FALALAR ZIKIRI DA TASBIHI DA GODIYA GA ALLAH

175 0 0
                                    

(17/6/2017. 4:58. A. M)
   (22/9/1438. AH)






® *_Eloquence Writers Association




*FALALAR ZIKIRI DA TASBIHI DA GODIYA GA ALLAH




Writing by ✍🏽
    Basira Sabo Nadabo



*Bismillarhir-Rahmanir-Rahiim

_Da Sunan ALLAH, Mai Rahama Mai Jin Kai



Ga Amsar Tambayar Mu Ta Jiya:

*Sallar Da Aka Farayi Bayan An Mayar Da Alkibila zuwa ka'aba Shine: Sallar LA'ASAR. Wallahu Ta'ala A'alam



*YADDA ANNABI (S.A.W) YAKE KIRGA TASBIHINSA

_Daga Abdullahi ɗan Amr, Allah ya yarda dashi ya ce: "Na ga Annabi (S.A.W) yana kirga tasbihi da yatsun hannun damansa. *Bukhari tare da Fat'hul Bari 10/88, da Muslim 3/1595.

Munga kenan bai halarta mu dinga kirga tasbihi da yatsun hannun dama da hagu ba kenan tunda wanda muke koyi dashi da hanun damansa ya kirga dashi, amma bance haramun bane kawai dai babu wani nassi ko hadisi inganttace da ya ce zamu iya kirgan tasbihi da hagu da dama, Kawai abinda na sani shine hannun dama shine mafi falala. Wallahu Ta'ala A'alam, ALLAH kasa duk ibadun mu dai dai mukeyi Amin Ya Allah.


*DAGA CIKIN AYYUKAN ALHERI DA KYAWAWAN HALAYE.

Jabir ibn Abdullah, ALLAH ya yarda dashi ya ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: 'Idan duhun dare ya gabato - ko kuma almuru tayi - to ku yana 'ya'yanku fita, domin Shaiɗanu suna bazuwa a wannan lokacin. Idan sa'a ta gota a cikin dare, to sai ku bar su. Ku rufe kofofi, kuma ku ambaci sunan Allah (yayin da kuke rufewa), domin Shaiɗan baya buɗe rufaffiya. Ku zuge bakin salkunan ruwanku, kuma ku ambaci Sunan Allah (yayin da kuke zugewa), kuma ku rufe kwanunkan abincinku, ku ambaci Sunan Allah (yayin da kuke rufewa); ko da ku ɗora wani abu ne akan kwanukan. Kuma ku kashe fitilunku na aci-balbal.

Allah yayi tsira da aminci da albarka ga Annabinmu Muhammadu, da halayensa, da shabbansa baki ɗaya, da tabi'un tabi'ina. Amin

Allah ka kara haske a karatun mu, da aiyikan mu, da haske a cikin rayuwar mu.

Ya Allah ka tsaida Sallah a kanmu da zuriyar mu baki ɗaya.

Ya Allah mu bayinka kane masu laifi, Allah ka yafe mana. Abinda ya gagare mu Allah ka iya mana. Allah abinda ke bamu tsoro Allah ka kauda shi a gare mu. Abinda zamu iya Allah ka taimaka mana.

Ya Allah kara tsare mu da imanin mu da barin hanyar tsira, Allah ka juyar da fuskokin mu ga aikata shirka, da barin ɓarna damu da zuriyyar mu gaba ɗaya.

Ya Allah wanda basu da matsuguni Allah ka basu, mu da muke dashi Ya Allah ka kore mana Shaiɗanu a cikin sa.

Ya Allah! Mata da suke kan gwiwa Allah ka sauke su lafiya kasa Albarka a abinda suka haifa, wanda suke nema Allah ka basu masu albarka.

Matan da suke gidan aure Allah ka kara zaunar dasu lafiya, mu da bamu dashi Allah ka haɗamu da mazaje nagari masu addini da tsoronka Ya Allah.

Duk wanda yake cikin bakin cikin rayuwa Allah ka yaye mana, ka biya mana bukatun mu na alheri.

Allah! Ka kara dauwamar damu a cikin raharmar ka da kwanciyar hankali. Amin Ya Allah

Ya Allah! Ka kare mu daga azabar sakar, da hawuya, da azabar wutar jahannama, Allah kasa muna daga cikin wanda za'a 'yanta daga wuta zuwa Jannatul Firdausi. Amin Ya Allah....


Ga Tambayar Mu Ta Yau:

*Shekaru Nawa Ne Annabi Yusuf (A.S) Yayi A Gidan Yari?.

Domin bani amsa saboda mu karu da juna ku biyo ni ta wannan number:

*In Dedication to my late Father Alhaji Sabo Nadabo and also Alhaji Nuhu Abdullahi and beloved Muslim Ummah

_May your gentle souls continue rest in perfect peace in paradise, Amin Ya Allah

Yar Uwarku Ce Koda Yaushe A Musulunci:

   Basira Sabo Nadabo

Falalar Zikiri DA TASBIHI Da GODIYA GA ALLAH Where stories live. Discover now