FALALAR ZIKIRI DA TASBIHI DA GODIYA GA ALLAH

40 1 0
                                    

[1/6/2017. 1:55 pm]
       [6/9/1438]

® *_Eloquence Writers Association



*FALALAR ZIKIRI DA TASBIHI DA GODIYA GA ALLAH



Writing by ✍🏽
       Basira Sabo Nadabo



*Bismillarhir-Rahmanir-Rahiim

_Da Sunan ALLAH, Mai Rahama Mai Jin Kai



Ga Amsar Tambayar Mu Ta Yau:


*Wa Sun Mu Basu Gane Tambayar Nan Ba Wato Ina Nufin Wanene Ya Fara Binne Ďan Uwan Sa A Doran Kasa?

*_Amsar Shine HANKAKA

*N.B*  _Eh Qabila Shine Ya Fara Kashe Habila To A Lokacin Da Ya Kashe Shi Sai Ya Rasa Yadda Zayyi Da Gawar Ďan Uwan Sa, Sai ALLAH (SWT) Ya Aiko Da HANKAKA Guda Biyu Suka Fara Faďa A Tsakanin Su Sai Daya Ya Kashe Daya, Sai Wanda Ya Kashe Dan Uwan Sa Yasa Bakin Sa Ya Tone Kasa Har Yayi Zurfi Sai Ya Dauko Wannan Gawar Ďan Uwan Nasa A Cikin Wannan Ramin Daya Tona Kuma Duk A Gaban Qabila Akayi Komai, Ganin Wannan Dabban Ya Tona Rami Kuma Har Yasa Gawar Dan Uwan Sa A Ciki Kuma Ya Rufe To Shine Shima Yayi Yadda Wannan HANKAKAN Yayi Kunga Kuwa HANKAKA Shine Malamin Farko Daya Fara Binne Ďan Uwan Sa A Doran kasa. Wallahu A'alam


*ADDU'AR RUKU'U

_Subhana Rabbiyal Azim_ *Sau Uki*

Tsarki ya tabbata ga Ubangiji Mai Girma *Abu Dawud, Tirmizi, Ibn Majah, Al-Nasa'i da Ahmad, duba cikin: Sahih Tirmizi 1/350.*

_Subhanakal-lahumma Rabbana Wabihamdika, Allahummagh-fir lii

Tsarki ya tabbata gare Ka, ya Allah! Ya Ubangijinmu, tare da godiya gare Ka. Ya Allah! Ka gafarta mini. *Bukhari 1/199, Muslim 1/350.*

_Subbuuhun Qudduus, Rabbul Mala-ikati Warruuh.

(Ubangiji) abin tsarkakewa, mai kuɓuta daga dukkan abin da bai kamace shiba, Ubangijin Mala'iku da jibrilu. *Muslim 1/534, da Abu Dawud 1/230.*

_Allahumma laka raka'atu, wabika amantau, walaka aslamtu, khasha'a laka sam'ii,  wabasarii, wamukhkhii, wa'azmii, wa'asabii, wamas-taqalla bihi qadamii.

Ya Allah! gare Ka nayi ruku'u, kuma da Kai nayi imani, kuma gare Ka na mika wuya. Jina yayi kaskanci gare Ka, haka ma ganina da ɓargona, da kashina, da jijiyata, da kuma abin da kafata ke ɗauke dashi. *Muslim 1/534, da Abu Dawud, Tirmizi da Al-Nasa'i.*

_Subhana dhil-jabaruut, wal malakuut, walkibriya'u, wal'azamah.

Tsarki ya tabbata ga (ALLAH) Mai dole, da mulki, da kasaitar ɗaukaka, da girma. *Abu Dawud 1/230, Al-Nasa'i, da Ahmad. Isnadinsa kyakkyawa ne.*


*The Continuation Of Earnest Prayers Of The True Believers

*Rabbana innaka Sami'naa Munaadiyan Yunaadi Lil-iimaani 'an 'aaminuu bi Rabbikum Fa'aamannaa.

_Our Lord! Verily, we have heard the call of one calling (us) to faith: 'Believe in your Lord' and we have believed. *Q3:192*

*Rabbana Faghfir Lanaa dhunuubana Wa Kaffir'annaa Sayyi'aatina Wa Tawaffana Ma'al-abraar(i).

_Our Lord! Forgive us our sin blot out from us our iniquities and take to Yourself our souls in the company of the righteous. *Q3:193*



Ga Tambayar Mu Ta Yau:

*Wata Sura Ce A Al'Qur'Ani Mai Girma Take Da Bismillah Guda Biyu?

Domin bani amsa saboda mu karu da juna ku biyo ni ta wannan number:


*In Dedication to my late Father Alhaji Sabo Nadabo and also Alhaji Nuhu Abdullahi

_May your souls continue rest in perfect peace in paradise, Amin Ya Allah



Yar Uwarku Ce Koda Yaushe A Musulunci:

    Basira Sabo Nadabo

Falalar Zikiri DA TASBIHI Da GODIYA GA ALLAH Where stories live. Discover now