FALALAR ZIKIRI DA TASBIHI DA GODIYA GA ALLAH

62 0 0
                                    

(21/6/2017. 3:55. A.M)
   (26/9/1438. A.H)







®  Eloquence Writers Association









*FALALAR ZIKIRI DA TASBIHI DA GODIYA GA ALLAH



Writing by ✍🏽
    Basira Sabo Nadabo




*Bismillarhir-Rahmanir-Rahiim

_Da Sunan ALLAH, Mai Rahama Mai Jin Kai



Ga Amsar Tambayar Mu Ta Jiya:

*A Shekara Ta Hudu Bayan Annabta Ne Sayyadina Umar Bin Khatab Ya Musulunta. Wallahu Ta'ala A'alam




*FALALAR ZIKIRI


ALLAH  Maɗaukakin Sarki Ya Ce:

_Fa-udhukuro-ne adhkur-kum wa-ushkuro liy-wa-laa tukfuro-ni

«Ku ambace ni zan ambace ku, ku gode mini kada ku butulce mini >>  (Bakara aya ta 152).


_Ya ayyuha allatheena aamanoo othkuroo Allah thikran katheera

«Ya ku waɗanda suka yi imani ku ambaci Allah ambato mai yawa>> (Ahzab, aya ta 41).

  Aya ta 35 kuma yace:

«Da masu ambaton Allah da yawa maza, da masu ambaton Allah mata, Allah ya tanadar musu gafara da lada mai girma>>  (Ahzab Aya ta 35).

_Waoothkur rabbaka fee nafsika tadarru an wakheefatan wadoona aljahri mina alqawli bialghuduwwi waal-asali wala takun mina alghafileena._

"Kuma ka ambaci Ubangijinka a cikin zuciyarka, kana mai kaskan da kai da tsoro, ba da ɗaukaka murya ba (tsaka-tsakinin asirtawa da bayyanawa), da safe da marece, kuma kada ka zamo daga cikin gafalallu>> (A'araf, aya ta 205).

Kuma Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce : «Misalin wanda yake ambaton Ubangijinsa da wanda ba ya ambaton Ubangijinsa, Kamar misalin rayayye da matacce ne>>

(Duba Sahihul Bukhari tare da Sharhinsa Fat'hul Bari 11/208. Muslim ma ya ruwaito shi da lafazin: 'Misalin gidan da ake ambaton Allah a cikin sa, da Wanda ba a ambaton Allah a cikin sa kamar misalin rayayye da matacce. 1/539)

Kuma ya ce: «Shin ba na baku labarin mafi alherin ayyukanku ba,  kuma mafi tsarkinsu a wajen Sarkin da yake mallakar ku, kuma mafi ɗaukakarsu ga darajojinku, kuma mafi alheri gareku daga ciyar da zinariya da azurfa, kuma mafi alheri gare ku da ku haɗu da abokan gabanku ku rika dukan wuyayinsu, suna dukan wuyayinku? Suka ce ka bamu labari. Ya ce: Ambaton Allah Maɗaukaki>>

(Tirmizi 5/459, Ibn Majah 2/1245. Duba Sahih Ibn Majah 2/316, da Sahihul Tirmizi 3/139).



Ga Tambayar Mu Ta Yau:

*Menene Matsayi Mafi Girma A Aljanna?


Domin bani amsa saboda mu karu da juna ku biyo ni ta wannan number:

*In Dedication to my late Father Alhaji Sabo Nadabo and also Alhaji Nuhu Abdullahi and beloved Muslim Ummah

_May your gentle souls continue rest in perfect peace in paradise, Amin Ya Allah

Yar Uwarku Ce Koda Yaushe A Musulunci:

  Basira Sabo Nadabo

Falalar Zikiri DA TASBIHI Da GODIYA GA ALLAH Where stories live. Discover now