IMRAN SALMAN
Tun bayan dawowar Salman Nijeriya ya ji duniya babu abin da yake so sama da yaransa, musamman Salmah da ta tsaya masa a rai. Ya wanke hotunan ta ya kafa su a bangon gidansa. Kullum sai ya shafa ya ce
"kin fi kowa bukata na amma sabo da wani Kawa na duniya na zama Silar rabuwa da ke" kwallar sa kuwa kamar jira suke duk ya tunkari hoton sai sun zubo.
A dalilin haka ya shirya ya samu RAHANATU har ofishin ta kasancewar ta kammala karatunta na doktora (PhD) sai suka bata aikin malanta anan jami'ar tabuk ɗin da tayi.
"lafiya malam, in har gaisuwa ya kawo ka mun gaisa ka bani wuri" Ta faɗi bayan sun gaisa a mutunce kamar da gaske.
"a iya sani na ko Allah ana ma laifi kuma ya yafe ko da kuwa laifin ya kai dutsen uhudu ne. Balle kuma mutum, ina kara neman afuwa a gurinki sannan ina rokon arziki guda ɗaya" Ya faɗa a sanyaye.
Duk da jikinta yayi sanyi hakan bai sa ta nuna ba, illa ma kara tsuke fuska da tayi, ganin bata ce komi ba ya cigaba da cewa
"Na san na cutar da ke, na kawo ki duniyar da ba ki da kowa sai ni amma saboda ajizanci da nai miki sanadi na ki miki uzuri na yassar da ke a lokacin da kika fi bukatar kasancewa na tare da ke, ki yafe min, mu je Nijeriya a gyara mana auren mu, mu ɗauko yayanmu mu je Sudan sannan mu dawo nan mu cigaba da rayuwar mu kamar ko wane iyali. Yaranki na bukatar uwa, yarana na bukatar uba kuma babu wanda zai basu abin da suke bukata sai ni da ke. Don Allah ki duba kar ki ki" ya karasa yana mai durkusa mata hawaye na rigerigen fitowa daga idanunsa.
"in mafarki kake toh tun wuri ka tashi. Ni duniya in da wanda na tsana yana bayanka, ka san wahalar da Salmah ke ciki, mace mai rauni, ka zama sanadin da ya sa na kaita inda ba'a ɗauki mace a matsayin mutum ba, wallahi IMRAN da ba don ina tsoron hukuncin Allah ba da babu abin da zai sa in kashe ka ko a rage mugun iri"
"tsaya! Mugun iri har ya wuce uwar ki da ta gagara tarbiyyantar da ke, ke idanunki basa kallon miki alkhairin mutum ne sai sharri, ko ba gazawarki bane ya kaini ga aikata zina? Eh faɗa min da kika ganni a halaka kin yi yunkurin ceto ni? Duk naji ban kyauta ba amma ke ma har da ke a wajen ba da gudunmuwan rabewar gidanmu, yara ne ba ki kwada ki cinye na san dai komin daren daɗewa sai sun nemi uba, kuma ni ɗin ne zasu nema" tun daga nan ya sa kai ya fice ya barta da.
***
Yana koma gida ya rubuta wasikar ajiye aiki, ya fara haɗa kayan shi waje ɗaya. Cikin kwana uku ya haɗe duk abin da yake bukata ya sa mu dilallai da ke harkan ba da hayar gida (estate agents) ya sa gidan shi shi kuma ya koka gidan baƙi na ma'aikatan jami'ar tabuk da zama.Duk wani hannu da za'a sa masa an kammala cikin sati biyu, kuɗin sa ma haka bai tsaya komi ba, ya tattara yana shi ya bar Kasar Saudiyya zuwa Kasar sa ta gado wato Sudan.
***
Da faɗuwar gaba ya sauka a filin jirgin sama ta birnin Khartoum. Garin na nan yanda yake sai yan canje canje da aka samu na cigaba. Hawaye masu zafi suka sauka a kuncin sa. Tunawa da yanda ya tsallake mahaifarsa da iyayensa da duk wani dangi nashi saboda abin duniya. Gashi yayi bokon, ya tara kuɗi amma zafin rabuwa da nashi ya'yan ya hana masa zaman Saudiyya.
Dama masu iya magana kan ce "iskar da ta kaɗa yaro waje ita zata kora shi gida".
Nan dai ya samu racsha (keke napep) ya ce da shi" Inqazz za mu je"
"Khamsa jinai" Ya amsa masa.
Bai ɓata lokaci ba ya shige suka tafi. Sunyi tafiyar da ya ke ganin ta fi komi tsawo ko don ya matsu ya ga irin tarbon da za'a masa ne ko yaya ne shi kan shi bai sani ba.
***
Gidan nasu na nan yanda yake, sai dai akwai wasu sashi da ya ga alamun an gyara yayin da wasu na nan sai ma kara lalacewa da suka yi. Haske ya wadatar da ko ina kasancewar dubun dare ya fara sauka
KAMU SEDANG MEMBACA
SILAR AJALI
Fiksi UmumDuk manoman dake wucewa zuwa gona a KAUYEN MARKE idan lokacin damina ne sun shaida fuskar RAHANATU . sun tabbatar da itace wadda tafi duk wani dan adama bi ta hanyar.... Saboda nanne hanyarta ta zuwa makaranta. Dabi'arta ce zuwa makaranta, duk wani...