Me ake nufi da So?

1K 9 0
                                    

Hakika ma'anar So, ta dade tana baiwa mallaman soyayya wahalan bayyanawa ga dalibai, makasudin hakan kuwa shine:- Sabanin ra'ayoyin da ake samu daga bangarori dabam dabam na mallaman soyayya ko luma ince masana soyayya a takaice. Wanda hakan yasa ma'anar So tazo da bayanai dabam dabam, inda wannan dalilin yasa ma'abota karatun littattafan soyayya suka kasa gane ainihin ma'anar So. Duk dacewar So yazo da ma'anoni dabam dabam. Amma hakan ba wani abu bane illah karin ilimi akan So. Saidai zamu iya kwatanta cewar Ma'anar so itace tsananin kauna da bukatar kusatar wani mutum ko wani abu daban. So", wata iska ce mai kadawa wadda babu wani dan adam bai shake
ta ba. Ya zama tilas kowane mutum ya kasance ya samu abin, amma ganin an hana shi saboda wasu
dalilai. Wannan ya yi daidai da lafazin wani marubuci
inda yace"so yakan tura saiwoyinsa cikin zuciya ne saboda hakaidan aka tunkudo shi, shi ma sai ya tunbuko zuciyar. Duk dacewa akwai karabcin lokaci na bayyana wadannan ma'anoni da suka fito daga magabata. Amma zamu bayani a cikin littafin mu da zamu wallafa a nan gaba kadan. ***** @Yahuza Moh'd BKY

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 10, 2017 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SIRRIN SOWhere stories live. Discover now