FALALAR ZIKIRI DA TASBIHI DA GODIYA GA ALLAH

45 1 0
                                    

(22/6/2017. 3:57. A.M)
   (27/9/1438. A.H)





® Eloquence Writers Association











FALALAR ZIKIRI DA TASBIHI DA GODIYA GA ALLAH





Writing by ✍🏽
   Basira Sabo Nadabo




Bismillarhir-Rahmanir-Rahiim

Da Sunan ALLAH, Mai Rahama Mai Jin Kai


GA Amsar Tambayar Mu Ta Jiya:

*Matsayi Mafi Girma A Aljanna Shine: Al'Wasila. Wallahu Ta'ala A'alam*l




FALALAR ZIKIRI




Kuma ya ce:  «Allah Maɗaukaki yana cewa: Ni ina tare da zaton bawana da ni, kuma ina tare da shi idan ya ambace ni. Idan ya ambace ni a cikin ransa zan ambace shi a cikin raina, idan ya ambace ni a cikin jama'a zan ambace shi a cikin jama'ar da tafi su alheri, in ya kusance ni taki ɗaya zan kusance shi kamu guda, in ya kusance ni kamu guda zan kusance shi tsawon gaɓa guda, in yazo min yana tafiya zan zo masa ina gaggawa»

(Bukhari 8/171, da Muslim 4/2061. Lafazin riwayar na Bukhari ne.)


Daga Abdullahi ibn Busr, Allah ya yarda dashi, ya ce: Ya Ma'aikin ALLAH! Shari'o'in musulunci sun yi yawa a gare ni, saboda haka ka nuna mini wani abu da zan yi riko da shi. Ya ce: «Kar harshenka ya gushe face yana ɗanye daga ambaton Allah».

(Tirmizi 5/458, da ibn Majah 2/1246. Duba Sahihul Tirmizi 3/139, da Sahih Ibn Majah 3/317).


Kuma Mai tsira da amincin Allah ya ce: «Wanda ya karanta harafi ɗaya daga littafin Allah yana da ladan kyakkyawan aiki ɗaya saboda shi, kuma dukkan kyakkyawan aiki ɗaya yana da ladan misalinsa goma. Ba ina cewa Alif Lam Mim harafi ba ne. A'a, Alif harafi ne, Lam harafi ne, Mim harafi ne.»

(Tirmizi 5/175. Duba Sahihul Tirmizi 3/9, da Sahihul jami'us sagir 5/340).

Kuma daga Ukbata ibn Amar, Allah ya yarda dashi, ya ce: Manzon Allah, tsira da amuncin Allah su tabbata a gare shi, ya fito alhali muna cikin runfa, sai ya ce: «Wane ne daga cikinku zai so ya fita kullun da safe zuwa koramar Buɗhan ko Akik, ya dawo da taguwa biyu masu manyan tozuwa, ba tare da yin wani laifi ba, ko yanke zumunta? » Muka ce: muna son haka. Ya ce: «Dayanku yaje masallaci ya nemi sani, ko ya karanta ayoyi biyu daga cikin littafin Allah, Mabuwayi Mai ɗaukaka, yafi masa taguwa biyu, ayoyi uku sunfi masa taguwa uku, ayoyi huɗu sun fi masa taguwa huɗu, da kwatankwacin adadinsu na rakuma. »

(Muslim 1/553).



GA Tambayar Mu Ta Yau:

*Saboda Me ALLAH Ya Halicce Taurari?


Domin bani amsa saboda mu karu da juna ku biyo ni ta wannan number:

*In Dedication to my late Father Alhaji Sabo Nadabo and also Alhaji Nuhu Abdullahi and beloved Muslim Ummah


May your gentle souls continue rest in perfect peace in paradise, Amin Ya Allah


Yar Uwarku Ce Koda Yaushe A Musulunci:

   Basira Sabo Nadabo

Falalar Zikiri DA TASBIHI Da GODIYA GA ALLAH Where stories live. Discover now