Babi Na Ashirin Da Shida

2K 245 83
                                    

Assalamu Alaikum warahmatullah

Am starting exams on the 8th Pls include me in ur dua. Promise u updates time to time Insha'Allah.

Love u ol
Ummu-Abdoul

Khartoum International Airport

"Hmmmn! " ajiyar zuciya kawai Salmah ta saki yayin da taji sanarwan saukar jirgin su. 
" ko da wani fuska zasu karɓe ki" wani sashi na zuciyar ta ya tunatar da ita. 
"Gbam! gbam! Gbam! " Kawai take ji sautin bugun zuciyar ta da ke ɗaga rigarta.

" Allahu ga baiwar ka nan kada ka sa rayuwata cikin garari" kawai ta tsinci bakin ta da faɗi.

Bayan saukar su, sun bi dogon layin bincike da karɓan kaya wanda ya kai musu awa biyu cur. Nan ta jiyo kiraye kirayen sallah, kai ta ɗaga taga garin ya rufe luf alamun magriba. Kallon agogonta tayi ta ga karfe huɗu da mintuna arba'in. Kallon agogon da ke manne a bango tayi, nan ta ga shida da minti arba'in.

"Subhanallah, amma karfe biyu fa jirgin mu ya taso. Ji lokaci" Ta sa mu kanta da faɗin haka. Ɗalibai biyu da suka sauka tare Rukayya da Zahra, suka sa mata dariya. Itama se wayance ta ce

"Yoh ni dai naga dai bai isa muyi tafiyar awa huɗu ba, sannan kuma ga agogo na ya nuna min karfe huɗu, ko nan ma irin Turai ne da sukan yi magriba da karfe huɗu in yanayi ya chanza" Ta karasa tana mai nuna iyakar gaskiyar ta kenan.

"kin san haka amma kin gagara sanin akan samu bambancin lokutan tsakanin yankuna" Zahra ta faɗi, Rukayya kuwa dariya ta kara tuntsirewa kamar ta gano Ummu-Abdoul tayi kuskuren larabci.

Sai a lokacin hankalin ta ya kai ga haka. Tabbas malamin english ya taba faɗa mata.

"Allah sarki ko yana ina, bawan Allah mai son mu amma tun da ya ce ta tafi aiki Kasar waje bai sake waiwayo mu ba" Ta faɗi a ranta

"kika sani ko yazo bakya marke"  zuciyarta ta tuna mata.

A haka har layi ya kawo kansu. Nan Rukayya tayi ajiyar zuciya tace

"Allah yayi, ni abin da ya sa na tsani Sudan kenan. Abba ya ce kowace kasa ana samun cigaba a wajaje musamman filin jirgi amma banda Sudan. Yace tun lokacin su na yara fa haka nan take sai sun kwashi layi kafin ka gama clearing komi tun daga arrivals har departure"

"Bara yan kasa su ji ki, ni ba ruwa na" kallon su sa salma keyi ya sa suka tambaye ta.

"ke me ya kawo ki Sudan? Mu Kinga karatu muke a jami'a."

"Nazo wajen Mahaifin mu ne, shi dan kasar nan ne amma babar mu yar MARKE ce a Nijeriya, amma yanzu tana Saudiyya"

"Allah sarki. In kin amshi jakar ki, can zaki bi zai sada ki da inda ake jiran baki" suka faɗa mata. Da murna ta gode musu, lokacin aka kawo kanta.

                          ***
Bayan ta gama komi ta je inda suka ce ta bi. Tana ta waige waige ga gari na kara rufewa. Can ta hango su zahra sun shiga taksi sun fice, kamar ance ta waiga nan ta ga wani mutumi dogo, ras! Gaban ta ya faɗi tayi saurin kauda kai.

"Daga ganin tsawon nan na mutanen Sudan ne ba MARKE ba, Marhabanbiki yaa Habibty"  Ya faɗi yana ɗan rungume ta, tare da sumbatar goshin ta.

Wani daɗi da ni'ima ya sauka a gare ta. "Alhamdulillah" kawai ta iya faɗi sai kuka shar. Share mata hawayen  yayi sannan ya rike hannun ta da hannun dama hannun hagun sa na rike da jakanta zuwa motarsa kirar Hyundai sonata 2.0t. Sai da ya tabbatar da ta zauna da kyau kafin ya rufe kofar, ya saka kayan a gidan baya sannan ya shiga gefen direba ya ja su suka tafi.

SILAR AJALI Where stories live. Discover now