Babi Na Talatin

1.7K 172 75
                                    

Bayan shekaru Ashirin

Biki ake da gani bikin er gata ake, kwararriyar mai kwalliya aka gayyato don yi ma amarya kwalliya. Ana tsaka da yi ne wata mata ta shigo, kallo ɗaya zaka mata ka san jini ɗaya ne. Tsalle amaryar tayi ta nufe ta

"Anty Salmah Oyoyo, wallahi jiya baki ga kukan da nayi ba, da aka ce wai ba zaki samu zuwa ba"  Ta ce cikin harshen larabci.

"Haba Afaf ana bikin kanwata guda ɗaya tilo ba Nijeriya ba, ai ko Kasar Sin ce zan taho auranki. Shari'ar wata yarinya ya tsaida ni, sanata ya mata fyade aka kama shi, shi ne suke son a ɓatar da Shari'ar." wacce ta kira da Anty Salmah ta bada amsa.

"Ai kina kokari sosai, su ummie na cikin gida ko kin gansu? "

" ina fa,  su Salman sun iso kuwa? Jiya ya ce min zai baro Spain, wai bizar Rayhan ne ya dakatar da su" Ta amsa tana mai tafiya hanyar wajen su ummi.

                                 ***
Cikin shekaru ashirin anyi abubuwa ciki kuwa har da rashi na hajiya aziza da Hakimi da duk sauran matansa. Abba ma Allah ya masa rasuwa.

An kuma samu cigaba don kauyen MARKE a dalilin RAHANATU da jinin ta ya zama babban gari, Salman bayan kammala karatunsa ya samu aiki a jakadancin Nijeriya. Suhayl kuwa ya shiga makarantar horar da sojoji in da ya fita a muqamin 2nd lt, Salmah kuwa ta kammala karatunta na lauya a jami'ar ifriqiyya da aurenta daure a kanta, shi kuma Adam ya zama cikakken injiniya, kuma mijin da Hausawa ke kira da mijin marainiya. Duk abin da ta zama bata manta da kawayenta kuma aminanta na MARKE ba, jiddo, Rufy da ummitr. Rayuwa ya musu shar abin su don da su ake damawa saboda kasancewar su manyan yan kasuwa.

                           ***
Nacin da Abdul Hadi ya nuna ya sa ya shawo kan RAHANATU har aka daura musu aure, Hakimi ya zame mata waliy kuma uba inda duk kuɗin ta sai da ya mata kayan ɗaki da gara da uba kanyi ma yarsa acewar sa amanar da malam Tanko mahaifinta ya bar masa ne ya sauke.

Tun kafin auren ta san son da Hadi ke mata ba ko kaɗan bane don Salman ya labarta mata yanda ya tsaya tsayin daka akan su a matsayin sa na malamin su a makaranta. Bata kara tabbatar da hakan ba sai da aka kaita gidan sa a matsayin matarsa, duk da kasancewar girma ya hau kansu bai hana masa sakin kwanji ya nuna mata soyayya ba.

Wata goma sha ɗaya bayan bikin su ta haifi yan uku, maza. Nan ya saka musu sunan annabi SAW da aminansa wato Muhammad, Abubakar da Umar.

Bayan shekara biyu, ta sake samun ciki, a lokacin aka tsaida auren Salmah inda suka dunguma zuwa Sudan don biki, a chan nakuda ya kamata ta haifi yan biyu maza, karamci irin na Abdul Hadi, bikin sunan gaba daya ya aminta ayi a chan, sannan ya ba IMRAN daman sanya ma yaran suna, nan ya sa musu Uthman da Aliyu, a Cewar sa A cikata Annabi SAW da surikansa kuma khulafaur rashidun.

                   ***
A bangaren Imran kuwa tun da Aisha ta haifa masa Afaf haihuwa ya tsaya mata, hakan ya sa bayan su Aliyu sunyi shekara uku a duniya, Abdul Hadi ya dauke su ya damka ma IMRAN, yace

"ni ba zai iya baks Suhayl da Salman ba saboda sun zama sashi na jikinna, amma ga Aliyu da Uthman Uthman tun da sun zaɓi kasancewa da kai tun fitowar su duniya" 

Farin cikin da IMRAN yayi baya misaltuwa, a dalilin haka  zumunci tsakanin su ya fi na da kulluwa.

                       ***
"Momma" faɗin yar budurwa da bazata wuce shekara goma sha biyar ba ya dawo da Salmah daga tunanin da ta ke a tsaye.

"Ummu abieha, ina su Yusra da sauran kannenki, da fatan kin kula min da su sosai" Ta ce da ita

"momma kin faye son ya'ya, ke da abba ban san wa ya fi son mu ba" Ta faɗi tana dariya

"Ja'ira ki jira ki haifi naki se ki banzantar da su" Ta faɗa tana jan kumatunta, nan ta lafe a jikinta itama wai kunya. A haka suka karasa wajen sauran, duk bakin Nijeriya ne, itama da sauri ta karasa wajen inna.

"Inna ta" Ta faɗi tana dariya

"kar ki karya min yar uwa" faɗin RAHANATU tana mai sha'awar shaquwar da ke tsakanin su.

"Kai Ummie, Inna ki gwasale ta ga amaryar Mahmoud na min dariya, se na sa ya auro biyu a tare" Ta karasa tana harar wacce ta kira amarya.

"Ai ya ce daga biyu ba kari" itama ta faɗi tana zumɓuro baki. Nan aka sa ta gaba da tsokana kasancewa kowa ya san ta da kishi.

                          ***
Haka aka ci buki aka kare kowa na farin ciki yayin da alkhairi ke bin kowa.

ALHAMDULILLAH

GODIYA ta musamman ga er uwa Hajiya Aziza Idris, marubuciya mai tarin fikra, ubangiji Allah ya kara basira.

An ce uwa ba ta gode ma ɗan ta, ni dai nagode ɗan kwarai, Marubucin littafai da Fim, kuma mawakin zamani Jamilu Nafseen, cigaba da tinkaho Addu'ar uwa na tare da kai.

Jinjinar ban girma ga Fikra Writers Association, hakika da bazar ku nake rawa.

In babu ku ba Silar Ajali Ɗaukacin makaranta Silar Ajali, nagode da karamci da soyayya, zan muku posting tsofaffin littafai na kafin Allah ya bani ikon yin wani. Allah ya bar kauna.

SILAR AJALI Donde viven las historias. Descúbrelo ahora