rabi 1.5m”
Amrah zare edo cike da mamaki take kallon rabi'at “Kee saboda Allah, banason karya fa”
   Rabi'at ta harareta cikin wasa “ karya zanmiki Allah da gaskiya ne, idanma karyace sai idan shi Mr, smiles din yakeyinta"
  Amrah ta fasa ihu cike da jindadi tace “wayyo dad'i zai kasheni, dan Allah kiyi saurin gayamin wane irin aiki ne wanda marubuta zasu yi har kowa ya samu wad'annan makudan kudi, idan ma da gaske ne mu ya za’ayi mu samu shiga wannan aiki/ irin wad'annan makudan kud'i aikinsan dole mukai jiki”
  Rabi’at tayi dariya tace “kedai bari, ai kinsan Abdul mutumin mune kuma gashi wannan kwangila garesa ta fad'o kuma ya saka dukkanin members din group dinsa yanzu hakama ana nan ana rubuta sunaye, kuma nasaka namu nidake da zarah bb”
  Amrah na wasar baki tace “kai shiyasa nake ji da group din nan domin akwaisu dakawo harkar karuwa” sai kuma ta tashi tsaye ta rike baki tana murmushi tareda duban Rabi’a tace “Duniya kenan, yau ace gani ni ce na mallaki 1.5m ai kuwa da kinga Shanawa, Allah har tafiya saina chanza”   Rabi’at tana dariya tace “ke ce za’ki shana koni, kenifa bari kiji harna fara lissafin abubuwan dazan saya dakud'in”.
Amrah na tsaye ta dawo zaune tabawa rabi'at hannu suka tafa tare da kwasar ihu najindad'i, sannan Amrah tace “ a ina ne za’ayi wannan taron kuma wane irin aiki ne?”
  Rabi'at tace “A Abuja za’ayi,  aikin kuwa sai anje can za’a sanar damu”
  Amrah takara zare edo  “Abuja!!!?  lallai abin ba karami bane, yanzu ni ce zan shiga Abuja har fadar Shugaban Kasa, lallai rubutun nan da wasu kemin kallon marar aiki zan more masa”
   Nan suka kara kwasar dariya harda tafi sannan amrah ta numfasa taci gaba da cewa “to sis ya za’ayi muje Abuja kina ganin za’a barmi kuwa?”
   Rabi’at tatabe baki tana kallon amrah cike da mamaki  “Harma tambaya kike za'abarmu, hmm ni wallahi harna samu karyar da zanyi, domin za’ayi auren ‘yar kawuna kuma a Kaduna ne, dan haka a can zan wuce bazan ma je wurin bikin ba”
  Amrah tayi saurin cewa  “yauwa shikenan sai ki biyomin kice rakaki zanyi, nasan Abba zai barni na rakaki”
   Rabi'at tana dariya tace "hakan kuwa za'ayi sis, dole muji kanmu a vila"
  Suka kara kwasar dariya  suka tafa tare da rungumar juna suna murna..

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 18, 2017 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SANSANIN MARUBUTAWhere stories live. Discover now