Dedicated to @ummyasmeen
Dearest
Manage this pls. Thank you for you for sticking around we r now #2 in general fiction. Lets hit the highest Rank with our love... I will update later and u shower me with ur votes and comments."Assalamu Alaikum warahmatullah" Ya faɗi yana mai shiga gidan gwaggo, ihun da Salma ta saki ne ya fito da Goggo da Baba Jamilu (kanin goggo) daga ɗakin ta.
"lafiyanki? Shegiya da idanu kamar... " bata karasa ba ganin jakunkunar da yara ke shigowa da su.
" lale maraba da Salmanu sannu da dawowa kaabo! kaabo inji yarbawa" da dariya ya karaso ciki duk da idanun sa sun gane masa abin da ta yi ma salma kunnuwansa sun jiyar da shi kalamanta.
"Oyoyo yaya Salman " Suhayl ya shigo da gudu da abokansa da suke wasan bauni a waje. Ɗaga Shi Sama Yayi Yana Murna Shima Don Gaskiya Yayi Kewan Kanninsa.
" Yaushe Su Ummi Zasu Zo Su ɗauke mu don mu huta Da gori" kwaf ta ji an gwaɓe bakin ta, ba kowa bane Goggo ce
"Makira, da idanunta kamar na uwar uban ta. Salon Ace muna musguna miki, ai yanda Jamilu ya zo da shawara haka za'a yi, aurar da ke zamu yi mu huta da Iskancin ki a gari" Ta karasa tana jan kunnen ta, nan take hawayen ta ya fara zuba.
Salman bai ce komi ba illa ya zauna a kujerar tayani gulma da ke tsakar gidan. Alwala yayi ya ranka sallolinsa da ake bin sa, sannan ya jira aka kira magariba ya sallata, sai bayan Isha'i ya dawo ya iske goggo ta rarraba kayan. Nan kuwa ya nuna mata sam ba haka bane don kowanne da sunan masu shi.
Nan ya cire na goggo ya bata, ya cire na kannensa sannan Ya cire na makota. Ahlin RAHANATU na Wattpad ma sai daya cire mu su dabino, zamzam, almiski da ta aiko masu na musamman.
Tsaraban malam na daban ne, shima a gefe ya sa da niyyar kai masa washe gari. Cikin daren aka mimmika ma mutane tsarabar su. Raba dare yayi da kannensa yana basu labari haɗe da nuna musu hotuna. Murna a wajen su ba'a ko magana. Tambayar sa suke yana amsa musu.
***
Washe Gari gidan goggo ya zama wajen hawan arafa saboda yan zuwa sannu da zuwa wanda mafi yawan su suna zuwa ne don tsegumi da son karasa labari."Salma Kiyi hakuri Wallahi ina son ki, ke ma kin san haka, wallahi raba mu aka yi se ɗazu ne fa baban Jidda ke ce wa ai zamu iya cigaba da miki magana amma banda shishigi." ummitr ke faɗin haka tun safe take bin Salmah amma bata samu fuska ba daga Salma ba.
"Albarka kike so na kwashe miki ko me ne?" Salmah ta faɗi tana cin magani.
"Haba yar uwa, yar fara yar duma duma ki yi hakuri mana don Allah, mu shirya " faɗin Rufy da Jidda a tare.
" Ya halib ya asal, yar balarabiya kyakkyawar malam Audu bature" cewan Ummitr. Nan duk suka sa dariya. Shike nan suka shirya, ta ɗiba musu tsaraba mai yawa su kayan zaki da sauran ababen kalama.
***
Sati uku da dawowar Salman daga Saudiyya farin jinin su ya dawo a garin marke, sun yi sababbin abokai. Yayin da kawu Jamilu ya bazama a gari yana neman ma Salmah miji. Gidan liman yaje duk da kasancewar limamin da ya kora RAHANATU ya daɗe da rasuwa amma ɗan sa da ke limanci ya buga tsalle ya ce ai kafin rasuwar mahaifinsa ya bar wasiyya akan babu zuriar shi ba na malam Tanko.Ya tashi ya je gidan Alu wanzami. Nan ma cewa akayi "ai wannan yarinya idanunta a buɗe ya ke ko anyi auren guduwa Saudiyya zatayi ta bar miji"
Haka yake ta yawo gidajen wa'inda a tunanin sa in sun aure ta zasu taya shi musguna mata amma a cikin shekara ɗaya bai samu wanda ya amince da auren ba. Nan fa labari ya ɗauka a gari Salmah tayi kwantai duk anyi baikon kawayenta amma ita maza gudun ta su ke yi.
***
A cikin haka ne aka sha bikin Rufaida da jiddo lokacin sun kammala aji uku na sakandire. Ummitr da Salmah ne kan gaba a duk wani shiri da aka yi na auren. An yi biki an shagale nan ne Salmah ta haɗu da yusuf abokin angon rufaida da yazo daga malumfashi.
