FALALAR ZIKIRI DA TASBIHI DA GODIYA GA ALLAH

58 0 0
                                    

(16/6/2017. 8:41 Am)
    (21/9/1438. A.H)





® *_Eloquence Writers Association







*FALALAR ZIKIRI DA TASBIHI DA GODIYA GA ALLAH





Writing by ✍🏽
    Basira Sabo Nadabo




*Bismillarhir-Rahmanir-Rahiim

_Da Sunan ALLAH, Mai Rahama Mai Jin Kai



Ga Amsar Tambayar Mu Ta Jiya:

*Sharudan Wajibcin Sallar Juma'a Guda 5 ne Sune: _Babban Abu Mai Mahimmanci Shine Mutum Ya Kasance Musulmi, Baligi, Mai Lafiya, Ba Bawa  ba, Namiji.  Wallahu Ta'ala A'alam






*ADDU'AR MAGANIN DAMUWA DA BAKIN CIKI


_Allahumma innii 'abduk, ibnu 'abdik, ibnu amatik, naasiyatii biyadik, madin fiyya hukmuk, 'adlun fiyya qada-uk, as-aluka bikulli ismin huwa lak, sammaytaa bihi nafsak, aw anzaltahu fii kitabik, aw 'allamatahu ahdan min khalqik awis-ta'dharta bihi fii 'ilmil ghaybi 'indak, an taj'alal-Qur'ana rabii'a qalbii, wanuura sadrii wajalaa huznii wazahaba hammi.

Ya Allah! Ni bawanka ne, kuma ɗan bawanka, kuma ɗan baiwarka. Makwarkwaɗata a hannunka take hukuncinka zartacee ne a kai na, kuma kaddararka gare ni mai adalci ce, ina rokon ka da kowanne suna naka, cikin littafinka, koka sanar da shi ga wani daga halittarka, ko ka keɓance kanka da saninsa a cikin ilimin fake da ke warin ka. Da ka sanya Alkur'ani ya zama kaka ga zuciyata, da haske ga kirjina, da kwaranyewa ga bakin cikina, da kuma mai tafiyar da damuwata. *Ahmad 1/391 kuma Albani ya inganta shi.



*Ma'anar kasancewa ALKUR'ANI ya zama kaka ga zuciyata shine Zuciya ta samu jin daɗi da hutu, saboda a lokacin kaka mutane suna samun jin daɗi da hutu, don haka sai aka ambaci zamanin a ka nufi halin da ke samuwa a cikinsa [Bayanin mai tarjama].


_Allahumma innii a'uudhu bika minal-hammi walhuzn, wal'ajzi walkasali walbukhli waljubn, wadal'id-dajni waghalabatir-rijal.

Ya Allah! Ina neman tsarinka daga damuwa, da bakin ciki, da gajiyawa, da lalaci, da rowa, da rangwantaka, da nauyin bashi, da rinjayen mazaje. *Bukhari 7/157, duba Fat'hul Bari 11/173.




Ga Tambayar Mu Ta Yau:

*Wani Sallah Ne Na Farko Bayan An Mayar Da Alkibila Zuwa ka'aba?.

Domin bani amsa saboda mu karu da juna ku biyo ni ta wannan number:

*In Dedication to my late Father Alhaji Sabo Nadabo and also Alhaji Nuhu Abdullahi and beloved Muslim Ummah*

_May your gentle souls continue rest in perfect peace in paradise, Amin Ya Allah

Yar Uwarku Ce Koda Yaushe A Musulunci:

    Basira Sabo Nadabo

Falalar Zikiri DA TASBIHI Da GODIYA GA ALLAH Where stories live. Discover now