FALALAR ZIKIRI DA TASBIHI DA GODIYA GA ALLAH

56 0 0
                                    

(15/6/2017. 3:27 Pm)
    (20/9/1438 A.H)




® *_Eloquence Writers Association_







*FALALAR ZIKIRI DA TASBIHI DA GODIYA GA ALLAH*






Writing by ✍🏽
   Basira Sabo Nadabo







*Bismillarhir-Rahmanir-Rahiim*

_Da Sunan ALLAH, Mai Rahama Mai Jin Kai_





Ga Amsar Tambayar Mu Ta Jiya:

*Ranar Da Mahajjata Suke Tsayuwar Arfah Shine: Tara (9) Ga Watan Zal'Hijjah. Wallahu Ta'ala A'alam*




*ADDU'AR IDAN DARE YA SHIGA*

_La'ilaha illal-lahul-wahidul-qahhar, rabbus-samawati wama baynahuma al'aziizul-ghaffar._

Babu abin bautawa da gaskiya sai ALLAH, makad'aici, ma rinjayi, Ubangijin sammai da kassai da abin dake tsakaninsu, mabuwayi, mai yawan gafara. *Abu Dawud 4/12 duba: Sahih Tirmizi 3/171.*

*ADDU'AR WANDA YA RAZANA A CIKIN BARCI, DA WANDA YA KASA BARCI*


_A'uuzu bikaliimatil-lahittammat min ghadabih, wa'iqabih, washarri 'ibadih, wamin hamazatish-shayatiin, wa-an yahduruun._

Ina neman tsari da kalmomin ALLAH Cikakku daga fushinsa, da ukubarsa da sharrin bayinsa, da kuma wasu-wasin shaidanu, da kuma kada su zo mini a cikin al'amurana. *Muslim 4/1772, 1773.*

*WANDA YA YI MAFARKI MARA KYAU*

Wanda yaga abu mummuna a mafarki, to sai yayi wadannan abubuwan:

- _Ya yi tofi gefen hagunsa sau uku (ikhlas, falaq, nas)_

- _Ya nemi tsarin ALLAH daga shaidan da kuma sharrin abin daya gani, sau uku_

- _Kada ya gaya wa kowa wannan mafarkin_

- _Ya juyar da kwaiɓin daya kasance yana kwance a kansa_

- _Idan ya so, ya iya tashi yayi sallah._

*Muslim 4/1773.*


Ga Tambayar Mu Ta Yau:

*Sharudan Wajibcin Sallar Juma'a Guda Nawa Ne?*


Domin bani amsa saboda mu karu da juna ku biyo ni ta wannan number:

*In Dedication to my late Father Alhaji Sabo Nadabo and also Alhaji Nuhu Abdullahi and beloved Muslim Ummah*

_May your gentle souls continue rest in perfect peace in paradise, Amin Ya Allah_


Yar Uwarku Ce Koda Yaushe A Musulunci:

   Basira Sabo Nadabo

Falalar Zikiri DA TASBIHI Da GODIYA GA ALLAH Where stories live. Discover now