Ba'a watse biki ba sai da suka daidaita kansu. Murna a wajenta ba'a magana don ita kanta ta gaji da gorin da Goggo ke mata na cewa shekara goma sha biyar ba ta da mashinshini
Tun bayan haɗuwar ta da yusuf Goggo ta fara sarara mata, ya kan zo sau ɗaya duk sati biyu. A haka suka fahimci juna soyayyar su tayi zurfi sosai. Anan ne Hakimi ya sa baki a lamarin wanda tun farko bai ce komi ba goggo da kawu Jamilu ke kidin su da rawar su. Aikawa yayi a kira su har da su salma.Bayan ya buɗe taro da addu'a sannan ya kalli Goggo Salame ya ce
"Salame a iya sani na ni ne makwafin Mahaifin ki, in kuwa hasashe na gaskiya ce toh lallai kina da na gaba, haka kai ma Jamilu" Ya ce yana kallon inda yake zaune.
"Haka ne Alhaji" duk suka haɗa baki wajen faɗi
"Yauwa kuma ni na san na sauke hakkin ku da ke kaina, na rungume ku tamkar ya'ya na tamakar kanne na kuma tamkar abokai na tun ban da karfin haka har nayi har zuwa yanzu da karfin ya kare, haka ne? " Ya sake faɗi yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya
" Eh! " suka faɗi a hankali
" sannan cikin mata na na tabbatar da babban su Hajiya Azizah ta jawo ku a jiki ta rike ku da karfin ta da aljihunta ba tare da nuna gajiya akan abin da take ba, haka ne? "
" Eh Alhaji, fatan dai ba laifi muka yi ba"
"Eh toh ba laifi bane, in har duk abin da na faɗi ba daidai bane, amma in ko gaskiya na faɗi toh sai in ji dalilin ku da na yin abubuwa a gaban kanku" Ya faɗi yana kara haɗe fuska
Nan suka kalli junansu, idanu zuru zuru kamar mazari.
"Wayyo ga ranar ummitr ba ta kusa " salma ta faɗi a hankali don ta tabbatar da ummitr na wajen sai ta yi dariya.
"Tun zuwan yaran nan da farko ban amince da zaman su ba saboda halin da muka taso da shi na laifin mace shi ne laifi. Har gida Azizah ta samo malami ya min wa'azi bayan ta min doguwar nasiha akan hakkin mu na rikon yaran. Shi ma maganar ɗaya ya jawo Hadisai ingantattu da ya ce uwa ce da hurumin rikon Yaranta bayan mutuwar aure ko mutuwa, bayan ita sai uwarta, sannan yar uwarta mace se de in ba wa'annan ne dangin miji zasu shigo ciki.
Duk da kasancewar su hannun uwarsu ciyawar su wajibin Ubansu ne. Haka tufatar da su da duk wani hidimansu.
Kun ga kenan ba mu san dalilin ta na turo su ba, sannan kuma mu muka kore ta ba tare da mun waiwaye ta ba. In tana da laifi ɗaya to mu muna da ɗari kuma dole sai mun amsa a gaban Allah, sai yayi mana hisabi da malam Tanko akan amanar sa da ya bari, mun rike ko kuwa.
Tun lokacin na saduda amma ina kula da irin rikon da kuke ma yaran. Har zuwa tafiyar Salmanu wajen uwar da Dawowa duk da baku sako mu ciki ba ina sane.
Bara sai naji ana yawo kwararo kwararo ana neman mai kwasar salma a matsayin mata, duk nayi shiru na sa muku ido. Jiya ina zaune sai ga wasu dattawa biyu sun zo wai a ja ma Salmah kunne ta rabu musu da yaronsu ba za su haɗa iri da Shegu ba. Ban yi kasa a gwiwa ba na kira lambar RAHANATU bayan na amsa hannun Salmanu.
Na ce ta shirya dawowa don tafiya da Yaranta kafin a hallaka mata su" Ya karasa yana kallon su ɗai ɗai
"Alhaji hallaka kuma, duk kokarin mu na rikon yaran?
"kokarin ka wajen tallata su ga duniya ko wani irin kokari kake nufi. Ina sane da abubuwan da kake yi fa. Kar ka kaini bango in sa a kulle ka wallahi" Ya faɗi rai a ɓace
"Allah huce zuciyar ka. Insha Allahu zamu kiyaye" suka faɗi
Nan dai ya zauna yana musu dogon nasiha sannan aka koma hira na zumunci.
YOU ARE READING
SILAR AJALI
General FictionDuk manoman dake wucewa zuwa gona a KAUYEN MARKE idan lokacin damina ne sun shaida fuskar RAHANATU . sun tabbatar da itace wadda tafi duk wani dan adama bi ta hanyar.... Saboda nanne hanyarta ta zuwa makaranta. Dabi'arta ce zuwa makaranta, duk wani...