(8/6/2017. 03:12 pm)
(13/9/1438 A.H)® *_Eloquence Writers Association_
*FALALAR ZIKIRI DA TASBIHI DA GODIYA GA ALLAH*
Writing by ✍🏽
Basira Sabo Nadabo*Bismillarhir-Rahmanir-Rahiim*
_Da Sunan ALLAH, Mai Rahama Mai Jin Kai
Ga Amsar Tambayar Mu Ta Jiya:
*17 Ga Watan Ramadhana Akayi Fadan Badar*
*ZIKIRIN SAFIYA DA MARAICE*
_Allahumma 'alimal-ghaybi washshahadah, fatiras-samawati wal'ard, Rabba kulli shay'in wamaliikah, ashhadu an la'ilaha illa anta, a'uudhu bika min sharri nafsii wamin sharrish-shayd'aani washirkih, waan aqtarifa ala nafsii suu-an aw ajurrahu ila muslim_
Ya Allah! Masanin abin dake fake dana sarari Mai kagen halittar sammai da kassai! Ubangijin komai, kuma Mamallakin sa! Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Kai! Ina neman tsarinka daga sharrin raina, da kuma sharrin shaidan da shirkarsa, dani tsuwurwurtawa kaina wani abu mummuna, ko in jawo shi ga wani musulmi. *Tirmizi da Ibn Majah, duba: Sahih Tirmizi 3/142.*
_Bismil-lahil'ladhii la yudurru ma'as-samii'ul-'alim_ (Sau Uku)
Da Sunan ALLAH, Wanda da Sunansa wani abu a samo ko a kasa baya cutarwa. Shi ne Mai ji, Masani. *Abu Dawud 4/323, da Tirmizi 5/465, da Ibn Majah da Ahmad, duba: Sahih Ibn Majah 2/332. Ibn Baz yace isnadinsa hasan ne. Duba Taufatul Akhyar, shafi 39.*
_Wanda ya faďa sau uku da yamma babu abinda zai cutar dashi_
_Radiytu billahi Rabba wabil-islama diyna, wabi Muhammadan Sallalahu Alaiyyah Wasalam Nabiya_ (Sau Uku)
Na yarda da Allah Ubangiji, da Musulunci addini, da Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Annabi. (sau uku). *Ahmad 4/337, da Nasa'i a cikin Amalul Yaum Wal Laila, hadisi mai lamba 4, da Ibn As-Sunni, hadisi mai lamba 68, da Abu Dawud 4/418, da Tirmizi 5/465. Ibn Baz yace hadisi ne hasan a cikin Taufatul Akhyar shafi 39.*
*Prayer For Spiritual Perfection*
*Rabbana 'atmim lanaa nuuranaa waghfir lanaa 'innaka 'alaa kulli shay'in qadiir
_Our Lord! Perfect our Light for us and grant us forgiveness. Verily, You have power over all things._ *Q66:8.*
Ga Tambayar Mu Ta Yau:
*Akwai Wata Kofa A Aljannah Wanda Masu Azumi Ne Kawai Zasu Shiga,Yaya Sunan Kofar?.
Domin bani amsa saboda mu karu da juna ku biyo ni ta wannan number:
*In Dedication to my late Father Alhaji Sabo Nadabo and also Alhaji Nuhu Abdullahi and beloved Muslim Ummah
_May your gentle souls continue rest in perfect peace in paradise, Amin Ya Allah
Yar Uwarku Ce Koda Yaushe A Musulunci:
Basira Sabo Nadabo