FALALAR ZIKIRI DA TASBIHI DA GODIYA GA ALLAH

301 3 0
                                    

[28/5/2017. 10:25 am]

®*Eloquence Writers Association

*FALALAR ZIKIRI DA TASBIHI DA GODIYA GA ALLAH

Writing by ✍🏽
        _Basira Sabo Nadabo




*Bismillarhir-Rahmanir-Rahiim

_Da Sunan ALLAH, Mai Rahama Mai Jin Kai

Ya Allah mun rokeka albarkacin azumin dake bakin mu, Ya Allah mun rokeka albarkacin watan Ramadhana, Ya Allah mun rokeka albarkacin littafin ka mai tsarki, Ya Allah mun rokeka Annabin Rahama, Ya Allah mun rokeka ka ɗauke wa nigeria bakin ciki da takaici, Ya Allah mun rokeka ka bawa shugaban kasar mu Muhammad Buhari lafiya, Ya Allah mun rokeka ka kara zaman lafiya a kasar mu nigeria, Amin Ya Allah

Ga Amsar Tambayar Jiya:

*Rakumar Da Ake Karanta Da Rakumar ALLAH Itace Rakumar Annabi Salihu (A.S)



  *ADDU'O'IN KIRAN SALLAH

*"Hayya alas-salaati (da) hayya alal falaah"

Ku Taho Ga Sallah: Ku Taho Ga Babban Rabo.

    A Maimakon Haka Sai ya ce:

_La'hawla wala quwwata illah billah.

  *Babu dabara, babu karfi da Allah, Bukhari 1/52, da Muslim 1/288.

Bayan ladanin yayi kalmar shahada, sai shi kuma wato mai sauraro sai ya ce:

_Wa'ana shhadu an la ilaha illal-lahu wahdahu la shariika lah, wa-anna Muhammadan abduuhu rasuulan wabil islami-diinan.

Ni ma ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi Kaɗai, babu abokin tarayya a gare Shi, kuma Muhammadu bawansa ne, kuma manzonsa ne. Na yarda da Allah Shi ne Ubangiji, kuma Muhammadu shine Manzo, kuma Musulunci shi ne Addini.

"Bayan ya gama amsa kiran sallar sai yayi salati ga Annabi (S.A.W) sannan kuma sai ya ce:

_Allahumma rabba hadhihid-da'awatit-tammah, wassalati-qa-imah ati Muhammadan alwasiilata wal fadiilah, innaka la tukhliful-mii'ad.

Ya Allah! Ubangijin wannan kira kammalalle, da wannan sallar da za'a tsayar da ita, ka bawa Muhammadu wasila (matsayin kusanci a cikin Aljanna), da matsayin fifiko, kuma ka tashe shi a matsayin abin godewa, wannan wanda kayi masa alkawarinsa. Lalle kai baka saɓa alkawari.

_Bukhari 1/52. Abin da aka sa a tsakanin baka biyu Baihaki ne ya ruwaito shi, kuma Shaykh Ibn Baz ya ce isnadinsa mai kyau ne. Duba Tuhfatul Akhyar, shafi na 38._  Allah shine nasani

_Sannan kayi wa kanka addu'a tsakanin kiran sallah da tayar da ikama, domin addu'a a wannan lokacin ba'a kin karɓar ta.

*Zikirin Bayan Anyi Sallama Daga Sallah

_Astagfirullah
            *Sau Uku*

Ina neman gafarar Allah

_Allahumma Anstas Salam Wa Minkal Sallam Tabarkta Ya Zal'jalallu Wal Ikram.

Ya Allah! Kaine Aminci, kuma daga gare ka Aminci ya ke. Alherinka ya yawaita, Ya ma'abocin girma da alheri.  *Muslim 1/414*

_As-Salam shi ne aminci; Allah shi ne mai tabbataccen aminci daga dukkan wani aibi ta kowace fuska. Allah amintacce ne a zatinsa daga dukkan aibi ko tawaya da zaizo cikin tunani, hakanan ma amintacce ne a cikin sifofinsa daga dukkan aibi ko tawaya, kuma amintacce ne a cikin ayyukansa daga dukkan aibi, ko tawaya ko sharri ko zalunci ko yin wani abu bada hikima ba. Don haka wannan suna ya kunshi dukkan abinda aka tsarkake Allah ga barin sa. (Duba Bada'i'ul Fawa'id 2/150-152).  [Bayanin mai tarjama]


*Prayer For Forgiveness and Safety From Punishment*

*Rabbana Innanaa 'Aamannaa, Faghfir Lanaa Dhunuubana Wa Qinaa 'Adhaaban-Naar(i).*

_Our Lord! We have indeed believed: So forgive us our sins and save us from the punishment of the fire. *Q3:16*

*Prayer For Forgiveness And Steadfastness In Faith.*

*Rabbana Igfir Lanaa Dhunuubana Wa Israafanaa Fi-amrinaa Wa Thabbit Aqdaamanaa Wansurnaa Alal-Qaumil-Kaafiriina(a).*

_Our Lord!  Forgive us our sins and anything we may have done that transgressed our duty; establish our feet firmly and help us against those that resist faith._ *Q3:147*

Ga Tambayar Mu Ta Yau:

*A Shekarun Musulunci A Wani Shekara Ne Mukeyin Azumi Yanzu Misali Shekara Ta 1430. To Azumin Mu Na Yanzu A Wata Shekara Ce Muke?

Domin bani amsa saboda mu karu da juna ku biyo ni ta wannan number ɗin


ALLAH kasa mu amfana da abinda muka faɗa Amin Ya Allah

In Dedication to my late Father Alhaji Sabo Nadabo and also Alhaji Nuhu Abdullahi

May your gentle soul continue rest in perfect peace in paradise, Amin Ya Allah

Yar Uwarku Ce Koda Yaushe A Musulunci

          Basira Sabo Nadabo

Falalar Zikiri DA TASBIHI Da GODIYA GA ALLAH Where stories live. Discover now