(20/6/2017. 4:38. A.M)
(25/9/1438. A.H)
® Eloquence Writers Association
FALALAR ZIKIRI DA TASBIHI DA GODIYA GA ALLAH
Writing by ✍🏽
Basira Sabo NadaboBismillarhir-Rahmanir-Rahiim
_Da Sunan ALLAH, Mai Rahama Mai Jin Kai
Don ALLAH, Yan Uwa Ina Barar Addu'an ku In Shaa Allah On 26-30 Ina Da Exams, Don Allah Ina Rokon Addu'an Ku, ALLAH yasa Nayi A Sa'a, Kuma ALLAH Yasa Karatun Ya Amfane Ni Da Addini Na Da Al'umman Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Da Iyaye Na Da Zuriya Ta. Amin Ya Allah, Don Allah
Ga Amsar Tambayar Mu Ta Jiya:
*_Annabi Isa (A.S) Yana Da Shekara 35 A Duniya Kafin ALLAH (S.W.T) Ya Dauke Shi Zuwa Sama. Wallahu Ta'ala A'alam
SALATI GA ANNABI, TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI
_Allahumma salli ala Muhammad, wa-ala-ali Muhammad, kama sallaitaa ala Ibrahim wa'ala ali Ibrahim, innaka Hamiidun majid, Allahumma barik ala Muhammad, wa'ala ali Muhammad, kama barakta ala Ibrahim wa'ala ali Ibrahim, innaka Hamiidun majiid.
Ya Allah! Ka yi salati ga Muhammadu da halayen Muhammadu, kamar yadda Ka yi salati ga Ibrahimu da halayen Ibrahimu, lallai Kai abin godewa ne, Mai girma. Ya Allah! Ka yi albarka ga Muhammadu, da halayen Muhammadu, kamar yadda ka yi albarka ga Ibrahimu, da halayen Ibrahimu, lallai Kai abin godewa ne, Mai girma. *Bukhari da Fat'hul Bari 6/408.
Ma'anar salati ga Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, shine yabo gare shi a wajen Mala'iku, da girmama shi. Haka aka ruwaito daga Abu Aliyu, kuma wannan shine abin da yawancin malamai suka rinjayar wajen ma'anar salati. (duba Fat'hul Bari 11/155-156.) [Bayanin mai tarjama].
_Abin nufi da halayen Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, su ne 'yan gidan sa, waɗanda suka haɗa matansa, da kuma duk waɗanda aka haramta musu cin sadaka,sune Banu Hashim. (Fat'hul Bari 11/160). [Bayanin mai tarjama]
_Allahumma salli ala Muhammad wa-ala azwajihi wadhurriyyatihi kama sallaitaa ala ali Ibrahim, wa barik ala Muhammad, wa'ala azwajihi wadhurriyyatih, kama barakta ala ali Ibrahim. Innaka Hamiidun majid.
Ya Allah! Ka yi salati ga Muhammadu, da kuma matansa da zuriyar sa, kamar yadda Ka yi salati ga halayen Ibrahim. Kuma Ka yi albarka ga Muhammadu, da kuma matansa da zuriyar sa, Kamar yadda Ka yi albarka ga halayen Ibrahim. Lallai Kai abin godewa ne, Mai girma. *Bukhari da Fat'hul Bari 6/407, Muslim 1/306, kuma lafazin na riwayarsa ne.
Ga Tambayar Mu Ta Yau:
A Wani Shekara Umar Bin Khatab Ya Musulunta?
Domin bani amsa saboda mu karu da juna ku biyo ni ta wannan number:
In Dedication to my late Father Alhaji Sabo Nadabo and also Alhaji Nuhu Abdullahi and beloved Muslim Ummah
_May your gentle souls continue rest in perfect peace in paradise, Amin Ya Allah
Yar Uwarku Ce Koda Yaushe A Musulunci:
Basira Sabo Nadabo