*Hi dearies.. thanks for adding Duniya makaranta. This is my first book and i hope u guys will love it. Keep on voting and commenting..i love u all.*
Fitar Anas ke da wuya, hajiya ta fito tana kwala kiran sunanta.. ke intisar!! Kulululu!!! Cikinta ya juya, saboda daga jin wannan kiran tasan ba na alheri bane. Tawa ta same ni, ta fada a cikin ziciyarta tare da mikewa da saurinta ta karasa gaban hajiya tace gani.
Hajiya tai mata wani irin duba wanda ake cwwa kallon tara saura kwata hade da janyo ta da karfin tsiya. Dan iyayenki anas tsaranki ne? Ban ce miki duk abinda ya bukata ai masa da gaggawa ba? Kin fara shigar min hanci da kudundune wallahi kuma zan fyato ki dan ke karamar alhaki ce.Hajiya dan Allah kiyi hakuri, intisar tace. Rufa min baki fitsararriya. Duk abinda 'ya'yana ke so daga yauu shi zaki aikata. Bana son taaurin kai. Dan kinga na sakar miki kwana 2 ba wai yana nufinki fara kawo mana raini ba.. intisar na shesshekar kuka ta gyada mata kai.. a fusace hajiya tace zaki amsa ko ba zaki amsa ba tace naji hajiya kiyi hakuri..fuuu ta wuce ta bar ta, dan hajiya na matukar tsoron bacin ran anas da ma 'ya'yanta baki daya.
********Ko da intisar ta karasa himilin ayyukanta, janyo tukunyar da ta gama girki tun dazu tayi, ta kuwa kama cin kanzon ciki kamar zata hada da tukunyar dan tsabar yunwa. Tana yi tana hadawa da ruwa a haka har ta gama ci duk da ba wai ta koshi bane. Ta jingina kanta a bangon kuntataccen dakinta ta zurfa cikin tunaaninta na yau da kullum.. wai ahin ina rayhaan ne? Ina ta shiga? Wacce orin rayuwa take yi? Hawaye suka ziraro mata da ta tuna da 'yar uwarta. Yaya zanyi ne da kuncin rayuwa ni 'yasu? Dama zan biki mummy da naji daadi. Au! Astagfirullah! Allah baya son irin wannan maganar. Bata san iya tsawon lokacin da ta dauka ba a zaune, bata ankara ba sai ji tayi ana shafa mata cinya. Ta zabura tare da matsawa baya. Tana dagobkai taga waye wannan sukayi ido hudu da anas idon nan yayi jajir. Gabanta yai mummunar fadiwa ta dube shi kamar zata fasa ihu. Cikin kakkausar murya ya daga hannu yana mata mgana. In kika kuskura kikai min wata magana sai na sassamaki. A raunace ta kalli shi da manyan fararen idanuwanta da sukai rau rau tace yaya anas kayi hakuri. Kaallonta yayi hadi da tuntsure da wata irin shu'umar dariya. Yau kumq ni akace wa yaya. Lallai na fara samun karbuwa. Haka nake sonki kanwata. Oya matso ki zauna nan ki kwantar da hankalin yaya. Waallahi inaa bukatar ki.ya miko hannu zai chafkota. Cikin zafi nama ta tsallake shi da gudu ta fice daga dakin .. ran shi ya kuma baci yace wannan yarinyar sai na koya mata hankaali. Bata son waye anas-cika-aiki ba. Yayi kwafa ya tashi yanaa hada hanya, da ka ganshi ka san a kwale yake.
***
So sorry loveey doviees. Been very busy these days, you know, fasting and all . But i promise u long chapters in sha Allah... keep on voting and commenting. Love u all
YOU ARE READING
DUNIYA MAKARANTA
عاطفيةlabarin rayuwa da abubuwan data kunsa na farin ciki,bakin ciki,samu,rashi,cin amana, da rikon amana