(18/6/2017. 3:58 A.M)
(23/9/1438. A.H)® *_Eloquence Writers Association
*FALALAR ZIKIRI DA TASBIHI DA GODIYA GA ALLAH
Writing by ✍🏽
Basira Sabo Nadabo*Bismillarhir-Rahmanir-Rahiim
_Da Sunan ALLAH, Mai Rahama Mai Jin Kai
Ga Amsar Tambayar Mu Ta Jiya:
*Annabi Yusuf (A.S) Yayi Shekaru Bakwai A Gidan Yari. Wallahu Ta'ala A'alam
*FALALAR SALATI GA ANNABI, TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI
Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: 'wanda yayi salati ɗaya a gare ni, Allah zai yi salati goma a gare shi. *Muslim 1/288
Kuma Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: 'ka da ku mai da kabarina idi; kuyi salati a gare ni ko ina kuke, domin salatinku yana isa zuwa gare ni ko a ina kuka kasance. *Abu Dawud 2/218 da Ahmad 2/367. Albani ya inganta shi a cikin Sahih Abu Dawud 2/383.
_Ma'anar mai da Kabarin Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, idi shi ne a rika kirdadon yin bauta a wajen Kabarin ta kamar salati a gare shi da waninsa. Haka kuma yana nuni ga hanin taruwa a kabarin don ziyararsa, kamar yadda ake taruwa wajen idi. Kamar yadda yake nuna hani ga zaton cewa ko yaushe mutum zai yi wa Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, salati sai ya dawo wajen kabarin zai yi, don haka ne ma sai aka ce a karshen hadisi: 'ku yi salati a gare ni ko ina kuke, domin salatinku yana riska ta. Ka duba Aunul Ma'abud sharhin Sunan Abi Dawud (6/23-24). [Bayanin mai tarjama]
Kuma Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: 'Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a wurinsa amma bai yi min salati ba. *Tirmizi 5/551 da wasu malamai, duba: Sahihul Jami 3/25 da Sahih Tirmizi 3/177.
Kuma Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: 'Allah yana da waɗansu mala'iku matafiya a bayan kasa, suna isar mini da sallama daga al'ummata. *An-Nasa'i, da Hakim 2/421. Albani yace isnadinsa hasan ne a cikin Sahih Abu Dawud 1/383.
Kuma Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: 'Babu wani wanda zai yi mini sallama face ALLAH ya dawo mini da raina na amsa masa sallamarsa. *Abu Dawud hadisi na 2041. Albani yace isnadinsa hasan ne a cikin Sahih Dawud 1/383.
_Sallahu Alaihi Wa Sallam
Ga Tambayar Mu Ta Yau:
*Wacce Bishiya Ce ALLAH Ya Fara Halitta A Bishiyoyin Duniya?
Domin bani amsa saboda mu karu da juna ku biyo ni ta wannan number:
*In Dedication to my late Father Alhaji Sabo Nadabo and also Alhaji Nuhu Abdullahi and beloved Muslim Ummah
_May your gentle souls continue rest in perfect peace in paradise, Amin Ya Allah
Yar Uwarku Ce Koda Yaushe A Musulunci:
Basira Sabo Nadabo