Farko

4K 248 27
                                    

Tsokaci daga marubuciya

Assalamu alaikum. Ina mai fatan na same ku lafiya. Allah Ya sa ba ku manta da ni ba😂😂. Na sani, na dade ban waiwaye ku ba. To yau da kullum ne, wai mai sa ango ya mari amarya!

Amarya?! Har kun tuno min. Wannan labari ne na mai sunan Mamana, wato Fatima. Zaku min afuwa don ni ban iya saka sunan zamani ba😁 don haka zaku yi ta karo da tsoffin. Ko da yake ma, gwara a samu irin mu, wadan da za su rika tunasar da ku irin sunayen da din.

To, ita dai Fatima ta sha na ta gwagwarmayar rayuwa, kamar kowa a fadin duniyar nan. Ta fada soyayya, ta san dadin ta. Sannan ta dandana kudar ta. Hakan ba sabon abu ba ne. Don haka ku biyo ni mu sha labarin tare.

Don Allah a kada kuri'a ta hanyar danna maballin tauraron da ke kasa, da fadin ra'ayi kamar yadda a ka saba. Hakan zai taimake ni wajen rubutu mai kyau da ba da labari mai inganci wa ingantattun ma su karatu kamar ku.

Na gode kwarai da gaske da yadda nake samun goyon baya daga gare ku, ta hanyar samun damar bude littattafai na ku karanta ko da ba ku ce uffan ba. Saboda ka je birni a koro ka ma ai arziki ne, ko ba haka ba?

To na yi shiru🙊, wai yaro ya ga bulala😂. Kar ku ce na fara. Allah Ya kara zumunci, so kuma da kauna.

A daure dai a rika dan dubawa, don ni ma ba kullum zan rika rubutu ba. Kun sani, karshen mako ya kusa zuwa, sai yadda hali yayi.

Na bar ku lafiya, kar ku ce na cika ku da surutu. 😁
😍😍😍😍😍😍😘😘😘😘😘😘

Gurbin Zuciya Where stories live. Discover now