FALALAR ZIKIRI DA TASBIHI DA GODIYA GA ALLAH

57 0 0
                                    

(14/6/2017. 3:40 Am)
   (19/9/1438 A.H)






® *_Eloquence Writer Association_








*FALALAR ZIKIRI DA GODIYA GA ALLAH*









Writing by ✍🏽
    Basira Sabo Nadabo







*Bismillarhir-Rahmanir-Rahiim*

_Da Sunan ALLAH, Mai Rahama Mai Jin Kai_





Ga Amsar Tambayar Mu Ta Jiya:



*Sunayen Annabawa 10 Da Aka Lissafo A Al'Qur'Ani Mai Girma, Farko Akwai*

_Annabi Muhammad (S.A.W)
_Annabi Ibrahim (A.S)
_Annabi Sulaiman (A.S)
_Annabi Yusuf (A.S)
_Annabi Yaqub (A.S)
_Annabi Zakariyya (A.S)
_Annabi Imran (A.S)
_Annabi Isa (A.S)
_Annabi Musa (A.S)
_Annabi Adam (A.S)
      *Wallahu Ta'ala A'alam












*ADDU'AR TAFIYA ZUWA MASALLACI*



_Allahumma j'al fi qalbi nuran, wa fi lisani nuran, wa fi sam'i nuran, wa fi basari nuran, wa min fawqi nuran, wa min tahti nuran, wa'an yamini nuran, wa'an shimali nuran, wa min amani nuran, wa min khalfi nuran, waj'al fi nafsi nuran, wa a'zim li nuran, wa'azzim li nuran, wa j'al li fi asabi nuran, wa j'alni nuran. Allahumma a'tini nuran, wa j'al fi'asabi nuran, wa filahmi nuran, wa fi dami nuran, wa fi sha'rii nuran, wa fi bashari nuran. Allahumma j'al lin nuran fi qabri, wa anuran fi izami, wa zidni nuran, wa zidni nuran, wa zidni nuran, wa hab li nuran ala nur._

Ya Allah Ka sanya haske a cikin zuciyata, da haske a kan harshena, da haske a jina, da haske a ganina, da haske a birbishina, da haske a karkashina, da haske a damana, da haske a haguna, da haske a gabana, da haske a bayana; Ka sanya haske a cikin raina, Ka girmama haske gare ni, Ka girmama min haske, Ka sanya haske gare ni, Ka sanya ni na zama haske, Ka sanya haske a cikin jijiyoyina, da haske a namana, da haske a cikin jikina, da haske a cikin gashina, da haske a cikin fatata. Ya Allah Ka sanya mini haske a cikin kabarina, da haske a cikin kasusuwana, Ka kara mini haske, Ka kara mini haske, Ka kara mini haske, Ka bani ni haske a kan haske. *Ibn Hajr ya bayyana riwayoyin wannan hadisin a cikin Fat'hul Bari 11/116.*


*ADDU'AR SHIGA MASALLACI*

_A'uzu billahil-aziim wabiwajhihil-karim wasultanihil-qadiim minash -shaydaanir-rajiim,  bismil-lah, wassalatu wassalamu aala rasuulillah. Allahumma iftah lii abwaba rahmatika._

Ina neman tsarin ALLAH Mai Girma, da na Fuskarsa Mai Alfarma, dana Mulkinsa daɗaɗɗe, daga shaiɗan tsinanne. Da sunan Allah, tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah. Ya Allah! Ka buɗe minu kofofin rahamarka. *Abu Dawud duba: Sahihul Jami hadisi mai lamba 4591; da Ibn As-Sunni hadisi mai lamba 88, kuma Albani yace isnadinsa kyakkyawa ne; da Abu Dawud 1/126 duba: Sahihul Jami 1/528; da Muslim 1/494.*

*ADDU'AR FITA DAGA MASALLACI*

_Bismil-lah wassalatu wassalamu ala rasuulil-lah, Allahumma innii as'aluka min fadlika, Allahumma AAsimnii minash-shaydaanir-rajiim._

Da Sunan ALLAH, tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah. Ya Allah! Ina rokonka daga falalarka. Ya Allah! Ka kare ni daga Shaidan tsinanne. *Duba riwayoyin nassi na 20. Jumla karshe Ibn Majah ne ya ruwaito ta, duba Sahih Ibn Majah 1/129.*





Ga Tambayar Mu Ta Yau:

*A Wani Wata Mahajjata Ke Tsayuwar Arfah, Kuma Nawa Ga Wata?.*





Domin bani amsa saboda mu karu da juna ku biyo ni ta wannan number:

*In Dedication to my late Father Alhaji Sabo Nadabo and also Alhaji Nuhu Abdullahi and beloved Muslim Ummah*

_May your gentle souls continue rest in perfect peace in paradise, Amin Ya Allah_



Yar Uwarku Ce Koda Yaushe A Musulunci:

    Basira Sabo Nadabo

Falalar Zikiri DA TASBIHI Da GODIYA GA ALLAH Where stories live. Discover now