Falalar zikiri Da TASBIHI Da GODIYA GA ALLAH

209 8 1
                                    

[27/5/2017. 11:36 am]

®Eloquence Writers Association

*FALALAR ZIKIRI DA TASBIHI DA GODIYA GA ALLAH*

Writing by ✍🏽
Basira Sabo Nadabo

*Bismillarhir-Rahmanir-Rahiim*

Da Sunan ALLAH, Mai Rahama Mai Jin Kai.

Ya Allah ina rokonka da kyawawan sunayen ka kasa na fara lafiya Kuma ka bani ikon gamawa lafiya, Ya Allah yadda mukaga watan Ramadhana lafiya Allah kasa damu za'a gama lafiya kuma kasa muna cikin 'yantattun bayinka na kwarai wanda yake farin ciki dasu, Ya Allah kasa Azumi mu karbabbiya ce tun daga farkon ta har karshen ta, Ya Allah ka jikan iyaye na da yayyi na da kanne na da duk kan al'umman Annabi kasa mutuwa hutuce agare su damu baki daya, Ya Allah in tamu tazo Ya Allah kasa muyi kyakkyawan karshe mu tafi muna murna Don Tsarkin fiyayyan Halitta Annabi Muhammad (S, A, W) Amin Ya Allah

*ASTAGFIRULLAH*
*Sau Uku*

Ina neman gafarar Allah

Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: 'Na rantse da Allah! Ina neman gafarar Allah, Kuma ina tuba zuwa gare shi, a kowace rana sama da sau saba'in.

Domin karayin bayani ku duba cikin littafin Bukhari da Fat'hul Bari 11/101.


Daga Sa'ad bin Abi Wakkas, Allah ya yarda dashi, yace mun kasance a wajen Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: 'Yanzu ďayanku yana kasa aikata kyawawan ayyuka dubu a kowace rana? Sai wani mutum cikin waďanda suke zaune tare da shi ya ce: 'Ta yaya ďayanmu zai aikata kyawawan ayyuka dubu?' Sai ya ce: 'Ya yi tasbihi ya ce:

*SUBHANALLAH*

*Sau ďari*

Tsarki Ya Tabbata Ga Allah

..... Sau ďari, sai a rubuta masa kyawawan ayyuka dubu, ko a kankare masa zunubai dubu'.

_Domin karin bayani duba cikin littafin Muslim 4/2073.

*Prayer For Acceptance Of Good Deed*

*Rabbana Taqabbal Minnaa 'Innaka 'Antas-Samii'ul-'Aliim(u)*

Our Lord! Accept (this service) from us for You are the All-Hearing, the All-Knowing. *Q2:127*


*Prayer for Forgiveness, Help and Mercy*

*Rabbana Laa Tu'aakhidhnaa 'In Nasiinaa 'Au'akh-ta'naa*

_Our Lord! Condemn us not if we forget or fall into error;_ *Q2:286*



Ga Tambayar Mu Ta Yau:

Wata Rakuma Ce Ake Kiranta Da Rakumar ALLAH?

Domin bani amsa saboda mu karu da juna ku biyo ni ta wannan number ďin

07030515774

ALLAH kasa mu amfana da abinda muka faďa Amin Ya Allah

In Dedication to my late Father, Alhaji Sabo Nadabo and Alhaji Nuhu Abdullahi

May your gentle soul continue rest in perfect peace in paradise, Amin Ya Allah

Yar Uwarku Ce Dai a Koda Yaushe a Musulunci

Basira Sabo Nadabo

Falalar Zikiri DA TASBIHI Da GODIYA GA ALLAH Where stories live. Discover now